MahmudHussaini's Reading List
22 stories
CIWON ƳA MACE.. by Ouummey
Ouummey
  • WpView
    Reads 2,969
  • WpVote
    Votes 111
  • WpPart
    Parts 16
Rayuwa cike take da kaddarori da dama, dan Adam baze ce tayi imani ba kuma Allah ya kyale shi kawai, dan yadda da wannan imanin se Allah ya rubuto series of jarrabawowi din tabbatar da ingancin imanin namu. Se dai san rai da son zuciya na jagorantar dan Adam ga munanan ayyuka, wanda daga karshe suke jinginawa ƙaddara, akwai ƙaddara, amma kuma a boye cikin kaddarar nan akwai jagorancin wasu munanan halaye, son kai, hassada, bakin ciki, da ire iren su. Akwai wani karin magana da Bahaushe ke amafani da shi,musamman a tsakanin mu mata, wanda nake da ja akan shi, da kwarin gwiwa ta, da dukkan zuciya ta, haka da dukkan murya ta nake faɗin CIWON ƳA MACE BE TAƁA ZAMA NA ƳA MACE BA!. Ban yarda da karin maganar wai CIWON ƳA MACE NA ƳA MACE bane, ban kuma aminta ba, shiyasa tun tasowa ta nayi watsi da shi, bangarori da dama da na duba na rayuwar mu mata ya karya ta shi. Ina tunanin bahaushe be fahimci rayuwar mu ba, be karanci mata ba, da na tabbata baze fadi wannan zancen ba balle har ya shiga jadawalin karin maganar mu na Hausa masu tushe da dimbin tarihi. Bari kuji, mace ita ce matsalar mace yar uwar ta, dukkan kukan mace in kun yi duba daga tushe zaku ga daga mace yake, kyashi, bakin ciki, hassada, son kai, munafunci da wasu sauran mugayen halaye da dabi'u sun tare a wajen mata ne. Ba zan ce duka ba dan ko a cikin gidan karuwai akan haifi malami, sedai da yawan mu haka muke, bana tunanin akwai macen da in aka binciki rayuwar ta ba za'a samu tabon yar uwar ta mace ba, in one way or the other, se kuma da na fara fahimtar rayuwa na fahimci DOLE ACE MATA SUN FI YAWA A WUTA.! Ban tsani mace ba dan nima itace, mahaifiya ta ma itace, akwai kuma tarin yayye da kanne, sedai na tsani munanan halayen mu, na kyamaci gurbatattun mata na daga cikin mu, dan sun taka rawar gani cikin KADDARAR RAYUWA TA!. Dan Allah kar ku yanke min hukunci batare da kun saurare ni ba, ina rokon ku ku bani aron lokaci da hankalin ku, ku biyo ni dan jin muguwar rawar da mace ta taka cikin ra
ZAMAN YA'YA by Mmnmuhibbat
Mmnmuhibbat
  • WpView
    Reads 13,607
  • WpVote
    Votes 1,219
  • WpPart
    Parts 35
Labari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari ne akan yadda Maza suke amfani da ya'ya wurin kuntata ma mace mutane suke amfani da kalmar zawarci suke kuntata ma mata yan'uwansu.Labarin Salma da sule maketacin namiji mai kwace kudin matarshi.Bala da balki da gaje masu munafukin miji mazinaci.Ma'u da Mudi Miji mai shaye shaye ga zama haramci.Sai baiwar Allah zainab wacce maraicin ta bai zama rauni gareta ba wurin kwatar kanta daga Miji mai cin amanar aure wato talle.
