LubnaSufyan
- Reads 2,241
- Votes 114
- Parts 1
Su uku suka kulla yarjejeniyar, sirri ne da ya kamata ya tsaya a tsakanin su ukun kawai, ko da ta kama zaren ta ja shi, ta hange shi da tsayin da ta kasa ganin karshen shi, burinta ne mafarin, yarjejeniyar da sirrin duk a tsakiya suke, karshen kuma sai ta dauka cikar burinta ne, shi tayi hasashe, shi ta shiryawa zuciyarta karba, ko a mugun mafarki bata hango burinta zai ci karo da kaddarar da ta dauketa tayi sama da ita, ta girgiza kafin ta tikota da kasa ba, faduwar da tayita akan sirrin da take ta riritawa, data mike kuma sai ya koma sama kafin tayi wani yunkuri ya dawo ya binneta da ranta!