dijawaziri's Reading List
43 stories
MATAR BAHAUSHE por Lubbatu_Maitafsir
Lubbatu_Maitafsir
  • WpView
    LECTURAS 61,957
  • WpVote
    Votos 7,604
  • WpPart
    Partes 20
Kamar yadda rayuwar ko wace MATAR BAHAUSHE take zuwa cikin yanayi mabanbanta, haka tata rayuwar ta fara cike da tarin kalubale. Sai dai ta fannoni da dama, ta banbanta da sauran matan hausawa da suke sarewa cikar burinsu na yau da kullun. She's ambitious, very courageous, and she's determined to fulfill her dreams. MATAR BAHAUSHE... When politics become more than just a dream. Lubbatu Maitafsir
DAUƊAR GORA...!! por BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    LECTURAS 9,199
  • WpVote
    Votos 339
  • WpPart
    Partes 6
Labari mai cike da bahaguwar cakwakiya, ɗimuwa, ruɗani tare da bam mamaki. tsantsar mulki da ƙarfin ikon masu mulki. tsaftatacciyar soyayya mai cike da nagarta da dattako.
BABU SO... por BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    LECTURAS 9,013
  • WpVote
    Votos 332
  • WpPart
    Partes 6
hhhh miya kawo kishi. littafin babu so yazo muku da nasa salon na musamman shima. sunce BASU son juna. to amma mike kawo musu KISHIN juna kuma masu karatu? a waje ɗaya zamu sami wannan amsar. shine ta hanyar bibiyar littafin BABU SO MIYA KAWO KISHI ɗaya daga cikin books biyar na zafafa dake zomuku cikin kowanne salo na burgewa.
BAƘAR INUWA....!! por BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    LECTURAS 14,591
  • WpVote
    Votos 252
  • WpPart
    Partes 12
Labari mai cike da sabon salo. Cakwakiyar siyasa. Soyayya mai sanyi da tsuma zuciya. Kai idan zanta jerowa sai na baku page guda anan. Ku kasance da BAƘAR INUWA.. domin jin su wanene baƙar inuwar?, miyazo da shi? Wane salone nashi shi kuma?. Kar dai ku bari a baku labari, dan yazo da abubuwa masu yawan gaske ta kowanne fanni da mai karatune kawai zai tantance. BAƘAR INUWA... yazone a cikin littatafan ZAFAFA BIYAR ɗin nan naku masu nishaɗantar daku da faɗakar daku. Sauran books namu suma sunzo da sabon salo na musamman masu tsinka kunnen mai karatu. Masoya ku antayo kawai, san kuwa ance gani ya kori ji😋😋😉.
ZAFAFA SABON KAFCE🤓 por BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    LECTURAS 11,530
  • WpVote
    Votos 174
  • WpPart
    Partes 4
ZAFAFAN LITTTAFAI DAGA ZAFAFAN MARUTA GUDA BIYAR👌🏼
TAKUN SAAƘA!! por BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    LECTURAS 17,064
  • WpVote
    Votos 428
  • WpPart
    Partes 8
TAKUN SAƘA littafi ne da yazo muku da wani salo na musamman. tare da tsaftatacciyar salon soyayya tsakanin wasu tom and jarry😂. halinsu ya banbanta da juna. hakama burinsu da halayyarsu. Ta yaya RUWA DA WUTA zasu kasance a mazubi guda bayan kowanne yanada power ɗin gusar da ɗan uwansa. humm karna cikaku da surutu, dan gane inda na dosa sai ka nema TAKUN SAƘA dake ɗaya daga cikin ZAFAFA BIYAR zaka fahimceni. Littafine mai ƙunshe da tsananin rikita-rikita da cin amana tare da cakwakiyar sarƙaƙiya. ba'ananfa kawai ya tsayaba. akwai ilimantarwa mai amfani tare da tabbatar muku MACE MA MUTUM ce da zata iya bama ƙasa da ƴan ƙasa gudun mawa ta fannoni da dama na rayuwa bayan gidan aurenta da tarbiyyar iyalanta da addininta. kukasance a TAKUN SAƘA domin samun cikakken wannan labari da yazo da sabon salo na musamman domin ƙayatar daku masoya😉😉😍😘. ZAFAFA BIYAR naku ne, Kuma na ZAFAFA BIYAR NE😋🤗.
MAKAUNIYAR ƘADDARA!! por BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    LECTURAS 12,816
  • WpVote
    Votos 298
  • WpPart
    Partes 9
MAKAUNIYAR ƘADDARA Labari mai cike da cakwakiyar rayuwa. Ta wayi gari da ƙaddarar da batasan mafarinta ba, batasan tushenta ba. Gata da ƙarancin shekaru, gata da ƙarancin gata. Labarin zai taɓo muku zamantakewa, Soyayya, harma da nishaɗi. Bama shiba, a wannan karon duka zafafa biyar sunzo mukune da sabon salo na musamman. Karku bari ayi babuku masoyan ƙwarai abokan tagiya😍😍😍😘🤗.
SANADIN BIKIN SALLAH!! por BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    LECTURAS 15,600
  • WpVote
    Votos 1,054
  • WpPart
    Partes 7
Yanda ƴammata ke mancewa da kansu da martabarsu a yayin bikin sallah, burinsu su haska kawai wajen samari, ko ina suka zagaya a yabasu su da kwalliyarsu, ajiye al'ada da addini dan kawai ace kaine wane, bin kowacce hanya wajen neman kayan bikin sallah. matan aure masu burin gasa da wance tayi kaza a gidanta, nima dolene sai nayi koda ban kaiba, mun manta ko yatsun hannunmu ba ɗaya bane ba, baki da gashin wance kice sai kinyi kitson wance🤦🏻.
ABDUL-MALEEK (BOBO) por BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    LECTURAS 226,627
  • WpVote
    Votos 11,598
  • WpPart
    Partes 53
Labarin mai nuni da muhimmancin biyayya ga iyaye, gujema son zuciya, soyayya, zuminci, tare da cakwakiya tsakanin yaya da ƙanwa akan son abu guda.
MUTUM DA DUNIYARSA...... por BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    LECTURAS 130,118
  • WpVote
    Votos 9,459
  • WpPart
    Partes 41
Wannan labari labarine da ya taɓo rayuwar da mafi yawan mata ke fuskanta a wannan rayuwar, tare da rayuwar kishi na gidajen aurenmu, da nuna jarumtar mazan ƙwarai da ke aiki da hankali da ilimi wajen tafiyar da ragamar rayuwar aurensu. Magidanta da yawa basa son a haifa musu ƴaƴa mata, abin kuma zai baka mamaki idan zaka tarasu wajen buƙatar jin dalilinsu, musani UBANGIJI ya fimu sanin mu su wanene? miyasa yayimu jinsi-jinsi, yare daban-daban, zuri'a daban-daban. kai dai ka roƙi ALLAH ya baka mai albarka kawai shine magana.