HurairaAdamuBilkodi9's Reading List
153 stories
RUBUTACCIYAR K'ADDARA by SafiyyahGaladanchi
SafiyyahGaladanchi
  • WpView
    Reads 34,145
  • WpVote
    Votes 2,102
  • WpPart
    Parts 36
LABARIN UWA DA Y'AR TA WANDA YAKE CIKE DA TAUSAYI DA AL'AJABI, KUYI KUTSE A CIKI DOMIN GANIN ABINDA YAKE FARUWA.
MUNA SON JUNANMU by AliyuSIbrahim0
AliyuSIbrahim0
  • WpView
    Reads 1,822
  • WpVote
    Votes 7
  • WpPart
    Parts 78
"GABATARWA" - A Yanayin Da Take Ciki Na Buƙatar Kulawar Mahaifi Data Rasa Tsawon Shekaru '15', Da Kewar Mahaifiyarta Wacce Basa Tare Tun Yarintar Ta. - Wata Ƙaddara Ta Haɗe Zukatan Su Waje Ɗaya, a Cikin Duniyar Qaunatayya Mai Cikeda Ababen Mamaki Da Burgewa. Ta Fara Hangen Kanta a Matsayin Mafi Sa'a Da Samun Nagartaccen Masoyi, Wanda Ya Shirya Bada Rayuwar Shi Gareta. - Sai Dai Lokaci Ɗaya Cikeda Rashin Tsammani Al'amura Suka Sauya, Wani Sabon Babi a Littafin Ƙaddarar Data Haɗa Zukatan Su Ya Sake Buɗewa Cikin Soyayyar Tasu, Cikin Yanayin Ɗimuwa Da Tashin Hankalin Daya Jefa Bugun Zuciyoyin Su Cikin Rashin Tabbas. - Amma Har Izuwa Karshe Rubutacciyar Kalmar 'Muna Son Junan Mu' Ta Gaza Gogewa Acikin Zukatan Su.
RAYUWA TA....(ƙaddara ta) by leemaMuhammad826
leemaMuhammad826
  • WpView
    Reads 4,873
  • WpVote
    Votes 190
  • WpPart
    Parts 65
RAYUWA DA ƘADDARA wasu kalmomi ne guda biyu masu sauƙin ambata a baki amma kuma,masu wuyar fahimta. Ko wane ɗan Adam da yanda ubangiji ya hallice shi,ya ƘADDARO yanda RAYUWAR shi zata kasance tun daga haihuwa har ya koma ga mahallicin shi. Mutane da dama na shan matuƙar wahala a RAYUWAR su saboda rashin amsan ƘADDARAR RAYUWA a yanda tazo masu wanda shi kan shi gaba ɗaya RAYUWAR ɗan adam ba'a bakin komi take ba amma ga wanda ya fahimta kenan. Yarda da ƘADDARA mai kyau ko akasin hakan na daga cikin rukunan imani. Saboda haka,a duk halin da bawa ya tsinci kan shi a duniyan nan ya rungumi ƘADDARAR RAYUWAR shi da hannu biyu cike da imani.
NADIYA! by jeeedorhh
jeeedorhh
  • WpView
    Reads 4,906
  • WpVote
    Votes 76
  • WpPart
    Parts 8
'Ta dan juya kanta cike da mamaki, tace, "Daddynka kuma? wanene shi?" Yace, "Habib Abdullahi Makama?!" cikin sigar tambaya. Jin sunanshi kadai ma sai daya sanya taji bugun zuciyarta ya canza. A duka kwanakin da suka wuce tun bayan daya ajiyeta a kofar gidansu ya wuce, karya take yi tace babu wata rana da zata fito ta koma ga mahaliccinta bata tunano wannan mutumin ba. Abin har ya kusa zame mata jiki, yin tunaninshi a lokacin da taje yin kwanciya barci. Wasu dararen kuwa har da mafarkinshi da tunanin wannan daddadan kamshi nashi, wanda ta lalubo turaren da yake amfani dashi cikin wadanda ya bata, itama ta mayar dashi nata turaren. Yaudarar kanta take, da take cewa wai tuni ta manta da sha'aninshi da kurar data kwasoshi. Ita tasan karya take yiwa kanta. Duk kuma yadda taso abinda ke tukarta a zuciya kada ya bayyana, sai daya bayyana din. Ta rasa fara'ar kirkirowa tayi koda ta yake ce kuwa, haka bugun zuciyarta ya ki saisaituwa duk yadda taso ta saisaita shi kuwa. Ta daure dai da kyar tace, "ok, na ganeshi. Yana ina yanzu?" Ya dan daga kafada, "ban sani ba nima. Kawai dai yace in zauna a wajenki zai dawo ya daukeni." Ita abin ma sai ya girmame mata, mamaki ya hanata motsi. To ita kuma a su wa? Kuma da wane dalili? Da zai dauko danshi ya kai mata?..." To domin sanin dalilin, don me, kuma me yasa? Sai ku biyoni Ni Jeeddah Lawals tare da Nadiya a wannan tafiyar tamu.
