KhadijahYusuf483's Reading List
5 stories
FATALWAR MATATA  by karimalawal
karimalawal
  • WpView
    Reads 255
  • WpVote
    Votes 13
  • WpPart
    Parts 8
The story of a wandering ghost seeking for revenge against her untimely death.
SIDDABARU Complete by MuntasirShehu
MuntasirShehu
  • WpView
    Reads 106
  • WpVote
    Votes 33
  • WpPart
    Parts 16
Bayan shekaru biyu da mutuwarta, sai ga hotunanta suna yawo a yanar gizo na gagarumin bikinta da za a yi a jihar Lagos. ko ya abin yake? Duk ƙarshen wata yakan je ziyara ƙabarinta amma a RANA ƊAYA TAK ya nemi ƙabarin ya rasa. ko me ya sa? Samari da dama sun rasa rayukansu. ko me ye dalili? Kabasa, mutum ne amma hatsabibancishi ya sa jinnu shakkar tunkararsa. ko ya abin yake? Ku biyo ni mu ji yadda SIDDABARUN yake
RAYUWAR BADIYYA ✅  by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 278,511
  • WpVote
    Votes 21,592
  • WpPart
    Parts 61
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi. Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai. Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu. _______ Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?
RAYUWAR MADINA! by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 9,211
  • WpVote
    Votes 646
  • WpPart
    Parts 72
Kowanne labari mai kyau ya cancanci ƙarshe mai kyau, duk wanda yayi mai kyau zai ga da kyau, tabbas wannan ba wani labarin soyayya bane. Na sha zafin duniya, na sha azaban da mutuwa bazai bani tsoro ba, amma yanzu ba na jin komai. Ba na jin komai...
FATIMA ZAHRA SA'EED (cmplt Book 1) by MuntasirShehu
MuntasirShehu
  • WpView
    Reads 747
  • WpVote
    Votes 42
  • WpPart
    Parts 11
Labari a kan wani mai kuɗi (Alh. Sa'eed) wanda Allah ya wadata shi da komai na jin dadin rayuwa, sai dai abu ɗaya ne ya gagareshi wanda a kan fafutukar neman abun idanunsa suka rufe ya aikata wani al'amari wanda shi ya zama silar ginuwar labarin. A ƙarshe ya samu biyan buƙatarsa sai dai kuma hakan ya zame masa wani babban ƙalubale a rayuwarsa. A gefe guda kuma labarin ya ƙunshi tsantsar soyayyar uwa da irin sadaukarwarta ga yayanta. Har ila yau labarin na kunshe da rikitacciyar rayuwa da kuma gagarin da ya mace ke fuskanta lokacin da ta rasa komai. Ku dai ku biyo ni sannu a hankali cikin labarin FATIMA ZAHRA SA'EED. Me yasa take kiran kanta da wannan sunan?