MaryamMohdGoni's Reading List
11 stories
Dangantakar Zuciya by huguma
huguma
  • WpView
    Reads 328,115
  • WpVote
    Votes 22,277
  • WpPart
    Parts 46
A heart touching story
BABU WAIWAYE by 68Billygaladanchi
68Billygaladanchi
  • WpView
    Reads 73,007
  • WpVote
    Votes 4,644
  • WpPart
    Parts 24
Bugun zuciyar tane ya qaru, ganin shigowar Al'ameen gidan, ktchen take qoqarin shigewa sanda ya qaraso gabanta ya murtuqe fuska hade da ce bayan ya qura mata manyan idansa "Ina sanin meye asalinki? Wacece ke? Wannan aikin dakike beyi kamada jikinki ba sam, alamomin ki da komai be sanar dani cewar daga wani mugun gida kika fito ba meya kawoki london? Tayaya ma kikazo? Dayaya kika soma wannan makarantar me tsada? Mesa kika saka kaya masu tsada kuma kina aikatau?" Hawayene ya dararo mata amma batayi magana cikin bacin rai yace "Wani karuwanki ne ya biya miki da kuka rabu yace baze kuma biya ba?" Da sauri ta dago ta kalkeshi ido cikin ido tana ci gaba da zubar kwalla,yaci gaba "Idan ba haka ba sanar dani dalilinki na zuwa london da kuma ya akayi kika zo? Kuma waye iyayenki inane garinku a niger? Sosai ta masa kallon na gaji da tsayuwa shida kanshi ya sani koda ze shekara magana bawai tankashi zata yiba,da saurinta kuwa ta juya zuwa ktchn aikam wani hankad'ota yayi seda ta buga goshi!!!!
BAKIN DARE by Sadnaf
Sadnaf
  • WpView
    Reads 63,007
  • WpVote
    Votes 4,272
  • WpPart
    Parts 21
heart touching story
KE NAKE SO by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 182,977
  • WpVote
    Votes 12,533
  • WpPart
    Parts 19
#1 sacrifice 21/08/2020 #5 in romance 27/09/2016 "Malam, ka yi kuskure, idan ka na tunanin zaka canza min ra'ayina a minti biyar". "Ko za ki gwada ki gani?" Ya tambaya, yana murmushi, ita ta rasa ma yadda aka yi ya iya murmushi, da dai ba ta ganin hakan a tare da shi. Ta kan dauka shi haka Allah ya halitto shi, duk lokacin da ta samu ganinsa a rayuwarta, sau daya ta taba ganin murmushinsa, ko ba da ita ba, idan tana wurin, baya yin murmushi da kowa. Ta danne zuciyarta, sannan ta zauna, don ita ko ganinsa ma ba ta son yi, bayan abin da ya yi jiya. "Tambaya na ke son na miki. Shin Alhaji Yusuf da ki ke son ki aura, kin tabbata ya damu da farin cikin ki, ko kuwa bacin ranki?" "Wace irin tambaya ce wannan?" Kallonta yake yi kamar zai hadiyeta "Ki amsa min, me ya sani game dake?" Kafin ta ba shi amsa ya ci-gaba. "Shin ya san cewa ba ki son turare mai karfi, saboda ki na da Allergy, ko kuwa ya san idan kin sha ruwan sanyi ciwon Agalawarki na tashi? Ko kuwa kin fi son kasancewa cikin mutane ki yi walwala. Ya san da cewa ba ki amfani da Salary dinki, sai dai ki yi hidima wa wadanda ki ke so?" Ya numfasa cikin murya kasa-kasa ya-ce. "Ya san cewa ba kya son shi?" This is the limit. Ya kai ta makura. "Yaya aka yi ka san duk wannnn a tare da ni?" "Saboda Jidda, na sanki. Na san komai game dake every. Little. Detail. na sani". Ya fada cikin wani yanayi mai tsinka jiyoyin jikin mai saurare. "Well, abinda ba ka sani ba, shi ne ka bata kan batun Alhaji Yusuf, domin kuwa SHI NA KE SO!
Gidan Bature by Ummusubaya
Ummusubaya
  • WpView
    Reads 69,732
  • WpVote
    Votes 3,361
  • WpPart
    Parts 10
Romantic Love story&Family Saga
Boyayyar soyayya by afreey101
afreey101
  • WpView
    Reads 267,661
  • WpVote
    Votes 16,672
  • WpPart
    Parts 42
hausa language story meaning SECRET LOVE "love at first sight" this story is about a low class girl who fall in love with a wealthy handsome youth service copper. labarin SIDDIQA da ADYAN. coming soon inshaAllah 20votes and I will continue updating.........
