diyanah03's Reading List
200 stories
ABOKIN RAYUWA  by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 45,381
  • WpVote
    Votes 1,288
  • WpPart
    Parts 76
A iyakar sani, kasuwanci ake wa siye da siyarwa. To ita wannan kaddara ta yi safararta tun daga Nijeriya har kasar Sudan, a can ta cike gurbin wata rayuwar da aka rasa ne, a wata masarautar mai ban tsoro, da ba a daga ido a kalli Sarki da mukarrabansa... Sai dai zaren be yi tsayi ba yanke, alkalamin da ya zana mata tafiya can, ya sake rubuta mata dawowa mahaifarta, ya cika mata wani sabon shafi mai cike da tsarkakiya har ta kasa zaba tsakanin rayuwarta da addinai guda biyu, wato Musulunci da kuma Christianity. Sunanta "Emily" Sunan yarta "Fadima" Sunan ɗanta "London" Shim hakan be baku mamaki ba? Ta rasa gata, ta samu gata, sai kuma ta sake rasawa kamin ta samu dawwamammen yancin daga ABOKIN RAYUWA "You belong to me!" Said VITO (The Mafia Man). "We are meant to be!" Said HAMZA ALI (Her Ex-husband). "I will search the world to find you, EMILY. You must live close to me, in our kingdom!" Said TURHAN MOHAMED ABDO (The Prince of Sudan). "You're mine, I am your soulmate!" Said ALIYU MUDALLAB (Her Boss). "The past can't touch you anymore. You're with me now and I won't let fear near you again." Said by Dr A-B (Her Doctor) Who among them is the best match? Who truly deserves her? Find out in **ABOKIN RAYUWA**. It's a hate story built on love, a sad story, and a heartbreaking tale.
SAMU DA RASHI...! by HauwaAUsmanjiddarh
HauwaAUsmanjiddarh
  • WpView
    Reads 306
  • WpVote
    Votes 14
  • WpPart
    Parts 1
A kan ce ana iya sabawa da komai, akance yau da gobe bata bar komai ba, shin ana iya sabawa da bak'ar k'addara? Kowacce dak'ik'a data harba a agogo tana harbawa ne da rubutun wata k'addara a rayuwarmu, k'addarar da zata iya zama shafi cikin littafin rayuwarmu, Lokaci baya jira, duk dakikar da ta wuce ba zata dawo ba, a lokaci daya kuma wucewar wannan dakikar dai-dai yake da budewar sabon shafi a littafin kaddarar da ba mu da tabbas akan abinda ta tanadar mana. Sai dai muyi addu'a, babu abinda yake canza kaddara
SANYI DA ZAFI by MSHAKURworld
MSHAKURworld
  • WpView
    Reads 39,679
  • WpVote
    Votes 921
  • WpPart
    Parts 30
Picture rayuwa kinada mahaifiya me HIV, the stigma, the takura from your community, and he daily battle then amidst this chaos something happened Soyayya!! But what do you think happens when FIRE meet ICE?? Idan SANYI DA ZAFI suka hadu aganin ku mezai faru???💫
JALILAH by AyusherMuhd
AyusherMuhd
  • WpView
    Reads 1,173,189
  • WpVote
    Votes 103,708
  • WpPart
    Parts 84
A painful love story.......... Duk yanda taso bacci ya dauketa ta kasa, juyi kawai take akan yar katifarta, ina zata sa kanta? Ya zatai da rayuwarta? Ina zata sa kanta? Me ya cancanta tai? Me zata zaba tsakanin burin zuciyarta da lafiyar Mahaifiyarta? Wasu zafaffan hawayene suka zubo mata......... Ku biyoni dan jin rayuwar Jalila a tsakiyar so da ceton Mahaifiyarta,
ƘALUBALEN RAYUWA  by Feedohm
Feedohm
  • WpView
    Reads 1,125
  • WpVote
    Votes 31
  • WpPart
    Parts 2
Wane irin miji ne? Mijin da bai san ya sauke haƙƙin da ya rataya a wuyan shi ba? Shin ko an faɗa mashi ci, sha da sutura kaɗai ne aure? Wallahi ba zan iya ba, ba zan iya zama da namiji mai mazantakar ƙananan yara ba! Namijin da mazantakar sa ba iya kawar da budurci na ba.... Ba zan iya ba Maama, na gwammace na koma Ƴar rawata! Na gwammace Yaya Ali na dj ina mashi rawa mu samu abinda zamu ci, rawa na ci da ni, tana shayar da ni, sannan ta na suturtar da ni, wannan abun da kike kira rashin kunya shi na ke buƙata, wannan abun da ya kasa tsayar da ke gare mu, wannan abun da kika zaɓa fiye da ƴaƴan ki......
