We've updated our Content Guidelines.
Review the latest guidelines to keep sharing stories safely.
bintusadeeq's Reading List
3 stories
Auren dangi ✔️ by Her__majesty__001
Her__majesty__001
  • WpView
    Reads 9,069
  • WpVote
    Votes 129
  • WpPart
    Parts 27
Kubiyoni muje
TSINTACCIYA by nimcyluv
nimcyluv
  • WpView
    Reads 26,151
  • WpVote
    Votes 340
  • WpPart
    Parts 16
Rayuwa mai ɗauke da ƙunci da kuma tarin baƙin ciki, Yayinda hasken wata ke fitowa yana haskaka samaniya, a lokacin ne kuma zuciya keyin zafi da wani irin tafarfasa, Idaniya sun makance dalilin zubar Hawayen da ban san yaushe ne zai tsaya ba, Ina jin inama zan iya kashe kai na! Ko hakan zai sanya zuciyata ta samu nutsuwa da kuma salama, a lokacin da kowa ya kamata yayi farin ciki a lokacin na kejin duniya nayi min zafi, Idaniyan zuciyata na tafarfasa, ban sani ko zan zama dai-dai kamar kowa? Ban san yaushe rayuwa zata juya min daga juyin wainar fulawan da take dani ba, rayuwata ita ake kira da GABA GAƊI rayuwa mara ƴan ci, ko wacce mace na amsa sunanta dana mahaifinta yayinda ya kasance ni kuma ina amsa sunana kana na bashi makari da TSINTACCIYA!
AL'AJABIN SO by Gureenjo6763
Gureenjo6763
  • WpView
    Reads 13,322
  • WpVote
    Votes 84
  • WpPart
    Parts 26
Tarihi yana nuna mana abubuwan da suka faru ne kafin mu a rayuwa! Rayuwar duniyar cike take da kalubale, haɗari, wahalhalu da musibu daban-daban, kusan in ka ga ka gujewa hakan to fa alƙalamin ƙaddara bata zana maka ita a shafin ƙaddararka ba, a lokacin da kaddara ke wasa da rayuwarka ya rage maka ɗaukan wannan kalubale a matsayin darasi, ka kuma yi haƙuri da jarabawar Allah (S.W.T) a gare ka. Ni Fatima ban taɓa sanin cewa igiyar ƙaddarar wani na iya shafan na wani har su sarƙe wurin zama abu guda ba sai da na tsinci kaina cikin alkaba'in rayuwa, zafi da kunci suka yawaita a gareni, farin ciki yayi min nisa irin tazarar dake tsakanin sama da ƙasa, na kasa tantance wai ƙaddarar wanene ya shafe ni, shin na mahaifiyata ne ko na mahaifina? Ko kuma nawa ne ni a karan kaina ba'a tsaga ni cikin masu rabauta da duniya ba? A mafi yawancin lokuta in har nayi irin wannan tunani, na kan samu kaina ne da yiwa gwanin halitta godiya da bai sa mana wani tabbataccen al'amari ba, farin ciki ko baƙin ciki yana da lokaci, komai kuma yayi farko to fa yana da karshe, wani karin maganar ma sai ya ce abinda ya baka tsoro a yau babu shakka ko tantama a gobe ya iya baka tausayi, rayuwar tamkar tafiyar hawainiya ce tana tafe tana chanza launi. Al'amuran da suka faru a rayuwata sun sanya min karsashin bayar da labarina.