Great Biologist
200 stories
MIJIN ARO  by rahmakabir
rahmakabir
  • WpView
    Reads 4,677
  • WpVote
    Votes 37
  • WpPart
    Parts 20
Yana karya zuciya, akwai saka nishadi, sannan zai saka ku farin ciki,kyakkyawar karshe
'YAR SHUGABA by rahmakabir
rahmakabir
  • WpView
    Reads 51,895
  • WpVote
    Votes 3,129
  • WpPart
    Parts 40
*'Yar Shugaban k'asa ce* Queen Basma, ta hakimce a seat d'in baya ita kad'ai, sai Meena 'yar Governor Kaduna ce ita ke driving, sai Leema 'yar Sarkin Kano wacce take gefen Meena. K'aran wak'ar Music na Larabawa ke tashi a motan, dukkan su suna bin wak'ar tamkar sune suka rerata, sunayi suna rawa da jinsu da kad'a kai, kana ganin su kaga 'ya'yan gata, cike suke da farin ciki fal da nishad'i, domin ba suda wata damuwa ko matsala a rayuwansu. Motan baya itama na bodyguard ne, suke marawa motan Queen baya. Wani Matashin Saurayi wanda bai wuce shekara Talatin ba (30yrs), yake tafiya cikin sauri domin ya amso wa Ummansa nik'an masara da k'anwarsa Khadija ta kai ta aje, saboda zata wuce tallan kwai, hankalinsa yayi nisa sosai cikin tunani, baisan yahau kan titi ba. Meena ce taja mugun burki, ji kake k'iiiii kad'an ya rage ta buge shi, Aryan tsayawa yayi cak ya runtse ido yana fad'in *Innalillahi wa inna ilaihir rajuun* jira yake motan ta bigeshi domin ya riga ya sadak'ar motan zata kad'eshi, Cikin b'acin rai Queen Basma, Leema, Meena duk suka fito a motan, haka bodyguard suka yi parking akan hanya suka fito rik'e da bindigogi, cikin k'ank'anin lokaci suka had'a gosilo, mutane suka fara taruwa, ganin bindiga ne yasa kowa ya kama kansa, Queen Basma ta k'arasa kusa da Aryan bodyguard suka take mata baya, tsadadden k'amshin turarenta ne ya dawo da hankalin Aryan jikinsa, domin ji yayi wani k'amshi na ratsashi, bud'e ido yayi a hankali yayi tozali da kyakkyawar fuskan Queen wanda saida gabansa ya fad'i, nan take tsoro ya ziyarce shi, kallon k'asa da sama Queen Basma ta bisa dashi cike da jin haushinsa, kyamansa taji saboda wani irin warin zufa dake tashi a jikinsa, tattaro miyon bakinta tayi ta tofa masa a jikinsa tare da toshe hancinta da hankacif.
ƘADDARATA by Kamala_Minna
Kamala_Minna
  • WpView
    Reads 45
  • WpVote
    Votes 4
  • WpPart
    Parts 1
Gajeran labari.
DUNIYARMU (Compelet) by Kamala_Minna
Kamala_Minna
  • WpView
    Reads 33,911
  • WpVote
    Votes 1,577
  • WpPart
    Parts 41
ko wacce kaddara akwai yarda take fadowa cikin duniyar dangin rai ta dadi da akasin ta zuciyoyi mafi ragwata ba su fiye daukar kaddara ta ko wani hali ta zo musu ba ba sa duba da yanayin rayuwar Duniyarmu da yarda Allah ya tsaga ga ko wani dangin rai zai yi ta mafiyan dangin rai zuciyoyi na kai su ga daura hannu aka su kurma ihu suna mai furta sun shiga uku wasu kuma masu jaruman zuciya murmushi suke su na mai cewa sun shiga aljanna
RANAR NADAMA (Completed by Kamala_Minna
Kamala_Minna
  • WpView
    Reads 13,451
  • WpVote
    Votes 433
  • WpPart
    Parts 10
BUNAYYA da RUKAYYA sun kace cikin wani.irin yanayi na rayuwar aure mai ciki da kayan tashin hankali da kashe zuciya da gurguntan da kwakwalwa sun rasa tunani a lokacin da ba su yi tsammani ba duk hakan ya faru a DALILIN DA NAMIJI wanda ba su taba zanto hakan za ta kasance
KAZAMIN BURI! (Completed by Kamala_Minna
Kamala_Minna
  • WpView
    Reads 485
  • WpVote
    Votes 20
  • WpPart
    Parts 1
yawan matasan mu maza suna shiga wata rayuwa mai dauke da bahagon yanayin da kwazazzaban tashin hankali gami da kayan kwadayi da ƙawa irin na zuciya da yawa matasan mu maza suke fuskantan ruɗin zamani da ruɗin abokai marasa tsoron Allah da yawa matasanmu sun shiga rayuwa gariri da yawa matasanmu sun shiga tashin hankali wanda yake barazana da rayuwarsu duk a dalilin...
