lee_marh's Reading List
62 stories
A ZATO NA...!  by jeeedorhh
jeeedorhh
  • WpView
    Reads 10,399
  • WpVote
    Votes 255
  • WpPart
    Parts 5
Kallon Umar nayi ina murmushi, "handsome, bari mu wuce ko?". Ya gyada kai, "Ok Sweety, zamu yi waya ko?". Na jinjina kai, "in shaa Allah. See you!". Har ya juya ya tafi, sai kuma ya juyo da sauri, "hey, bari in miko miki fruits". Na daga baki da niyar cewa na gode, Yaya Bilal ya katse ni ta hanyar yiwa motar key. Ya kalli Umar, "ta gode, sauri muke". Da wannan yaja motar. Ina hango Umar ta cikin gilashi yana daga kafada. Munje main gate, na juya na kalleshi, nace "Yaya ko zaka ajiye ni anan kawai, sai in karasa ciki?". Yadda kasan bango, haka ya maida ni, ko kallon inda nake bai yi ba. Bai ma nuna alamun yaji abinda nace ba, sai ma ya karawa motar wuta ya shige cikin makarantar. A bakin hostel ya samu waje yayi parking din motar, na fara yunkurin bude kofar ina jera mishi godiya, "na gode Yaya, a gaida Anty Ameerah". Sai da na fita, ina kokarin maida kofar in rufe, naga yana miko min leda mai dauke da tambarin Bitmas, na kalleshi fuskata dauke da alamun tambaya, kafin inyi magana ya riga ni, "karbi mana, kina bata min lokaci!". Nasa hannu biyu na karba, nace "nagode, Allah Ya amfana". Yace "Ameen" a kaikaice, yawa motarshi wuta ya kara gaba. Ni kuma na shige cikin hostel. ~Wannan littafi tsakure ne kawai. Zaku iya samun cigaban shi a zaurenmu na WhatsApp. Ga duk masu bukatar shiga, akwai bayanan yadda zaku yi ku shiga a ciki.
KWARATA... by meelatmusa
meelatmusa
  • WpView
    Reads 807,240
  • WpVote
    Votes 33,469
  • WpPart
    Parts 112
Ƙalu bale gareku matan aure
TAKAICIN DA NAMIJI! by Khairat_
Khairat_
  • WpView
    Reads 130,958
  • WpVote
    Votes 5,955
  • WpPart
    Parts 72
the story is about a young gurl who struggles alot in her life she faces a lot of difficulties right from childhood,she had no knowladge of father's love or care nor her mother know's the happiness of being a housewife! i think you had like the story.
Hilwa. by rukayya_abdullah
rukayya_abdullah
  • WpView
    Reads 1,862,416
  • WpVote
    Votes 40,923
  • WpPart
    Parts 13
Hilwa Haroun, a spirited girl from a small town in Nigeria, relocates to the bustling city of Abuja, hoping for a fresh start and new opportunities. However, adapting to her new life proves to be a challenging journey filled with unexpected twists. As she navigates the fast-paced lifestyle and the complexities of a blended family with contrasting personalities, Hilwa struggles to find her place in a world that feels foreign. Just when she begins to settle in, a shocking revelation turns her life upside down, presenting her with a challenge she never anticipated. Faced with emotional turmoil, Hilwa must confront her fears. Will she be able to embrace the changes and accept this unexpected turn of events with an open heart, or will it push her further away from the life she longs to build? Join Hilwa on this exhilarating and poignant journey as she learns to balance love, family, and self-discovery in a city that promises both excitement and uncertainty. It's a bumpy, emotional and an exciting ride. BETWEEN TWO WORLDS. H I L W A. ~ H E L WA.
...YA FI DARE DUHU by rashkardam
rashkardam
  • WpView
    Reads 63,858
  • WpVote
    Votes 3,350
  • WpPart
    Parts 40
Labarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.
ABINDA KE B'OYE by hajjac
hajjac
  • WpView
    Reads 128,839
  • WpVote
    Votes 8,753
  • WpPart
    Parts 51
labari ne mai cike da ban al'ajabi, ban tausayi ban haushi da ban dariya, soyayya kulawa da nuna ban-bancin al'ada uwa uba.... kubiyo mu danjin ya zata kaya.