muwaddat  by hauesh
hauesh
  • WpView
    Reads 157,065
  • WpVote
    Votes 4,242
  • WpPart
    Parts 15
"auwal ni ko sai nake ganin kamar kayi kankata a batun soyayya balle kuma akai ga batun aure ,yanzu fa kake shekara 22 a duniya , ba soyayya ce ta dace da Kai ba, karutu ne ya dace da rayuwarka, bugu da k'ari ita wacce kake so din ta girmeka . ya dubi mahaifiyarsa kamar zaiyi kuka yace" ni kaina nasan soyayya bata dace dani ba, ban san ya'akayi zuciyata ta afka wannan lamarin mai wuya misaltuwa ba ,zuciyata bata yi shawara da ni, na dauki abun amatsayin wata jarabawa ce daga Allah,.. ki yarda ummi ki amince ki bani auren diyarki muwaddat, ni ita kadai nake so,duk rayuwar da babu ita to babu auwal .. faiza idanunta taf da ruwan hawaye ta dubi auwal cikin muryar kuka tace " in har zaka iya son yayata data girmemaka ,ni mai zai hana ka so ni, tunda nima jininta ce uwa daya uba daya, gashi Allah ya jarabeni da matsanancin soyayarka, nice daidai da kai ba yan'uwata ba, ni yafi dacewa kaso takarasa mgnr tana kuka.. auwal batare daya dubeta ba yace "nayi rantsuwa da Allah har yau sama da shekara sha takwas kenan ban taba kaunar wata diya mace ba sai yayarki muwaddat, ban taba jin sonki na daidai da second daya ba, ni matsayin k'anwata na d'aukeki, amman batu na soyayya babu shi atsakaninmu, muwaddat ce acikin kokan raina, ina sonta tamkar raina ,ita kad'ai ce macen da nake jin zata kashe iya kashe min ki shi ruwan danake d'auke dashi na tsawon shekaru.......
HAIRAN🔥💥♥️ by Shatuuu095
Shatuuu095
  • WpView
    Reads 7,044
  • WpVote
    Votes 160
  • WpPart
    Parts 23
Tunda Anty ta fara magana, Prof yake kallon ta, idan ka kalle shi ba zaka taba fahimtar a yanayin da yake ciki ba, ba zaka fahimci emotions din shi ba, Amma yadda yake kallon Anty, da yadda ya bata dukkan hankalin shi, Abu ne da zai tabbatar maka cewar maganar babba ce. Anty ta gama bayanin ta tsaf sannan tayi shiru tana jiran ganin hukuncin da Prof zai yanke. Cikin nutsuwa yace " A Ina ta samu?" Shi ne tambayar da yayi ma Anty, maimakon tayi masa bayani se cewa tayi " Ai na Gama nawa professor, abin da ya rage kaji ta bakin HAIRAN kawai!" "Me yasa Anty?" Cike da nutsuwa tace " Saboda zaka ga kamar kare ta nake, Amma idan tayi maka bayani Ina Jin zaka fi gamsuwa da kyau!" Daga haka Prof yayi shiru Yana son ya auna nauyin Abubuwan da Anty ta fada Masa, se kawai ya Mike yayi ma Anty sallama ya fita. Kunsan yadda tsumma yake idan aka tsoma shi cikin ruwa ko? To haka Prof yayi, gaba daya jikin shi ya saki, yayi shiru tamkar wani kurma, ya bude mota ya shiga ya kifa Kan shi akan steerer wheel, shi yasa take fada Masa lallai lallai se sun rabu kenan? To Ina ta samu shi ne tambayar da take zuwa Masa... *** Shigowa ta kenan daga lecture, na gaji, gajiya kuwa matuka saboda shirin exams da muke, har lokacin bana cikin dadin rai, Abu ya kusa wata daya Amma still nukurkusa ta yake Yi. Ina Zama Saman gado Ina kallon Nuriyya da ta dakko wani gari tana kokarin kwaba shi da ruwa nace " Me zakiyi?" Tace "Kunun aya Mana!" Se nace " Kunun Aya Kuma, gaskiya Kin iya bawa Kai wahalar, ana shirin exams din!" Tayi dariya tare da daga min wata transparent ziplock tace " Waye zai Baki wani wahala, wannan ai is outdated, halan Baki San Islah foods ba ko? To ita take siyarda wannan garin na kunun Aya, yours is just to make little effort se ki Sha!" Nayi murmushi Amma kafin nayi magana se Naga Kiran Anty na shigowa cikin waya ta, da sauri nayi excusing Kai na sannan na mike Dan fita
CIWON 'YA MACE by fadeelalamido
fadeelalamido
  • WpView
    Reads 4,122
  • WpVote
    Votes 352
  • WpPart
    Parts 27
CIWON 'YA MACE rikitaccen al'amarine mai kulle kai, nishadi,soyayya, cin amana, da yadaura, acikin labarin ne zaga yadda ciwon 'ya mace ya zama na yarwanta mace, duk kuwa da tarin alakar dake tsakani makusantan biyu, ta tsayawa yar uwarta mace duk kuwa da cewa abin ita zai bibiya tare da ciwo arai, a nan ne zata ji inama ace nakiya bata tono garma ba.
