A DAREN AURENA(SABON SALO)
Based on True life event
Rayuwa kan zo ma kowa da kalar qaddarar sa, walau khairan ko akasin hakan. A duk yanda ta zo maka da kamata yayi ka rungume shi cikin gode ma Allah akan sauran ni'imomin da ya maka ba tare da sanya damuwa ba. Zainab (Amra) da Fatima (Amma) suna cikin ya'yan da duk faɗin unguwar su babu kamar su. Ba unguwar kaɗai ba h...