TeemahNuhooMuhd's Reading List
11 stories
BAN FARGA BA.. by ayshajb
ayshajb
  • WpView
    Reads 160,369
  • WpVote
    Votes 1,487
  • WpPart
    Parts 22
Hattara dai iyaye masu barin ƴaƴa kuna tafiya aiki maiyasa wasu matan suka fi bawa aikinsu muhimmanci fiye da iyalansu read This novel labarine wadda ya faru a gaske ba kage bane, labarine mai tsuma zuciyar mai karatu da sauraro .....
ALKAWARIN MU by ayshajb
ayshajb
  • WpView
    Reads 42,704
  • WpVote
    Votes 322
  • WpPart
    Parts 12
Labari mai cik'e da Zazzafar Soyayya tausayi Romacing nadama tare da darasin Rayuwa
ƳAN HARKA by ayshajb
ayshajb
  • WpView
    Reads 191,062
  • WpVote
    Votes 1,711
  • WpPart
    Parts 36
,Kamar koda yaushe tana tsaye jikin windo hannunta ɗaya yana riƙe da labulen windon, yayinda ɗaya hannunta yake ɗaure bisa ƙan mararta sai shafa cikin jikinta take a hankali tana lumshe ldo jiki a matukar sanyaye ta sauke labulen tare da zamewa kasa tayi zaman ƴan bori, "yaushe zan ganka har sai yaushe zaku waiwayeni na gaji bana jin daɗi wayyo rayuwa bazan taɓa yafewa duk ...."
SHU'UMAR MASARAUTAR 1 by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 11,167
  • WpVote
    Votes 141
  • WpPart
    Parts 13
"Na sadaukar maka da kishiyata a wannan daren, shi ne tukwicin da zan iya yi maka." Ba ta jira cewarsa ba ta ɗora rigar a jikinta. Bamaguje ya gyaɗa mata sannan ya furta. "Za ku iya tafiya." Umaima ta yi masa jinjina da hannu sannan ta sake ɗiban ruwan da ta wanke fuska da shi ta nufi wurin da Maimuna ke zaune hannunta ɗauke da kunamar da Bamaguje ya damƙa mata. Abin da suka aiwata a farkon zuwansu yanzun ma haka ne ya faru, sai da suka koma daidai wurin da suka buɗe ido suka gan su tun farkon zuwansu sannan, Fulani Umaima ta ɗaga ƙahon ta runtse ido ta busa haɗe da kiran sunan Bamaguje. Ƙamshin ɗakin Fulani ne ya ankarar da Maimuna dawowarsu gida, cike da girmamawa ta zube ƙasa ta furta. "Allah huta gajiya uwar gijiyata."
WUUF HAUSA SERIES NOVEL by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 895
  • WpVote
    Votes 103
  • WpPart
    Parts 10
Abuh bata damu ba ta ci gaba da jijjiga ƙafar tana cewa, "Chogal wallahi ka kiyaye ni, na rantse da Allah idan ka takura wata rana sai na jirge ƙafa na mayar da kai Audu gundul ba audu chogal ba." Tana gama faɗa ta saki ƙafar ta wuce cikin gida, sai a lokacin Abokansa suka ƙarasa suna masa sannu. Alhaji Audu Chogal ya jinjina kai yace, "Ƙwal uba ni yarinyar nan za ta yi wa lalata, ta jawa kanta da wata biyu na yi niyyar a saka rana amma wallahi sati biyu za a saka."
WANDA BAI JI BARI BA.... by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 3,908
  • WpVote
    Votes 272
  • WpPart
    Parts 22
Iska ce ta fara kaɗawa ahankali ta fara hango waɗansu irin manyan ƙwari masu kama a fasalin maguna sai dai kowanne su maƙale yake da fukafuki a gadon bayansa, sautin tafiyar Dokin ce ta ƙara kusantota hakan ne yasa ta maida kallonta ga inda tafi jin sautin na matsowa. Kamar yanda ya bayyanar mata a karan farko wannan karan ma wata zabgegiyar Abaya ta hango baƙa, tsawon abayar ya kece tsawon bishiyoyin dake cikin dokar Dajin sai da ta ɗaga kanta sama sosai sannan ta hango dai-dai kansa sai dai kansa ne amma babu alamar fuska ajikinsa. Ƙarasowa yayi gabanta ya tsugunna cikin murya mara daɗin sauraro ya fara magana, " Bingirsima baguar kinbasu wakisfatminar, kisasu biragu kilbasu tattarakimbas wajihagar, farafafus bintigad gurmanas YUSRA? harbaskila mindadu bar washbasbismas shizas kima bu warsa? " ( A karo na biyu ina ƙara miki barka da zuwa cikin daularmu nida ahalina, da sannu zan gabatar da ke ga sauran iyalaina domin kusan juna keda su ina fatan kina jina YUSRA? Ga