KADDARA KO SAKACI? by MssHussaynah
MssHussaynah
  • WpView
    Reads 32,912
  • WpVote
    Votes 1,354
  • WpPart
    Parts 19
Wannan kagaggen labari ne kan wata 'yar jami'a da tayi depending kan lecturers domin cin jarrabawarta. wannan ya zamo mata babbar kuskuren da yayi sanadiyar lalacewar rayuwarta........
WUTA A MASAƘA by Ayshercool7724
Ayshercool7724
  • WpView
    Reads 51,090
  • WpVote
    Votes 2,132
  • WpPart
    Parts 31
labari akan wata yarinya me rawar kai da rashin jin magana sam, labari akan taɓarɓarewar zumunci, tarbiyya da rayuwar 'ya mace idan ta rasa me jiɓantar lamarinta, Yayin da ake zaton wuta a maƙera katsam se ta bayyana a masaƙa, ku kasance dani dan jin me ze faru a wannan littafin
NANA AMINATU 2022 by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 16,379
  • WpVote
    Votes 916
  • WpPart
    Parts 56
Maganganun ta tamkar saukar kibiya take jin su a zuciyarta duk idan ta tuna, suna sukan ta su hana ta sukuni, suna tarwatsa ta su saka ta taji ita ƙasƙantanciya ce wacce bata kai ɗin ba kamar yadda take cewa, tana ganin baƙin kanta a koda yaushe a wacce bata kai ba, ko kaɗan bata taɓa saurara mata ba, ya za'a yi ta dena kallon kanta ta daban a cikin mutane yayinda take tuna duk wata kalma ta ɓatanci da take bin ta dasu a kullum ranan duniya? tun sanda ta buɗe idanuwanta da wayon ta take jin waɗannan munanan kalaman da ke tarwatsa mata duk wani farin ciki da jin daɗin ta. Sai dai kuma a duk sanda take jiyo kalaman sa sai ta ji ƙwarin gwiwa har ta kalli kanta a wacce ta kai kuma ta isa, ashe akwai ranan da zata yi farin ciki haka? Akwai ranan da wani zai iya yabon ta har ya nuna mata tana da matsayi fiye da sauran Mata? She can't believe that... Shi ne Mutum na farko da yake faɗa mata kalaman da idan ta ji su take ganin ta kai Mace, ta kai Mace cikakkiya ba wacce ta rako Mata ba, a kullum ganin kanta take yi a bata kai matsayin ba, ita bata kai Macen da zata iya fitowa ayi gwagwarmaya da ita a matsayin ta na ɗiya Mace ba. Shin wane ne shi wannan ɗin? Tabbas Ƙaddara kowa da irin tasa, wasu tana zuwar musu da sauƙi wasu kuwa akasin hakan, ba wai don wani ya fi wani bane a wurin Allah hakan ke faruwa, a'a, sai dai don Allah na gwada ko wanne bawa ta hanyar ɗaura masa tashi ƙaddaran, walau me sauƙi ko akasin sa, ko wanne bawa da tashi ƙaddaran kuma kowa yana fatan ace ya tsallake ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa. Haka itama NAANA AMINATU tayi fafutuka a cikin rayuwar ta domin ta ga ta cinye nata ƙaddaran da ta kasance babba a gare ta. Na san Kuna so ku bibiyi labarin ta domin ku ji mene ne ya faru a rayuwar ta, to ku bi Ni sannu a hankali Zan warware muku komi a cikin sauƙi, ina fata labarin zai zame muku darasi a cikin rayuwa.