AL'AJABIN SO by Gureenjo6763
Gureenjo6763
  • WpView
    Reads 8,671
  • WpVote
    Votes 66
  • WpPart
    Parts 26
Tarihi yana nuna mana abubuwan da suka faru ne kafin mu a rayuwa! Rayuwar duniyar cike take da kalubale, haɗari, wahalhalu da musibu daban-daban, kusan in ka ga ka gujewa hakan to fa alƙalamin ƙaddara bata zana maka ita a shafin ƙaddararka ba, a lokacin da kaddara ke wasa da rayuwarka ya rage maka ɗaukan wannan kalubale a matsayin darasi, ka kuma yi haƙuri da jarabawar Allah (S.W.T) a gare ka. Ni Fatima ban taɓa sanin cewa igiyar ƙaddarar wani na iya shafan na wani har su sarƙe wurin zama abu guda ba sai da na tsinci kaina cikin alkaba'in rayuwa, zafi da kunci suka yawaita a gareni, farin ciki yayi min nisa irin tazarar dake tsakanin sama da ƙasa, na kasa tantance wai ƙaddarar wanene ya shafe ni, shin na mahaifiyata ne ko na mahaifina? Ko kuma nawa ne ni a karan kaina ba'a tsaga ni cikin masu rabauta da duniya ba? A mafi yawancin lokuta in har nayi irin wannan tunani, na kan samu kaina ne da yiwa gwanin halitta godiya da bai sa mana wani tabbataccen al'amari ba, farin ciki ko baƙin ciki yana da lokaci, komai kuma yayi farko to fa yana da karshe, wani karin maganar ma sai ya ce abinda ya baka tsoro a yau babu shakka ko tantama a gobe ya iya baka tausayi, rayuwar tamkar tafiyar hawainiya ce tana tafe tana chanza launi. Al'amuran da suka faru a rayuwata sun sanya min karsashin bayar da labarina.
Zuria Daya(rikicin cikin gida) by MaryamAbdul559
MaryamAbdul559
  • WpView
    Reads 43,796
  • WpVote
    Votes 2,417
  • WpPart
    Parts 61
Labarin ZURI'A DAYA(RIKICIN CIKIN GIDA) labari mai dauke da makirci irin na cikin gida, sadaukarwa, soyayya, hassada, kiyayya, dama dai sauransu mai karatu kaidai biyoni kasha labari.
MUGUN ZALUNCI by uwanibachaka
uwanibachaka
  • WpView
    Reads 13,707
  • WpVote
    Votes 651
  • WpPart
    Parts 36
MUGUN ZALUNCI Labarin Ruk'ayyatu, tana tsaka da rayuwa da mijinta Lami'do mutuwa ta raba tsakanin su, bayan wani lokaci Ruk'ayyatu ta auri Abubakar, Abubakar yanada mata Mimi, Mimi mace mai tsananin kishi, zata iya aikata komai akan kishi, ya rayuwar Ruk'ayyatu zata kasance a gidan Abubakar
RUƊIN DUNIYA! by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 15,643
  • WpVote
    Votes 707
  • WpPart
    Parts 77
The lives of some sisters. Haƙiƙa Ina matuƙar son kuɗi, ji nake yi idan babu su kamar bazan iya rayuwa ba, ɗaukar da nayi musu su ne suke kare mutunci, sannan kuma su ne suke sa wa a yi maka soyayya, ashe ba haka ba... Tabbas kuskure. nayi su da dama, amma ina ganin kamar ana sake ba ma mutum damar sake kura-kuran sa, ban taɓa sanin wata soyayya ba, face soyayyar da na maka....
RAYUWAR MADINA! by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 8,948
  • WpVote
    Votes 646
  • WpPart
    Parts 72
Kowanne labari mai kyau ya cancanci ƙarshe mai kyau, duk wanda yayi mai kyau zai ga da kyau, tabbas wannan ba wani labarin soyayya bane. Na sha zafin duniya, na sha azaban da mutuwa bazai bani tsoro ba, amma yanzu ba na jin komai. Ba na jin komai...
ƳAR IYA (Mai hannun ɓarna) by Diamond_Bhatool
Diamond_Bhatool
  • WpView
    Reads 1,029
  • WpVote
    Votes 11
  • WpPart
    Parts 69
Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love.