habiba1986's Reading List
12 stories
NANA AMINATU 2022 by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 18,228
  • WpVote
    Votes 946
  • WpPart
    Parts 56
Maganganun ta tamkar saukar kibiya take jin su a zuciyarta duk idan ta tuna, suna sukan ta su hana ta sukuni, suna tarwatsa ta su saka ta taji ita ƙasƙantanciya ce wacce bata kai ɗin ba kamar yadda take cewa, tana ganin baƙin kanta a koda yaushe a wacce bata kai ba, ko kaɗan bata taɓa saurara mata ba, ya za'a yi ta dena kallon kanta ta daban a cikin mutane yayinda take tuna duk wata kalma ta ɓatanci da take bin ta dasu a kullum ranan duniya? tun sanda ta buɗe idanuwanta da wayon ta take jin waɗannan munanan kalaman da ke tarwatsa mata duk wani farin ciki da jin daɗin ta. Sai dai kuma a duk sanda take jiyo kalaman sa sai ta ji ƙwarin gwiwa har ta kalli kanta a wacce ta kai kuma ta isa, ashe akwai ranan da zata yi farin ciki haka? Akwai ranan da wani zai iya yabon ta har ya nuna mata tana da matsayi fiye da sauran Mata? She can't believe that... Shi ne Mutum na farko da yake faɗa mata kalaman da idan ta ji su take ganin ta kai Mace, ta kai Mace cikakkiya ba wacce ta rako Mata ba, a kullum ganin kanta take yi a bata kai matsayin ba, ita bata kai Macen da zata iya fitowa ayi gwagwarmaya da ita a matsayin ta na ɗiya Mace ba. Shin wane ne shi wannan ɗin? Tabbas Ƙaddara kowa da irin tasa, wasu tana zuwar musu da sauƙi wasu kuwa akasin hakan, ba wai don wani ya fi wani bane a wurin Allah hakan ke faruwa, a'a, sai dai don Allah na gwada ko wanne bawa ta hanyar ɗaura masa tashi ƙaddaran, walau me sauƙi ko akasin sa, ko wanne bawa da tashi ƙaddaran kuma kowa yana fatan ace ya tsallake ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa. Haka itama NAANA AMINATU tayi fafutuka a cikin rayuwar ta domin ta ga ta cinye nata ƙaddaran da ta kasance babba a gare ta. Na san Kuna so ku bibiyi labarin ta domin ku ji mene ne ya faru a rayuwar ta, to ku bi Ni sannu a hankali Zan warware muku komi a cikin sauƙi, ina fata labarin zai zame muku darasi a cikin rayuwa.
IMTIHAL (COMPLETED) . by Nafeesat_Anka1
Nafeesat_Anka1
  • WpView
    Reads 153,222
  • WpVote
    Votes 8,272
  • WpPart
    Parts 40
Labarin wata yarinya ne data had'u da jarabawan rayuwa, soyayya me had'e da sarkakiya, da tarin rikici, kada Ku bari a baku labari 💖😍
Sarkakiya by Bintabusaddiq
Bintabusaddiq
  • WpView
    Reads 75,449
  • WpVote
    Votes 2,141
  • WpPart
    Parts 111
Labarin tsantsar soyayya me cike da sarkakiya ce ta kullu a tsakanin su. Ummulkhair ta zamo Allura cikin ruwa wanda me rabo ne ze dauka. Shin wa zata zaba a cikin su? Boyayyen masoyi Abdulkareem wanda yayi dakon soyayyar ta na tsahon lokaci ko kuma mahaukacin masoyi umar da yake son yi mata fin karfi?
