Rashi ba shi kaɗai yake samar da giɓi a rayuwa ba. Wani yana doron ƙasa amma dalilai kan sa wanzuwarsa ta kasa amfanar da makusantansa. Me zai faru da rayuwar ƴaƴan da su ka zaɓi zama da giɓi a gurbin da mai cike shi yake da rai da lafiya? RAYUWA DA GIƁI...
Burin kowace uwa ta raini ɗanta ya girma kamar ubanshi. Amman ni na raine ka da zullumin kar ka zamo kamar ubanka...tun daga ranar da na haife ka bakina ya buɗe da addu'ar ka bambanta da ubanka ta dukkan bangare..
Rayuwa gaba daya ta canzawa Rabi a dalilin kishiya, duk wata dama da ta zata kauna ce ta sa ya hanata yanzu ya bawa amaryarsa wannan damar; harma ya na kafa mata hujja.
Bata taba zaton zai yi mata haka ba ko mata nawa zai aura.
Labarin matar cushe, Rukayya Mus'ab a Daular Musulunci Alhareeh, wacce aka ba wa Ishaq Mahmud ita a matsayin LADAN NOMA.
Labarin aure auren Ishaq duk a bulayin bambanta matar so da ta cushe.
Ko zai dace🤔