khairi_muhd
- Reads 2,004
- Votes 46
- Parts 50
A cikin duniyar da soyayya ke rikicewa da laifi, Uwani ta tsinci kanta tsakanin maza biyu masu tasiri a rayuwarta. Habib, wanda ya fitar da ita daga kangin bautar gida, ya kasance hasken farko da ya haskaka mata hanya. Ta haifa masa yara biyu, amma a lokacin da zuciyarta ta fara tasowa da soyayya, uwargidansa ta fatattake ta da wulakanci. Uwani ta bar gidan cike da ciwo da ƙunci, tana gudu daga soyayyar da ba ta da kariya.
Rayuwa ta sake jefa ta cikin duhu hannun karuwai da kaskanci. Amma Haidar, wani matashi mai zuciya mai taushi, ya zama sabon tauraro a duhun rayuwarta. Ya fitar da ita daga kangin Magajiya ya maido ta makaranta, har ya kai ta ga danginta na
asali.
A yayin da Habib ke kokarin dawo da abin da ya rasa, Uwani na cikin rikici tsakanin ƙaunar da ta rasa kariya da kuma soyayyar da ta samo mafita. Shin zuciyar Uwani za ta koma baya ta rungumi wanda ya jefa ta cikin rana da dare, ko kuwa za ta ci gaba da tafiya da sabon tauraron da ya haskaka mata gaba?
Wannan labari na ɗauke da rikitarwa, alhini, da gasar soyayya mai zafi inda zuciyar ɗaya ke iya kashe soyayyar biyu.