Khadeejarh ❤️❤️ by khadijamuktar55559
khadijamuktar55559
  • WpView
    Reads 157,536
  • WpVote
    Votes 6,679
  • WpPart
    Parts 53
Fam,love,romance,money& possessiveness ❤️❤️ Hausa novel Hausa novel Ku biyo ni ku sha lbr ❤️❤️❤️
KUNDIN QADDARATA by huguma
huguma
  • WpView
    Reads 1,592,104
  • WpVote
    Votes 121,186
  • WpPart
    Parts 112
Kalmar QADDARA kalma ce dake rataye bisa wuyan kowanne bawa,haka rayuwa ta gada,tafe take da QADDARORI kala kala,masu zaqi da akasin haka............. SUMAYYA na kallon yadda KUNDIN QADDARARTA ke ta bude mata shafi bayan shafi na TATA QADDARAR kowanne shafi kuma da irin nasa salon karatun da yake biya mata..... Shin wai sai ko yaushe KUNDIN ZAI QARE? sai yaushe zata kammala bitar QADDARORINTA? Kuyi nitso da linqaya cikin labarin don samun amsoshin kalolin qaddarar tata da kuma ranar yankewarsu 'Yar mutan HUGUMA kuma UWA GA MUHAMMADIYYA ke riqe da alqalamin jagorancin labarin..........
HAIHUWA DA HANJI  by Gureenjo6763
Gureenjo6763
  • WpView
    Reads 57,891
  • WpVote
    Votes 1,502
  • WpPart
    Parts 60
TIME... LOKACI. Lokaci kamar Unit ne da ke barin shaidar wanzuwar abu walau kyakyawa ko mummuna sai dai shin yaushe zai wuce? Ta yaya zai shuɗe? Me ya ke tafe da shi? Allah ne kaɗai masani.. Kaman yadda ƊIGON RUWA kan bushe cikin lokaci ƙanƙani haka na ɗauki jarrabawa ta da ke maƙale bisa zaren ƙaddarar rayuwata... Sai dai kash tawa ɗigon ruwan duk yadda zan fifitata ta gagara bushewa. Na zaɓi zama tamkar tuwon hatsi don juriya sai kuma ya kasance ba komai ne tuwon hatsin ka iya jura ba. Matsi, takura da tsananin rayuwa sun sa na yanke yin mai ɗungurungun wai haihuwa da hanji wurin ɗaukar raina da hannuna saboda ban ɗanɗani wani garɗi ko zaƙi na wannan duniya ba!
Rubutacciyar Ƙaddara by ayshajb
ayshajb
  • WpView
    Reads 154,133
  • WpVote
    Votes 791
  • WpPart
    Parts 24
Rashin kula da bamu samu daga iyayenmu ba , shi ya taka muhimmiyar rawa gurin gurbata Rayuwar mu. musammanma ni dana taso a hannun Matar Uba, da'ace na samu kula a gurin Ubana wlh da ban d'auki dala ba gammu ba, Banshiga rayuwar kawayena dan na gurb'ata su ba!, hasali ma su suka bibiye ni ganin yanda nake fantamawa yasasu Kwad'ayin Rayuwar da nake ,duk da iyayensu , sun raba Amintar dake tsakanin mu Nayi kokarin barinsu sai dai Shakuwa tun na yarinta ya kasa bari muyi nesa da Juna, duk da na guje musu bisa i'rin gurbatacciyarr rayuwar da nake amma Haka sukayi fatali da shawarata. bakai kake zabarwa kanka Kaddara ba, Haka zalika bakai kake zanawa kanka, Rayuwar da zakayi ba, Kaddara i'ta ke zab'arka rayuwa kuwa i'ta ke juyaka yanda taso, Amma Allah na dubi da Halinka ne. tabbas rayuwar mu Rubutacciyar Kaddara ce , abin dubawane Dan Allah ku d'auki darasin cikin labarin akwai fad'akarwa sosai a cikinsa...
MATANA ✓ by AutarMama56
AutarMama56
  • WpView
    Reads 48,002
  • WpVote
    Votes 2,594
  • WpPart
    Parts 53
Matar shige da zabinsa.. Read and find out 💃🥰