MATAN?? KO MAZAN??? by MSHAKURworld
MSHAKURworld
  • WpView
    Reads 87,112
  • WpVote
    Votes 2,534
  • WpPart
    Parts 45
Labarine kan matsalolin da ake samu agidajen aure daga bangaren Matan dakuma Mazan. Series ne dazan dinga kawo muku duk ranan ASABAR DA LAHADI
SIRRIN MU by nimcyluv
nimcyluv
  • WpView
    Reads 11,866
  • WpVote
    Votes 286
  • WpPart
    Parts 12
_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin littafi ce,baka sanin abinda yake bangwan baya dole saika buɗe shafin gaba,muna zuwa Duniya ne ba tare da sanin abinda ke cikinta ba,wasu na zuwa a makance, wasu a kurmance,wasu kuma babu ido,kunan jin magana,uwa uba wasu basa zuwa da ƙafar takawa_ _Nakasa bata taɓa zama kasawa,haka kuma ƙaddarar data mai dashi nakashasshen zata iya sauya, kullum cikin zullumi yake, shin tayaya ne rayuwa zata kasance masa? tayaya yana nakashasshen zai iya mulkan dubban jama'a? Cikin ana tsangwamarsa bare ace ya zama shugaba,yaya jama'ar gari zasu ɗauke sa?tayaya zai gabatar da mulkin bayan Allah ya taushe ta hanyarsa rasa wani ɓangare na jikinsa?_ _Zuciya nada abubuwan ban mamaki,abinda kake so ita bashi take so ba,kullum yana ganin abin kamar mafarki amma yadda abin ke zamar masa a gaske shike masa mamaki,me zaiyi wanda zai samu farin ciki?me zaifi wanda zuciyarsa zata daina kewa ta daina ƙunci,duhun dake cikinta haske ya mamaye shi, FARAUTA shine abinda zuciyarsa ta yanke masa,abin mamaki shine tayaya nakashasshe zai iya zama mafarauci? Tayaya farauta zata masa maganin damuwarsa?.._ '''SHIN ZAI IYA KO A'A? YANA CIN RIBA A FARAUTAR KO A'A? KUNA TUNANIN WATA RANA NAKASAR SA ZATA IYA ZAMA RIBA GARESA?
Bakuwar Fuska by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 41,341
  • WpVote
    Votes 3,868
  • WpPart
    Parts 50
"Babu wata mace da nake son kasancewa da ita bayan ke Boobah. Babu macen da zan iya rayuwar aure koma-bayanki. Ki amince ki share mini hawayena, na yi alkawarin share miki naki hawayen, na baya, na yanzu, da kuma na gaba wanda ba na ma fatansu, zan kokarta yaki da su ta yadda za su nisance ki, ke da hawaye sai dai na farin ciki, da izinin Ubangijin al'arshi mai girma." Cewar Ishraq Sulaiman, hannunshi dafe da zuciyarshi da ke bugawa da sauri.
WATA DUNIYA! by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 4,600
  • WpVote
    Votes 334
  • WpPart
    Parts 15
"Ina son ka Amaan. Na dauki alkawarin ci gaba da kula da kai duk rintsi duk wuya. Zan ba ka gata, zan kaunace ka fiye da yadda nake kaunar kaina, sai dai...!" Numfashi ta ja tana furzar da iska daga bakinta, "Sai dai a boye zan so ka, ba na so kowa ya san da zaman ka, kar ka rinka fitowa a kalle min kai, ina gudun kada idanuwa su yawata a kanka, bak'in idon da tsoro da kokarin ture abin da bai zama jinsi a gare shi ba. Ba na son abin da zai karce kyakkywan jikinka, balle ya had'a da zama silar kashe min kai!" Aafiyah 'yar shekara shida zuwa bakwai a duniya ke magana da wani matsakaicin bak'in kumurci, mai jajayen idanuwa, fatar jikinshi kalar k'asa. Macijin sai fasa kai yake, yana fitar da harshensa da mayar da shi, launin idanuwansa sun sauya zuwa jajaye, yana yi yana kad'a kanshi. Shin a wace duniya ce muke? Ina ne za ta kai mu? Ta yaya aka yi yarinya k'arama ke magana da maciji ba tare da tsoro ba? Tabbas kowa ka gani a duniya akwai dalilin wanzuwarsa akwai kuma manufar alakantuwa da zama sila na bayyanarsa. Sai dai silar da ke cikin tafiya WATA DUNIYAR kan iya shafe labaran da aka shekara sittin ana rubuta shi. Ku shigo ciki a yi tare da ku...kar ku bari labarin WATA DUNIYA ya wuce ku.
HAKKIN UWA by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 5,092
  • WpVote
    Votes 294
  • WpPart
    Parts 13
Wannan labari ne mai tsananin ban tausayi da taba zuciya wanda kuma ya faru da gaske sai dai 'yan gyare-gyare wadanda ba za a rasa ba. Shin kun san girman hakki kuwa? Kun san girma da darajar da uwa take da shi? Kun san babbar tabewa ce ga mai murje darajar uwa? Kun san cewa hakkinta ba zai bar mutum ba? Ku biyo ni don ganin salon wannan labarin.