Rayuwa gaba daya ta canzawa Rabi a dalilin kishiya, duk wata dama da ta zata kauna ce ta sa ya hanata yanzu ya bawa amaryarsa wannan damar; harma ya na kafa mata hujja.
Bata taba zaton zai yi mata haka ba ko mata nawa zai aura.
Shin wai ni yau bari na tambayeki. Shin wai Hameedu ƙafar Habu Maharbi ya cire ko kuwa ta Bawa? Shin wai Hameedu dukiyar Ladi ya cinye ko kuwa ta Bawa? Shin shi Bawan me yake zame miki ne banda miji? Shin akwai wani jini guda ko da na halittar kaza ne da kika dasa a tsakaninki da Bawan? Kai! Ko kuwa akwai halittar mutum irin wacce uwar Halliru ta bashi, shin ko kuwa banda abinda na sani akwai wani abu tsakaninki da Hameedun..!?"
Sai anan ta cira idanuwanta sama ta dube shi a yayin da wata kwalla guda ta sauko daga kurmin idonta...
Ban taɓa gaya maka ba ne Ya Annur, amman bari yau zan faɗa maka. Wannan matar taka da kake kira da 'da wani abu', ko da baka aureta ba, lalle ne sai jininka ya fita daga jikinta ta kowacce irin saɗara!
Biyo mu sannu a hankali don jin TAZARAR da ke tsakanin Dee Yusuf da Amatullah.
Updates zai dinga zuwa duk ranakun Laraba da laha3.
Ku biyo Ni Safiyyah Ummu-Abdoul tare da Khadija Sidi don jin wannan TAZARAR