SHAREEF 2023 by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 9,998
  • WpVote
    Votes 456
  • WpPart
    Parts 49
Guguwar ƙaddara, mai sauya fari ya koma baƙi, haka shima baƙi ya koma fari. Haƙiƙa duk abun da Allah ya ƙaddara zai faru; to dole sai ya faru, kuma Bawa bai isa ya tsallake sa ba Wata iriyar ƙaddara ce da ta shigo cikin Rayuwar matashin, yayinda tayi tasiri a cikin rayuwarsa har ta canza mishi alƙibla. Zan so ku bi Ni a cikin ƙayataccen labarin nan domin sanin wane ne SHAREEF? "Wlh ko kukan jini zaka yi SHAREEF sai ka amshi cikin nan a matsayin naka, kana son ka nuna mana bamu san me muke yi ba ne? Kuma yarinyar zata yi maka ƙarya ne? ko kuwa Maryam tana da wayon da har wani zai yi mata ciki sannan ta laƙaba maka ne? To ka canza tunani da dabara, babu yanda za a yi Maryam tayi maka wannan mummunar sharrin, ai dama Likita ya faɗa kana buƙatar Mace a tare da kai, sai ga shi kayi amfani da damar ka ka shiga ka titsiye yarinya ka biya baƙatun ka; sai ya zamana Allah ba azzalumin Bawan sa bane ya nuna maka Iyakan ka, sannan ita ɗin Matarka ce, kai ko ba Matarka bace tunda har ka iya keta mata mutunci dole kai zaka aure ta, tarbiyyar da muka baka kenan ko SHAREEF?" Hhhhh labari mai taɓa zuciya!
SAWUN GIWA...!🐘 by Hafnancy01
Hafnancy01
  • WpView
    Reads 8,045
  • WpVote
    Votes 98
  • WpPart
    Parts 18
"Dallah gafara can malama, har ke kin isa ki mana abunda Allah bai mana shi ba? Akanki ne aka Fara irin hakan? Ko kuwa akanki ne za'a daina? Sai wani ciccika bak'in banza kike awurin kamar zaki iya tabuka abun kirki idan har mukayo gaba da gabanta, Ke kin sani sarai ba yabon kai ba ammh wallahi tsab zan tumurmusheki anan wurin kuma in zauna lfy lau agidan Mijina, Kuma ki saurareni dak'yau, halinki ne ya jaza miki wannan cin amanar, Ke kowacce mace tana mafarkin samun miji kamar naki ammh ke Allah ya baki salihin mutum mai tsoron Allah, Sai ke kuma kikai amfani da hakan kina muzguna masa? Bashi da iko da gidansa sai yadda kikai? Babu wata muryar da yake tsoro da shakka face naki? To wallahi ki sani da'ace ayau bani da aure ne to Kinji nace Allah mijinki zan aura, zan shawo kansa kuma dole ya saurareni don kowacce mace da salon nata kissar, balle ma idan yaga ina masa abunda ke baki masa shi, kin san Zuciya nason mai faranta mata, ke mahaukaci kankat kenan yana kaunar mai faranta masa balle mai hankali, Hajiya Sa'a kiyi kuka da kanki ba dani ba don iya allonki ne yaja miki Faruwar hakan." Kuka sosai Hajiya Sa'a ke rerawa don ta kasa Furta komai kuma, Hajiya Aisha ta gama kashe mata jiki, Kama baki Hajiya Aishar tayi tana Fadin"Ai baki ma soma kukan ba, nan gaba kadan zakiyi wanda yafi wannan, kuma ki saurareni dak'yau, ga 'yata nan amana, Ku Zauna lfy ke da ita don wallahi kika sake naji ance ko ciwon kai kin sakata Allah saina lahira ya fiki jindadi, don kwarai zan cire kunyar Surukuta da amintar dake tsakaninmu musa wando kafa daya dani dake, Sabida haka ki kiyaye sannan Kuma akyalesu su sha amarcinsu Cikin kwanciyar hankali, don wallahi Hajiya Sa'a tashin hankalinsu kema tashin hankalinki, Tun wuri ki iya takunki don karki ce ban fada miki ba, Suhaila ita kadai ce 'yar da Allah ya bani sabida haka zan iya yin komai akanta, Ki huta lfy."