zm-chubado
ta zabi Yusuf Attahiru a matsayin abokin rayuwarta na har abada, bayan ta saka ƙafa ta shure zabin iyayenta.
ta biyewa ra'ayin zuciyarta kuma ta samu abinda take so, sai dai, soyayyar ba tai mata rana ba, illa jefata da tayi a cikin tarkon bala'in dangin miji!!
Cikin ƙanƙanin lokaci su ka gigita mata lissafi ta dena gane komai saboda masifar su.
Sai dai, a lokacin data yankewa kanta shawarar tserewa daga garesu tuni bakin alƙalami ya jima da bushewa✍️