mimiswit's Reading List
4 histoires
TAFIYAR DARE ( MAYYUN JINI ) par abdulkingarticle
TAFIYAR DARE ( MAYYUN JINI )
abdulkingarticle
  • LECTURES 3,757
  • Votes 132
  • Parties 3
A duk lokacin da tafiyar dare ta kamaka, bako shakka kana cikin barazanar haduwa da mayyun dare......
JARRABAR RAYUWA COMPLETE✅ par SaNaz_deeyah
JARRABAR RAYUWA COMPLETE✅
SaNaz_deeyah
  • LECTURES 38,768
  • Votes 2,293
  • Parties 54
Sai daya gama lalata ƙanwarta sannan ya dawo da niyyar aurenta Shin zata amince ta aure shi,bayan ya san ƙanwarta a ƴa mace?. Labarin Sadiya budurwa mai ɗauke da cutar Sickler,wadda cutar ta haddasa mata jarabobi,ta kasa samun tsayayyen masoyi,tasha baƙar wahala da ita da ƙanwarta Afreen,kuma Allah ya ɗauki rayuwarsu ba tare da sunji wani daɗi na rayuwa ba,sai kuma wasu matasa guda biyu wanda suka faɗa wahalalliyar soyayya,littafin jarrabar rayuwa salo ne mai tafiya da zamanin nan namu...........ku shiga cikin labarin dan jin komai,labari ne mai taɓa zuciya.
TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata... par 68Billygaladanchi
TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...
68Billygaladanchi
  • LECTURES 175,773
  • Votes 15,180
  • Parties 52
"Mesa kake ambatar mutuwar nan wai, idan akan nace banasan kane kayi hakuri ina sonka wlhy, fiye ma da tunanin ka, na Amince zan rayu dakai rayuwa ta amana daso dakuma k'auna" ka tallafi rayuwata kadena fad'ar hakan kaji" Cikin azabar ta ciwon dayake ciki ya saki wani murmushi dayake nuna tsantsan jin dad'in da kalaman ta suka saka shi ya ce..."Naso ace kin furta mun wannan kalman tuni amma ko yanzu naji dad'i sosai, dad'in dana tabbatar dashi zan mutu a raina, My meenal zo matso kusa dani kinji?" da sauri ta k'arisa kusa dashi da rik'o hannun shi tace "kaga yanda kake numfashi ko yaa muhammad? ka daure ka dena magana kafin likitan yazo, save ur strenght plss" K'walla ya gangaro masa da k'yar ya iya furta "Wanda yake bayarda ikon numfashin ya buk'aci abinsa my meenal, lokacin tafiyane yazo tafiyan daba fashi, dukkanin abinda ya faru tsakanina dake na yafe miki matsayina na mijinki ina mikin fatan aljannar firdaus mad'auka kiya, ki sani inajin tsoro wlhy, tsoro nakeji my meenal" kuka ya k'wace mata sosai ta sanya kukan kuwa "Mesa kakemun maganganu a baud'e, wlhy ina fahimtar komai yanzu, hausarka tangaran nake fahimta mutuwa kake nufi zakayi bana fata kuma, kayi shiru kaji" Hannunsa d'aya ya mik'o mata wani takarda ta karb'a ya k'ara had'e hannun shi da nata da takardan, yace yana numfarfashi da k'yar "Ki bi abinda na rubuta a takardan nan, ki karantashi cikin nutsuwa kinji" batace komai ba daga ita har k'aninsa dake nan kusa da ita se gani sukayi yayi shiru bakinsa yana motsi amma basajin meyake cewa numfarfashi kurun yake sama sama, daganan sekuma yae shiru komai ya tsaya cak rai yayi halinsa!!!!!!!
WANI GIDA...! par jeeedorhh
WANI GIDA...!
jeeedorhh
  • LECTURES 128,618
  • Votes 12,202
  • Parties 31
Tana shiga cikin dakin, taji an janyo hannunta anyi gefe da ita. Cikin tsananin tsoro da bugun zuciya ta daga baki zata saki ihu, taji an sanya hannu an rufe mata baki, a lokaci guda kuma aka juyata tana kallon wanda yayi mata wannan aika-aika. Ta saki wani numfashi da bata san lokacin data rike shi ba, ta jefa mishi harara cikin wasa. Duk da cewa manyan fararen idanunta babu abinda suke fitarwa sai tsananin kauna mai tsafta. Ya kasheta da murmushin nan nashi da har kullum yake kashe mata jiki, ya kanne mata idanu, "Hello, love!". * Wai bahaushe yace 'hali zanen dutse!', 'mai hali baya canza halinsa!'. Bahijjatu tayi tunanin wadannan duk fada ce kawai, sai da ta kwashe watanni shida bata cikin gidansu ta koma, ta ga babu abinda ya canza zani daga tsarin rayuwar gidan. Wata irin rayuwa ce ake yi a cikin gidansu mai matukar daure kai. Rayuwar da babu girmama na gaba, babu bautar Allah, babu kuma tsoron Allah a cikinta. Bata san cewa rayuwarta na shirin yin juyi wanda bata taba zata ko tsammani a wannan dawowar ba. Ku biyo matashiya Bahijjatu domin jin ta yadda zata karbi wannan canji da yazo mata babu zato balle tsammani, ba kuma tare da ta shirya ba. Wannan littafi kyauta ne, wanda zai dinga zo muku a duk lokacin da damar yin typing ta samu... :)