AMAREN BANA by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 143,437
  • WpVote
    Votes 9,318
  • WpPart
    Parts 17
#9 in romance on 05/09/2016 "Wai ina son ki fada min, me yake damun ki ne, da za ki haddasa irin wannan fitina, sannan ki zauna lafiya, kamar ba abinda ya faru?" Dubansa ta yi a sanyaye, sannan ta-ce. "Ina da dalilina." "Wane irin dalili ne, zai sa ki na ji, ki na gani auren iyayenki ya mutu? Idan banda irin gurguwar tunani irin naki? Ashe ki na da halin yin gyara a wannan al'amari, ba za ki yi ba?" Mikewa ya yi daga kan kujerar zai tafi, da sauri ta kamo bakin rigarsa, ya tsaya, ganin zai saurareta, ya sa ta sakar masa riga. "An fada maka ni ma ina jin dadin ganinsu da na ke yi a haka ne? Sam, ba son raina bane, amma na daure na kauda kaina, saboda mu kawar da gagarumar matsalar da ta fi wannan. Na san halin Momi, tana da fada, tana da rashin son gaskiya, amma kuma haka tana da saurin nadama, na san za ta nemi afuwa, kuma Abba zai saurareta. Sai dai wannan tafiyar, dole ka taimaka ka ba ni goyon baya, don mu shawo kan al'amarin nan tare." Kallonta ya yi, ita ma duk ta jikkata, ta jejjeme ta zama wata iri, tabbas yadda take ji haka yake ji, koma fiye, don bayan baya sonta, ya tsani uwarta, sannan yana mutuwar son Meena. "Ki yi hakuri, amma ba zan iya aurenki ba." Ranta ya baci kwarai, har ya juya zai fita ta-ce. "Saboda me ya sa ba za ka iya aure na ba? Saboda me ya sa ban kai matsayin na zamo matarka ba?" "Ki fada min, ta yaya zan iya zama dake, alhali ki na matsayin 'yar matar da na tashi da tsanarta a zuciyata?" "Wane irin dalili zai sa maka tsanar mahaifiyata, har da zai sa ni ba za ka iya aurena ba?" Shiru ta yi don ta ji dalilin wannan tsanar.
KE NAKE SO by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 182,602
  • WpVote
    Votes 12,531
  • WpPart
    Parts 19
#1 sacrifice 21/08/2020 #5 in romance 27/09/2016 "Malam, ka yi kuskure, idan ka na tunanin zaka canza min ra'ayina a minti biyar". "Ko za ki gwada ki gani?" Ya tambaya, yana murmushi, ita ta rasa ma yadda aka yi ya iya murmushi, da dai ba ta ganin hakan a tare da shi. Ta kan dauka shi haka Allah ya halitto shi, duk lokacin da ta samu ganinsa a rayuwarta, sau daya ta taba ganin murmushinsa, ko ba da ita ba, idan tana wurin, baya yin murmushi da kowa. Ta danne zuciyarta, sannan ta zauna, don ita ko ganinsa ma ba ta son yi, bayan abin da ya yi jiya. "Tambaya na ke son na miki. Shin Alhaji Yusuf da ki ke son ki aura, kin tabbata ya damu da farin cikin ki, ko kuwa bacin ranki?" "Wace irin tambaya ce wannan?" Kallonta yake yi kamar zai hadiyeta "Ki amsa min, me ya sani game dake?" Kafin ta ba shi amsa ya ci-gaba. "Shin ya san cewa ba ki son turare mai karfi, saboda ki na da Allergy, ko kuwa ya san idan kin sha ruwan sanyi ciwon Agalawarki na tashi? Ko kuwa kin fi son kasancewa cikin mutane ki yi walwala. Ya san da cewa ba ki amfani da Salary dinki, sai dai ki yi hidima wa wadanda ki ke so?" Ya numfasa cikin murya kasa-kasa ya-ce. "Ya san cewa ba kya son shi?" This is the limit. Ya kai ta makura. "Yaya aka yi ka san duk wannnn a tare da ni?" "Saboda Jidda, na sanki. Na san komai game dake every. Little. Detail. na sani". Ya fada cikin wani yanayi mai tsinka jiyoyin jikin mai saurare. "Well, abinda ba ka sani ba, shi ne ka bata kan batun Alhaji Yusuf, domin kuwa SHI NA KE SO!