Fantasy Books
4 stories
H U R I Y Y A by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 18,793
  • WpVote
    Votes 657
  • WpPart
    Parts 16
Wata rayuwa ce zan taɓa ta Hausawa, wani ɓangare na ƙabulan da yara suke fuskanta a gidan iyayensu, tun farko tashi har girma, wani abu ne da nake ta hangowa kuma na daɗe da ƙishin son rubutawa. ••• ••• H U R I Y Y A -Labari ne mai ban tausayi da taɓa zuciya. Story of the Year 2023... Be kind to every human being, because you don't know the whole story and matter what you are facing never give up. You don't know what the future holds...
TA ƘI ZAMAN AURE... by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 15,051
  • WpVote
    Votes 459
  • WpPart
    Parts 19
"Ni ma ina da buri, ina da mafarkai irin na kowace mace, sai dai kuma kaddara ta shata min layi, yadda alƙalamin ya zana dole haka zanbi... Daga lokacin da na fahimci haka, sai tsoro da fargabar me zai faru a gaba ya fice a zuciyarta. Tafiyar da babu dawowa ta zama dakuna..." TA ƘI ZAMAN AURE... Share fagen wata tafiya ce mai sarkakiya da daure kai. Wata kalar kaddara ce mai rikitarwa, shimfida ce dake lalaye tafiyar wasu daidaikun mata.... Tafiya ce ta irin matan da duniya ta canja musu zane, suke da wani rufaffen sirri a zuciya! Sai dai kadan daga masu ilmi ke fahimta. A cikin rayuwa akwai mutuwa haka ma a cikin mutuwa akwai rayuwa shim kun ankara da haka? Mabudin kowace kofa makulli ne sai dai wannan kofar a balleta ne ta kasa, sai shigar cikinta ta kasa yi ma mai dakin dadi. Al'umma sun kasa yi mata uzuri iyayenta sun kasa fahimta, mazajen kuma sun kasa riko...? Uba na gari jigo, sai dai ita bata dace ba, miji na gari gimshiki a nan din ma dai bata dace ba, kuma duka laifin yana komawa zuwa gareta ne.... Duniya ta yi mata juyin masa, ta yadda ta kasa banbance fari da baki, ji da gani sun mata nisa, albishin daya take jira... mutuwa...!
KHADIJATUU by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 286,718
  • WpVote
    Votes 24,841
  • WpPart
    Parts 66
NOT EDITED ⚠️ Yayi kyau matuƙa, yadin ya fito da farinsa da kuma kyaun fuskarsa, Idan ka kalleshi, sai ka ganshi kamar mai cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali, al-halin sune abubuwan da suka masa tawaye. A hankali ya sauke ajiyar zuciya yana lasa lip ɗinsa. Juyowa yayi yana wani taku da idan baka karance shi ba, zaka iya cewa na wulaƙanci ne da nuna isa, al-halin babu hakan a tare da shi ko kaɗan, ƙarasowa yayi gun da Khadijatu take kwance ya duƙo daidai ita, ya hura mata iska a fuska kamin ya kai hannu ya taɓa jikinta. Hannun yasa ya tallafota ta dawo saman cinyoyinsa, fuskarta na fuskantar tasa, ido ya sakar mata kamar yau ya fara ganinta, a hankali ya kai hannun ya shafa gefen fuskarta, tausayinta ne yake ƙara shiga zuciyarsa. Shi kansa yana ji a jikinsa akwai wani sirri dake tsakaninsa da haɗuwarsa da Khadijatu, sirrin da har yanzu bai san na minene ba, yana jin shi ɗin wani bangone a shafin rayuwarta, lallai idan har babu shi a ƙaddarar Khadijatu toh babu wanzuwar labarinsa a doron ƙasa, yana ji a jiki da kuma ruhinsa domin ita akayi shi, kamar yadda yake jin da a'ace ya rabu da ita tsakanin jiya zuwa yau da bai san yadda rayuwarsa zata kasance ba, bai san wane irin hali zai samu kansa ba, dan baya taɓa rasa natsuwarsa idan yana kusa da ita, idan tayi nisa dashi ji yake kamar ya rasa wani ɓangare na jikinsa. Ba sonta yake ba, dan baya tunanin zai iya buɗewa wata ƴa mace zuciyarsa, tun bayan abunda Malak tayi masa, sai dai kuma yana jin fiye da yadda yake ji idan yana tare da Malak, yana jinsa cikin wani yanayi wanda bai taɓa ji ba idan yana tare da Malak. ® 2018
DEENAH by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 48,026
  • WpVote
    Votes 3,359
  • WpPart
    Parts 14
The beginning of another life. suspicious, terrified, remorseful. DEENAH...! ®2015 NOT EDITED ⚠️