Hausa
5 histórias
AMAREN BANA de ummyasmeen
AMAREN BANA
ummyasmeen
  • Leituras 141,891
  • Votos 9,279
  • Capítulos 17
#9 in romance on 05/09/2016 "Wai ina son ki fada min, me yake damun ki ne, da za ki haddasa irin wannan fitina, sannan ki zauna lafiya, kamar ba abinda ya faru?" Dubansa ta yi a sanyaye, sannan ta-ce. "Ina da dalilina." "Wane irin dalili ne, zai sa ki na ji, ki na gani auren iyayenki ya mutu? Idan banda irin gurguwar tunani irin naki? Ashe ki na da halin yin gyara a wannan al'amari, ba za ki yi ba?" Mikewa ya yi daga kan kujerar zai tafi, da sauri ta kamo bakin rigarsa, ya tsaya, ganin zai saurareta, ya sa ta sakar masa riga. "An fada maka ni ma ina jin dadin ganinsu da na ke yi a haka ne? Sam, ba son raina bane, amma na daure na kauda kaina, saboda mu kawar da gagarumar matsalar da ta fi wannan. Na san halin Momi, tana da fada, tana da rashin son gaskiya, amma kuma haka tana da saurin nadama, na san za ta nemi afuwa, kuma Abba zai saurareta. Sai dai wannan tafiyar, dole ka taimaka ka ba ni goyon baya, don mu shawo kan al'amarin nan tare." Kallonta ya yi, ita ma duk ta jikkata, ta jejjeme ta zama wata iri, tabbas yadda take ji haka yake ji, koma fiye, don bayan baya sonta, ya tsani uwarta, sannan yana mutuwar son Meena. "Ki yi hakuri, amma ba zan iya aurenki ba." Ranta ya baci kwarai, har ya juya zai fita ta-ce. "Saboda me ya sa ba za ka iya aure na ba? Saboda me ya sa ban kai matsayin na zamo matarka ba?" "Ki fada min, ta yaya zan iya zama dake, alhali ki na matsayin 'yar matar da na tashi da tsanarta a zuciyata?" "Wane irin dalili zai sa maka tsanar mahaifiyata, har da zai sa ni ba za ka iya aurena ba?" Shiru ta yi don ta ji dalilin wannan tsanar.
Al'amarin Zucci de ummyasmeen
Al'amarin Zucci
ummyasmeen
  • Leituras 273,910
  • Votos 16,698
  • Capítulos 26
#13 in romance hot list. 25/1/2017 Still faring high after months of completion. Thank you. A duniyar Aneesa babu abinda ya kai mata Innarta muhimmanci, gashi Innarta ta tura ta birni ta zauna da mutumin da bata taba haduwa dashi ba iya rayuwarta. Shin Tafiya birni zai rufe duhun dake cikin rayuwarta ko kwa zai yi sanadin tono abubuwa masu daci? Ba abunda Sagir Daggash yake so a macen aure sai wayewa, ilimi, sanin ya kamata da iya magana ta yanda zata iya raka shi duk inda zai shiga a duniya cikin harkokinsa, su halarci dinner parties. Mace kyakkyawa ajin farko, wacce zata rike masa kasuwancinsa idan ya matsa. Abokansa sukan masa tsiya da cewa sekatariya yake nema ko macen aure? Yanzu, daya daga cikin richest bachelors a gari an manna masa hadin gida da macen da kaifin hankalinta bai wuce na 'yar firamare ba, bata da ilimin boko bare na kasuwanci macen da ta girma a kauye futuk! yanda babu yanda za ayi ace ta taba jin kalmar dinner party. Shin yaya auren nan zai yiwu? Ko Sagir zai watsar da batun ya munanawa mahaifinsa da yake kan gangarar mutuwa? Shin zamu ga wedding of the decade? Biyoni a labarin Al'amarin Zucci don jin yanda zata kaya. Azizah Idris Muhammad.
BA SON TA NAKE BA | ✔ de fadeelarh1
BA SON TA NAKE BA | ✔
fadeelarh1
  • Leituras 342,276
  • Votos 26,138
  • Capítulos 49
"BA SONTA NAKE BA" Shin dagaske ba sonta yake ba? Shin ita din son shi take??
UMMI | ✔ de fadeelarh1
UMMI | ✔
fadeelarh1
  • Leituras 197,814
  • Votos 18,560
  • Capítulos 54
Ta tafka babban kuskure a rayuwarta... Shin zata iya gyara wannan kuskuren ko kuwa??
Labiba de bilkyysu
Labiba
bilkyysu
  • Leituras 156,823
  • Votos 14,612
  • Capítulos 32
COMPLETED English/Hausa For someone who has never had it easy in life, Labiba believed her world has finally come to an end when she was practically forced into marrying her dead sister's husband. But if there's one thing that'll make her tolerate Salim Magatakarda, it's Laila, his one year old daughter who just happens to be her niece and the love of her life.