BAKAR WASIKA
KhadeejaCandy
- Reads 24,081
- Votes 1,090
- Parts 11
BAƘAR WASIƘA...
Mai farin rubutu
Ban ce tafiyar mai sauki ba ce.
Ban muku alkawarin zallar soyayya ba.
Ban ce babu farincikin ba.
Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki.
Labarin Talba, Rafi'a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal da kuma Aminatu. Labarin BAKAR WASIKA, labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta...
Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira!
A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi.
Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke?
Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa?
BAKAR WASIKA...
JUANURY 2022