ƴaƴana nan sun fara zuwa gaisheki ina fatan zaki basu kulawa ? ) Wannan zabgegen Aljanin ya ƙarasa maganar yana nuna mata waɗannan hallittun masu fasalin Maguna da fukafukai. Yusra da tuni hawaye yake wankewa fuska ta ƙara durƙushewa ƙasa cikin sigar magiya tana faɗin, " Ka dubi girman Allah da Annabi ba dan ni ba, ba dan halina ba kayi haƙuri ka maidani cikin mutane dan Allah, wallahi bazan iya rayuwa cikinku ba na tuba dan Allah kamun rai " Miƙewa tsaye yayi sannan yayi taku biyu zuwa uku sannan ya waigo ya ce mata, " Hargigas markusa bayas tinga " ( Tashi tsaye kije jikin waccen bishiyar kukar ) Yusra har tuntuɓe take da sauri ta miƙe tsaye saura kaɗan Abayar jikinta ta kayar da ita, jikin bishiyar taje ta tsaya tana sauraron abinda zai sake faɗa, batayi aune ba ta tsinkayi muryarsa yana faɗin. " YUSRA Lilbas faragaras binsafa walgibas zalzulfat kinari " ( YUSRA kalli Abayar jikinki da kyau, idan har kin iya cireta daga jikinki
DUBU JIKAR MAI CARBI by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 9,093
  • WpVote
    Votes 276
  • WpPart
    Parts 14
Da sauri Yaya babba ta matsa baya tana zaro ido ta ce, "Dubu me nake gani kamar aski akanki." Dubu ta rushe da kuka ta ce, "Inno wallahi aski ya mini kuma wallahi ɗan iska ne." Cak Yaya Babba ta tana ƙarewa Dubu kallo sannan ta ce, "Dubu je ki can mu gani." Dubu ta tashi tana ƙobare ƙafafuwa saboda irin gwale-gwalen da ta sha. Ba su yi aune ba sai ga ni suka yi Yaya babba ta faɗa ɗaki ta rushe da kuka. Da sauri suka bi bayanta saboda kusan kowa bai ji daɗin abin da Aseem ya yi ba musamman Mahaifinsa, faɗa yake yi masa sosai sannan suka shiga ɗakin. Yaya babba kallonsu ta yi fuska a murtuke ta ce, "Garba ka tara mini ƴan uwanka saboda wannan ba maganar tsaye ba ce. Kuma idan har Aseem ya farke mini Dubu na rantse da Allah ba ita kaɗai ya yi wa illa ba, ya fi kowa shiga uku domin babu makarin maganin ƴan shafi mu lerar da za a bashi. Kai ni wallahi ban lamince ba ke Nafisa ke ce uwarsa wuce ki je ji bincike shi tas, don wallahi Idi ɗan wanzan ya mutu babu wani magani da zai karya laƙanin aikin, saboda aikin har da haɗin ƴan shafi mu lera." Tana gama maganar ta fisgo Dubu tana shafa mata suɗaɗɗen kanta ta ci gaba da cewa, "Ka ga yanda Kan Dubu ya sulle kamar bayan sulba. To kwarankatsa dubu idan har ka farketa kaima haka wurin zai shafe kamar bayan silba." Kallon-kallon aka fara yi da juna, jikin Hajiya Nafisa ya yi sanyi dukda ta san a tarbiyyar da suka bawa Aseem ba zai taɓa yi wa Dubu fyaɗe ba. Amma shaidar ɗan yau bata da tabbas, domin ɗa ne ka haifshe baka haifi halinsa ba. Babban abin da ya fi ɗaga hankalinta da ta ji an ce Aseem ɗin ta ya koma kamar bayan silba. Ita da take yi masa tanadin Yusra ƴar aminiyarta ya aura.
FATALWAR MIJINA by Hafnancy
Hafnancy
  • WpView
    Reads 27,395
  • WpVote
    Votes 1,929
  • WpPart
    Parts 14
Horro
GIDAN FATALWA by abdulkingarticle
abdulkingarticle
  • WpView
    Reads 4,428
  • WpVote
    Votes 169
  • WpPart
    Parts 3
Duk wanda yaga sharri to ya binciki kansa......
GIMBIYA SA'ADIYYA (Aljana Ko Fatalwa?) by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 160,192
  • WpVote
    Votes 19,499
  • WpPart
    Parts 55
Haka rayuwarta ta kasance tsawon lokaci a cikin kwalbar sihiri. sai dai kuma a lokaci guda BOKA FARTSI ya yi watsi da alkawarinsa da KURSIYYA, ya fiddo ta tare da umurtar ta kan cewa ta ci gaba da bibiyar rayuwar KURSIYYA domin ta kwato wa kanta da kuma shi kanshi fansa. Ko wace ce wannan Kursiyyar? Wace ce wannan daga cikin kwalba? Wace irin fansa ce za ta kwatar wa kanta da boka FARTSI? Ku biyo ni a cikin labarin GIMBIYA SA'ADIYYA don jin bayanai game da abubuwa da dama.