AMAREN BANA by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 143,684
  • WpVote
    Votes 9,321
  • WpPart
    Parts 17
#9 in romance on 05/09/2016 "Wai ina son ki fada min, me yake damun ki ne, da za ki haddasa irin wannan fitina, sannan ki zauna lafiya, kamar ba abinda ya faru?" Dubansa ta yi a sanyaye, sannan ta-ce. "Ina da dalilina." "Wane irin dalili ne, zai sa ki na ji, ki na gani auren iyayenki ya mutu? Idan banda irin gurguwar tunani irin naki? Ashe ki na da halin yin gyara a wannan al'amari, ba za ki yi ba?" Mikewa ya yi daga kan kujerar zai tafi, da sauri ta kamo bakin rigarsa, ya tsaya, ganin zai saurareta, ya sa ta sakar masa riga. "An fada maka ni ma ina jin dadin ganinsu da na ke yi a haka ne? Sam, ba son raina bane, amma na daure na kauda kaina, saboda mu kawar da gagarumar matsalar da ta fi wannan. Na san halin Momi, tana da fada, tana da rashin son gaskiya, amma kuma haka tana da saurin nadama, na san za ta nemi afuwa, kuma Abba zai saurareta. Sai dai wannan tafiyar, dole ka taimaka ka ba ni goyon baya, don mu shawo kan al'amarin nan tare." Kallonta ya yi, ita ma duk ta jikkata, ta jejjeme ta zama wata iri, tabbas yadda take ji haka yake ji, koma fiye, don bayan baya sonta, ya tsani uwarta, sannan yana mutuwar son Meena. "Ki yi hakuri, amma ba zan iya aurenki ba." Ranta ya baci kwarai, har ya juya zai fita ta-ce. "Saboda me ya sa ba za ka iya aure na ba? Saboda me ya sa ban kai matsayin na zamo matarka ba?" "Ki fada min, ta yaya zan iya zama dake, alhali ki na matsayin 'yar matar da na tashi da tsanarta a zuciyata?" "Wane irin dalili zai sa maka tsanar mahaifiyata, har da zai sa ni ba za ka iya aurena ba?" Shiru ta yi don ta ji dalilin wannan tsanar.
BAN SAN SHI BA PART 1. Part 2 Of The Book Is On Okadabooks.com  by Deejahabdul
Deejahabdul
  • WpView
    Reads 132,562
  • WpVote
    Votes 4,799
  • WpPart
    Parts 37
Part 2 of the book is on okadabooks.com #1 in Mystery/Thriller 5 February,2017 #2 in Mystery/Thriller 24 july,2017 NO JUMPING, NO TRANSLATING THIS BOOK INTO ANY LANGUAGE, NO COPYING AND SHARING MY STORY. ANY SORT OF PLAGIARISM IS NOT ALLOWED ON MY STORY. DOING SO WILL LEAD TO THE BANNING OF THE STORY FROM WATTPAD COMPLETELY. HOPE ZA'A KIYAYE. BANYARDA A KWASHE KO A JUYAMIN LABARI TA KOWACCE HANYA BA. BANYARDA AMIN SHARING LABARI A KO'INA BA. YIN HAKAN ZAISA NA TSAYARDA LABARIN KUMA NA CIRESHI GABAD'AYA DAGA WATTPAD. HOPE ZA'A KIYAYE.
Sila by Khairat_
Khairat_
  • WpView
    Reads 42,150
  • WpVote
    Votes 1,693
  • WpPart
    Parts 36
Amma kin san akwai karatu ko ko kyalkyalen banza kike so Ni de aa wallahi bazan iya ba Ta mike Ya biyo ta *DEAR* ta juyo yaya na gaji tafiya xan yi. Ki xauna anjima kadan zan yi lec in nayi sallah se mu tafi tare Yaya da mota nazo Ni yau da napep nazo Kai yaya ina motar taka? Tana gun gyara mashin din kuma abulkhair ya amsa zaiyi amfani dashi. Ku jirani se mu tafi tare Aa Kawarta ta ce aa *DEAR* mu jira yayan mana me a ciki in mun yi sallar ma tafi.
UMM ADIYYA (Read Full Book On okada) by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 109,676
  • WpVote
    Votes 2,946
  • WpPart
    Parts 7
#6 in Romance 14/04/2017 Tunda take bata taba ganin mugun mutum marar kunya irin Zaid Abdurrahman ba. Ta so ta juya amma ganin su Maami yasa ta fasa ta shigo falon ta gaishe su sama-sama don tare suke da yayanta Saadiq. Har ma yana tambayarta "Ummu A. da fatan dai wadannan basu baki wahala a wurin aikin?" Murmushi tayi har sai da kumatunta ya loba sannan tace "Mutanen da suka bini har da roko saboda na musu aiki ba sau daya ba ba sau biyu ba, ai kaga bazasuyi garajen bani wahala ba, don haka ina aikina cikin kwanciyar hankali with full amenities. Ko ba haka ba?" Ta fada cikin dai murmushinta hade da harde hannayenta saman kirjinta. Idanunsa ya zuba mata tamkar mai karantar duk wani motsi da ruhinta yakeyi, "Saadiq, dole mu kula da Adiyya, saboda ko ba komai ta san yanda take amfani da kwakwalwarta, she's very smart." Ya kare maganarsa cikin murmushi. Tsumewa tayi hade da aika masa kallon banza, "Dole kace kuna kula da Adiyya, banda dan karan wuyar da kuke bani me kuke yi? kullum nayi aiki sai an kwakulo kuskure a ciki, ko me ya kaishi daukana aikin ma tun farko oho." Barin falon tayi zuwa kicin inda tayi zamanta a can taci abincinta. Bata sake bi ta kan falon ba bare ta san lokacin tafiyarsa. Tana kwance kan gado sai aikin sake-sake takeyi abu daya ke yawo a kwakwalwarta, kuma hanya dayace da zata bi don magance wannan damuwar- itace ta bar aiki a AZ IT consultants. A karo na uku! Ko su kadai suke daukan ma'aikatan da suka karanta fagenta ta yafe wannan aikin da irin ukubar da take shiga kullum wayewar gari, "To ma wai aikin dole ne?" Ummu Adiyya ta tambayi kanta, ba tare da sanin dalili ba ta samu kanta tana tsiyayar hawaye. "Duk harda laifin Abba ma yaya za ayi bayan na fada masa komai kuma yace na ci gaba da aiki dasu?" ******