NAƘASAR ZUCI...(Completed) by Kamala_Minna
Kamala_Minna
  • WpView
    Reads 428
  • WpVote
    Votes 9
  • WpPart
    Parts 1
'Ina kika dosa?'. Na ji wani sashi na zuciyata ya sanar da ni hakan. Sosai na ji duniyar ta sake hautsine mani, ba abin da nake tunawa sai maganar mahaifina a ranar da aka daura mani aure na zama matar Adamu. "In har kika yi sake wani abu ya fallasa akan lamarin nan, kar ki sake ki tunkaro mani gida, ki nemi wani wajan da za ki kafa rayuwarki".
UKU BALA'I (Completed) by Kamala_Minna
Kamala_Minna
  • WpView
    Reads 67,173
  • WpVote
    Votes 3,742
  • WpPart
    Parts 77
"kin gama aikin ki don haka ga tukuicin ki". Ya fadi yana sanya hannu cikin aljihunsa yana zaro bandir din yan dubu dubu guda biyu ansa tayi tana mai kau da fuska kamar bata so ba. "Sannan kuma wannan lamarin ya kasance tsakanina da ke in har naji labari mai kama da shigen wannan lamarin kin san Allah sai kin bar filin duniyar nan". Ya karashe fuskarsa a daure kamar bakin hadarin dake kokarin zubda ruwa. Ko a jikin ta bata nuna damuwa da maganganunsa ba illa tsaki da tayi can kasar makoshi ta na balle murfin motar ta fice Khairiyya dake takure bayan mota ta duba da wani irin yanayi na tausayawa tana faman gyaɗa kai kafun ta dubi Alhaji Mati. "batar da sunanka sananne ka aro na banza ka sakawa kan ka akan wani KUDIRI naka na daban...Uhmm ba na ganin wanda ya isa rikakken mutum mara tsoro zai fito da wannan salon na boye sunan sa domin duk wanda yake so ya fado DUNIYAR SHAHARA a wani fanni da sunan sa ya kamata a san shi ko an rufe babin sa ba za taba mantawa dashi ba da abin da ya aikata". Tana gama fadin haka ta buga murfin motar da karfi yan yatsunta biyu ta dagawa Khairiyya wacce a wannan lokacin ta dago da kanta tana dubansu su duka biyun cikin yanayin na rashin inda suka dosa a tsakanin su. "Hajiya Layla" Ya fadi da murmushin mugunta a laɓɓansa kafun ya dora. "...abu daya zai sa na kyale ki a filin duniyar nan shi ne wannan yarinyar da kika bada takomashin taimako har na same ta saboda ita ce hanyar samun arzikina da nake burin cimma wa wannan dalilin zai hanani yi miki komai amma duk da haka ki tsumaye ni ina nan tafe". yatsine fuska tayi kafun ta juya ta fara takawa kan kafafuwanta. Dariya yake yi sosai da sosai har yana buga sitiyarin motar kafun ya tsagaita kamar daukewar ruwan sama fuskar nan tashi ya haɗe ta waje daya kafun yayi wa motar ki ya fizge ta kamar mai kokarin tashi sama.
MATAR MIJINA...Completed by Kamala_Minna
Kamala_Minna
  • WpView
    Reads 37,563
  • WpVote
    Votes 2,661
  • WpPart
    Parts 92
...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi amanna da bukatar Jaamal Bukar Kutigi ba, in tayi duba da halaccin da Sumayya Attahiru Kangiwa tayin mata, a filin duniyar rayuwarta.Butulci take kallon lamarin, butulci mafi girma wanda in har mutanan duniya suka ji,ta sani za suyi mata tofin Allah tsine...
...YA FI DARE DUHU by rashkardam
rashkardam
  • WpView
    Reads 64,056
  • WpVote
    Votes 3,350
  • WpPart
    Parts 40
Labarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.