maigwanjo01's Reading List
5 stories
HAIRAN🔥💥♥️ by Shatuuu095
Shatuuu095
  • WpView
    Reads 6,854
  • WpVote
    Votes 160
  • WpPart
    Parts 23
Tunda Anty ta fara magana, Prof yake kallon ta, idan ka kalle shi ba zaka taba fahimtar a yanayin da yake ciki ba, ba zaka fahimci emotions din shi ba, Amma yadda yake kallon Anty, da yadda ya bata dukkan hankalin shi, Abu ne da zai tabbatar maka cewar maganar babba ce. Anty ta gama bayanin ta tsaf sannan tayi shiru tana jiran ganin hukuncin da Prof zai yanke. Cikin nutsuwa yace " A Ina ta samu?" Shi ne tambayar da yayi ma Anty, maimakon tayi masa bayani se cewa tayi " Ai na Gama nawa professor, abin da ya rage kaji ta bakin HAIRAN kawai!" "Me yasa Anty?" Cike da nutsuwa tace " Saboda zaka ga kamar kare ta nake, Amma idan tayi maka bayani Ina Jin zaka fi gamsuwa da kyau!" Daga haka Prof yayi shiru Yana son ya auna nauyin Abubuwan da Anty ta fada Masa, se kawai ya Mike yayi ma Anty sallama ya fita. Kunsan yadda tsumma yake idan aka tsoma shi cikin ruwa ko? To haka Prof yayi, gaba daya jikin shi ya saki, yayi shiru tamkar wani kurma, ya bude mota ya shiga ya kifa Kan shi akan steerer wheel, shi yasa take fada Masa lallai lallai se sun rabu kenan? To Ina ta samu shi ne tambayar da take zuwa Masa... *** Shigowa ta kenan daga lecture, na gaji, gajiya kuwa matuka saboda shirin exams da muke, har lokacin bana cikin dadin rai, Abu ya kusa wata daya Amma still nukurkusa ta yake Yi. Ina Zama Saman gado Ina kallon Nuriyya da ta dakko wani gari tana kokarin kwaba shi da ruwa nace " Me zakiyi?" Tace "Kunun aya Mana!" Se nace " Kunun Aya Kuma, gaskiya Kin iya bawa Kai wahalar, ana shirin exams din!" Tayi dariya tare da daga min wata transparent ziplock tace " Waye zai Baki wani wahala, wannan ai is outdated, halan Baki San Islah foods ba ko? To ita take siyarda wannan garin na kunun Aya, yours is just to make little effort se ki Sha!" Nayi murmushi Amma kafin nayi magana se Naga Kiran Anty na shigowa cikin waya ta, da sauri nayi excusing Kai na sannan na mike Dan fita
MAI SAƘO (DAGA NEMAN GIRA) by 68Billygaladanchi
68Billygaladanchi
  • WpView
    Reads 3,243
  • WpVote
    Votes 96
  • WpPart
    Parts 32
Rayuwata duhu ce! rayuwata ni kaɗaice a cikinta! Rayuwa ta na neman haske duk da bazata taɓa inganta ba, anya zan iya kuwa???????
H U R I Y Y A by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 18,655
  • WpVote
    Votes 657
  • WpPart
    Parts 16
Wata rayuwa ce zan taɓa ta Hausawa, wani ɓangare na ƙabulan da yara suke fuskanta a gidan iyayensu, tun farko tashi har girma, wani abu ne da nake ta hangowa kuma na daɗe da ƙishin son rubutawa. ••• ••• H U R I Y Y A -Labari ne mai ban tausayi da taɓa zuciya. Story of the Year 2023... Be kind to every human being, because you don't know the whole story and matter what you are facing never give up. You don't know what the future holds...
BAKAR WASIKA by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 25,187
  • WpVote
    Votes 1,093
  • WpPart
    Parts 11
BAƘAR WASIƘA... Mai farin rubutu Ban ce tafiyar mai sauki ba ce. Ban muku alkawarin zallar soyayya ba. Ban ce babu farincikin ba. Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki. Labarin Talba, Rafi'a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal da kuma Aminatu. Labarin BAKAR WASIKA, labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta... Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira! A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi. Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke? Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa? BAKAR WASIKA... JUANURY 2022
SAIFUL_ISLAM..💞(COMPLETED✅) by missxoxo00
missxoxo00
  • WpView
    Reads 42,286
  • WpVote
    Votes 2,065
  • WpPart
    Parts 20
Labarin sarqaqiyar rayuwa, Makirci, Hassada, da tsantsar mugunta. Gefe d'aya kuma labarin SAIFUL_ISLAM labari ne dake tafe da luntsumammiyar soyayya marar gauraye👌🏾 SAIFULLAH DA ISLAM (SAIFUL_ISLAM).. Its just a romantic love story.. DONT be left out😘😻