ummukhairiyya's Reading List
8 stories
MAI HAKURI (shi ke da riba) oleh rahmakabir
rahmakabir
  • WpView
    Membaca 29,322
  • WpVote
    Vote 2,024
  • WpPart
    Bab 50
D'aki ne mai duhu sosai baka iya ganin tafin hannunka, lantarkin d'akin yana a kashe, Jannat cike da tashin hankali da tsoro ta isa wurin makunnin hasken d'akin da lalube, nan take ta kunna haske ya gauraye ko ina, ganin abinda ba tayi tsammani ba ta k'ara shiga tsananin tashin hankali, idonta kamar zasu yo k'asa ta dafe kanta tace "Na shiga ukuna ni Jannat" Sai ta saki wani gigitaccen k'ara. Abbanta ne kwance a tsakar d'akinta cikin jini, wanda ya malale tiles d'in d'akin, ya dafe gefen cikinsa da hannun damansa babu alaman rai a tattare dashi, wuk'ar dake hannunta ta kalla wanda duk jini ya gama b'ata shi tare da hannunta na hagu, kamar an tsikareta ta jefar da wuk'an a k'asa da k'arfi, wani ihun ta kuma saki wanda duk sai da ya tada duk Mutanen dake cikin gidan.
RAI DA KADDARA oleh LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Membaca 78,133
  • WpVote
    Vote 7,816
  • WpPart
    Bab 59
Daada, Ku saka mata Munawwara, ku kira ta da Madina. Watakila albarkacin sunayen biyu rayuwar da bata da zabi a kanta ta zo mata da sauki ko yaya ne. Zan so kaina a karo na biyu, ku fada mata mahaifiyarta ta sota a watanni taran zamanta a cikinta, ko ba zata yarda ba Daada ki fada mata ta yafe mun, ki bata hakuri na yanda zata kare sauran kwanakin ta a duniya tana biyan zunuban mahaifanta. Kuma ku fada mata sunan baban ta Kabiru, yanayin haihuwar ta ba zai canza cewa ita din jinin shi bace ko da bata da gadon shi. Ke ma ki yafe mun, kiyi mun addu'a ko da rayuwa ba zata sake hada fuskokin mu ba. Yelwa.
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) oleh MaryamahMrsAm
MaryamahMrsAm
  • WpView
    Membaca 148,532
  • WpVote
    Vote 10,256
  • WpPart
    Bab 67
Labarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.
KE NAKE SO oleh ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Membaca 183,158
  • WpVote
    Vote 12,551
  • WpPart
    Bab 19
#1 sacrifice 21/08/2020 #5 in romance 27/09/2016 "Malam, ka yi kuskure, idan ka na tunanin zaka canza min ra'ayina a minti biyar". "Ko za ki gwada ki gani?" Ya tambaya, yana murmushi, ita ta rasa ma yadda aka yi ya iya murmushi, da dai ba ta ganin hakan a tare da shi. Ta kan dauka shi haka Allah ya halitto shi, duk lokacin da ta samu ganinsa a rayuwarta, sau daya ta taba ganin murmushinsa, ko ba da ita ba, idan tana wurin, baya yin murmushi da kowa. Ta danne zuciyarta, sannan ta zauna, don ita ko ganinsa ma ba ta son yi, bayan abin da ya yi jiya. "Tambaya na ke son na miki. Shin Alhaji Yusuf da ki ke son ki aura, kin tabbata ya damu da farin cikin ki, ko kuwa bacin ranki?" "Wace irin tambaya ce wannan?" Kallonta yake yi kamar zai hadiyeta "Ki amsa min, me ya sani game dake?" Kafin ta ba shi amsa ya ci-gaba. "Shin ya san cewa ba ki son turare mai karfi, saboda ki na da Allergy, ko kuwa ya san idan kin sha ruwan sanyi ciwon Agalawarki na tashi? Ko kuwa kin fi son kasancewa cikin mutane ki yi walwala. Ya san da cewa ba ki amfani da Salary dinki, sai dai ki yi hidima wa wadanda ki ke so?" Ya numfasa cikin murya kasa-kasa ya-ce. "Ya san cewa ba kya son shi?" This is the limit. Ya kai ta makura. "Yaya aka yi ka san duk wannnn a tare da ni?" "Saboda Jidda, na sanki. Na san komai game dake every. Little. Detail. na sani". Ya fada cikin wani yanayi mai tsinka jiyoyin jikin mai saurare. "Well, abinda ba ka sani ba, shi ne ka bata kan batun Alhaji Yusuf, domin kuwa SHI NA KE SO!
GUGUWAR SO (Completed✅) oleh HafsatRano
HafsatRano
  • WpView
    Membaca 22,488
  • WpVote
    Vote 1,309
  • WpPart
    Bab 17
RAYUWAR MARYAMU oleh hsady85
hsady85
  • WpView
    Membaca 15,970
  • WpVote
    Vote 530
  • WpPart
    Bab 3
Rayuwar maryamu labarine kagegge Wanda yakunshi abun tausayi,alajabi dakuma nishadantarwa kubiyumu kusha labari!!!
...YA FI DARE DUHU oleh rashkardam
rashkardam
  • WpView
    Membaca 64,026
  • WpVote
    Vote 3,350
  • WpPart
    Bab 40
Labarin ƙauna gamida cin amana da tausayi ga uwa uba soyayya.