SirLawal's Reading List
3 stories
A JINI NA TAKE by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 69,455
  • WpVote
    Votes 3,091
  • WpPart
    Parts 12
Labari ne daya kunshi masarautu biyu; Masarautar Katsina, wacce take cikin Nigeria da kuma Masarautar Damagaran, wacce take cikin Kasar Niger. Labarin yayi duba ne da rayuwar Yarima Bilal, wanda rashin magana da miskilanci ya kanja ya shiga tarun matsaloli, wanda hakan yake haifar mashi da auren Zeenah Kabir Muhammad. Diyar Bafade da kuma baiwa. Me zai faru a rayuwar auren da aka hada miskili da kuma masifaffiya? Wanda dama tun farkon haduwarsu da masifa aka fara har yakai ga ya kure hakurinta ta sharara mashi maruka biyu? Shin ko zasu samu zaman lafiya kuwa? Bilal wanda ya kasance zuciyarshi a kulle take tun bayan rasuwar mahaifiyarshi zai bude ma Zeenah ita? Ya rayuwa zata basu bayan Zeenah ta fada soyayyarshi sai kwatsam Juwairiyya ta kunno kai? Wane hali Bilal zai shiga a lokacin da Fulani ta bankado wani tsohon sirri dake tsakaninsu? Fulani fah? Wacce take uwar gida kuma mai kula da hidimomin Masarautar Katsina gaba daya? Zata rufe sirrin data gano tsakanin Zeenah da Bilal dan gujewa tarwatsewar farin cikinsu? Abu daya ne zai kai ga na biyu, wanda har Bilal zai tsinci kanshi an mashi shamaki da Masarautar Katsina, hakan zai dangantashi da Masarautar Damagaran! Ku biyo Yar Malumfashi domin jin yadda labarin zai kasance.
MENENE MATSAYINA... by Hafssatu
Hafssatu
  • WpView
    Reads 59,473
  • WpVote
    Votes 2,578
  • WpPart
    Parts 53
"Don ubanki wanki dana barmiki kimin shine kika kiyimin Kika zauna kika rungume wannan shegiyar d'iyar taki wallahi koki aje ta ko kuma yanzu jikin ki ya gayamiki nafada miki banza..." Fuskar jike da hawaye ta d'ago ta kalleshi cikin kyarmar murya tafara Magana Haba! Noor...marin dataji a fuskar ta ne yasa bata Ida fadar Abinda ke bakin ta ''shegiya tun yaushe na haneki da furta wannan sunan gareni wallahi duk ranan danaji kin kara Ambata ta da wannan sunan na lahira sai yafi jikin dadi jaka kawai ball..yayi da ita daga ita har d'iyar dake hannun ta goshin ta ya bugu da bango d'iyar dake hannunn ta tsayanra kuka tare da Ambatar Umme... ''Kafin nadawo gidanan ki tabbatar da kimin wanki sannan kingyara min dakina nafada Miki.."" Juyawa yafita yabarta rushewa tayi dawani matsanancin kuka mai tattare da tausayi hannu taji da fuskar ana share mata hawaye "Ummee kidaina kuka kitaci mutafi gun Umman ki ko Uncle Abdul..." Rungume ta tayi.."zamuje Basmah Amma inaje gunsu *MENENE MATSAYINA..?* "............ _Menene matsayina? Labari mai cike da tausayi fadakarwa.. butuulci #Soyaya #Shakuwa #Tausayi #
Tsohuwar Soyayya (Best Hausa love story) by BestHausaNovels_
BestHausaNovels_
  • WpView
    Reads 17,195
  • WpVote
    Votes 351
  • WpPart
    Parts 13
Labarin soyayyar Aaliyah Badamasi Bulama da Sa'eed Aliyu Modibbo a shekarun 80's...