Labarin Yarinyar da ta tashi a tsakanin yayyenta maza, da suke shirye da aikata ko menene saboda ita, ba ta san tsoro ba, rashin ji ya kaita ga haɗuwa da ƙaddararta, ko wace iri ce ƙaddarar ta ta?
Rayuwa tana zo ma mutum a ko wane yana yi inda ƙaddara me kyau ko akasin ta ke faruwa a gare ka, tawa ƙaddarar ta shallake tunanin duk wani me tunani, tawa ƙaddarar wata aba ce wadda babu masu fuskantar ta a cikin mutane, tawa ƙaddarar ita ce CIKIN ALJAN!!!