WUUF HAUSA SERIES NOVEL
Abuh bata damu ba ta ci gaba da jijjiga ƙafar tana cewa, "Chogal wallahi ka kiyaye ni, na rantse da Allah idan ka takura wata rana sai na jirge ƙafa na mayar da kai Audu gundul ba audu chogal ba." Tana gama faɗa ta saki ƙafar ta wuce cikin gida, sai a lokacin Abokansa suka ƙarasa suna masa sannu. Alhaji Audu Chogal ya...