Gureenjo6763
- Reads 30,088
- Votes 1,020
- Parts 60
TIME... LOKACI. Lokaci kamar Unit ne da ke barin shaidar wanzuwar abu walau kyakyawa ko mummuna sai dai shin yaushe zai wuce? Ta yaya zai shuɗe? Me ya ke tafe da shi? Allah ne kaɗai masani.. Kaman yadda ƊIGON RUWA kan bushe cikin lokaci ƙanƙani haka na ɗauki jarrabawa ta da ke maƙale bisa zaren ƙaddarar rayuwata... Sai dai kash tawa ɗigon ruwan duk yadda zan fifitata ta gagara bushewa. Na zaɓi zama tamkar tuwon hatsi don juriya sai kuma ya kasance ba komai ne tuwon hatsin ka iya jura ba. Matsi, takura da tsananin rayuwa sun sa na yanke yin mai ɗungurungun wai haihuwa da hanji wurin ɗaukar raina da hannuna saboda ban ɗanɗani wani garɗi ko zaƙi na wannan duniya ba!