ZaynabSadeeq's Reading List
51 stories
AL'ADUN WASU (Complete) by BatulMamman17
BatulMamman17
  • WpView
    Reads 225,179
  • WpVote
    Votes 16,168
  • WpPart
    Parts 45
Bahaushen mutum yana da kyawawan dabi'u wadanda addinin Musulunci da al'adunmu su ka koyar damu. Sai dai zamani yazo da wani salo, mun wayi gari bamu da abin koyi da tinkaho sai AL'ADUN WASU. Shin hakan hanya ce mai bullewa???
KU DUBE MU by BatulMamman17
BatulMamman17
  • WpView
    Reads 17,736
  • WpVote
    Votes 781
  • WpPart
    Parts 2
Sojoji sun zame mana wannan babban jigo a rayuwa. Sune suke sadaukar da duk wani farincikinsu ciki kuwa harda iyali da jindadin rayuwa domin tsaron lafiyarmu....shin wace gudunmawa al'umma take bawa wadannan jarumai da iyalansu???
A DALILIN KISHIYA  by sakee19
sakee19
  • WpView
    Reads 65,302
  • WpVote
    Votes 5,901
  • WpPart
    Parts 39
Rayuwa gaba daya ta canzawa Rabi a dalilin kishiya, duk wata dama da ta zata kauna ce ta sa ya hanata yanzu ya bawa amaryarsa wannan damar; harma ya na kafa mata hujja. Bata taba zaton zai yi mata haka ba ko mata nawa zai aura.
BAƘAR AYAH by SAKHNA03
SAKHNA03
  • WpView
    Reads 25,864
  • WpVote
    Votes 945
  • WpPart
    Parts 35
..........."Hajiya kar burin ɗaukar fansa ya shiga ranki,ki kasa gane wane irin makami kike son sokawa kanki da kuma danginki. Kawota cikin zuri'arki tabbas zata magancemiki Masifar da kike ciki,saidai kina ƙoƙarin korar macijiyane da wata macijiyar,kina ganin hakanne mafita?"..... ......."Ni bandamu damai zatayi ba,indai har zan daina buɗar ido ina kallon wannan matsiyaciyar a cikin gidana,to komai ma yafaru,ko mai zai faru saina sake ɗaura masa aure da wata,naga shin itama zata kasheta kaman sauran matan,ko kuma wannan zatafi ƙarfinta"...... "Zaro ido tayi ganin tabbas dagaske take abinda ta faɗa,shin hajiyah kuwa wacce irin uwace,bata damu da rayuwar ɗanta ba indai akan cikar burinta ne,hmmm zakuwa tayi maganinki kema,nidai babu ruwana,sojoji ma sunyi sun barta ballantana kuma ke".....ta faɗa a cikin ranta.......... ........Meee amarya tazo da ɗan shege wata biyu?! Sannan kuma a matsayin Budurwa akan Aurota???. "Eh haka ne,dan gatacan ma a falonta tana bashi mama,wai bataga wanda ya isa yasakata tashi tazo gaisheki ba ɗan bai ƙoshi ba"...... "Haka tace".... "Tabbass" Ohh nabaku satar amsa dayawa a cikin littafin Baƙar Ayah,mai son ganin mai zai faru yashigo a dama dashi kawai.......
ALK'AWARI BAYAN RAI (Completed✅) by HafsatRano
HafsatRano
  • WpView
    Reads 194,600
  • WpVote
    Votes 14,418
  • WpPart
    Parts 72
A story of a young girl who sees the bad side of the world from both angle.. Suddenly an angel came to her rescue.. Destiny will take it place.. Will he be able to rescue her? find out in this astonishing story
BA GIRIN-GIRIN BA  by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 61,978
  • WpVote
    Votes 8,387
  • WpPart
    Parts 36
BAN YARDA A YI COPYING DAGA NAN ZUWA KO INA BA, YIN HAKAN SHIGA HAKKIN MALLAKA NE ANA IYA MANA HISABI AKAN HAKAN Burin dukkan iyaye shi ne su aurar da ya'yansu da sun taka munzalin aure musamman ya'ya mata. Hakan ya kasance daga cikin Addini da Al'adunmu. Rashin aure kan haifar da damuwa a zukatan iyaye da su kan su ya'yan amma kamar yanda addini ya koyar da mu cewa "Komai da lokacin sa" shi ma auren ya shiga sahun "komai" ɗin. Gaggawa da kwallafa ran akan sai anyi aure ya sa da yawa daga cikin jinsinmu yin KUSKUREN da har su mutu suna nadamar sa. Jinkiri kan sa mutane su rasa tauhidinsu na duk abin da zai faru a doron kasa ya kan faru ne a bisa ga ikon Allah, in bai so ba hakan ba zai faru ba, kuma komai rubutacce ne, kuma alkaluma sun bushe. Sai su zama su na takurawa wanda aurensu ya zo da jinkiri da kalaman "Yaushe za ki yi aure?" ko kuma "Kin ki aure ko" abin tambaya ga duk wanda ya ke ɗaukan aure a wani hanyar nuna Darajan mutum shi ne "mai ya hana musu mutuwa" don kuwa aure, haihuwa da mutuwa lokutansu rantsattse ne. Babu abin takaici kamar a ce mace don ba ta yi aure ba, sai ma su kiran ta ki aure su zagayo suna neman ta da lalata don a ganinsu tun da ta ki aure toh mazinaciya ce. Wacce gaggawa ya dibe ta sai ta ba da kai bori ya hau don a tunanin ta hakan zai sa su aureta. Wasu daga cikin kawayensu kuma kan ɗauki rashin aure dalilin yanke zumunci da su, saboda a ganinsu babu kaskanci kamar rashin aure ko da kuwa auren da za'a rike zai kai su ga wuta ne ba Aljannar da kowa ke yin aure don nemansa ba. Tsabagen son aure ya sa tun yarinya na kwailar ta ake dasa mata ra'ayin duk abin da za ta yi don farin cikin wani ɗa namiji ne ba wai don kanta ko farin cikin mahallicinta ba. Sai ka ga don yarinya ta ci kwalliya ba za'a nuna mata tayi kyau don ta ji daɗi ba sai dai a nuna mata tayi kyau za ta burge wani ɗa namiji. A haka za ta taso in ba'a taki sa'a ba sai ta kai ga siyar da mutuncin ta duk don ta birge namiji.
WANI GIDA...! by jeeedorhh
jeeedorhh
  • WpView
    Reads 130,272
  • WpVote
    Votes 12,237
  • WpPart
    Parts 31
Tana shiga cikin dakin, taji an janyo hannunta anyi gefe da ita. Cikin tsananin tsoro da bugun zuciya ta daga baki zata saki ihu, taji an sanya hannu an rufe mata baki, a lokaci guda kuma aka juyata tana kallon wanda yayi mata wannan aika-aika. Ta saki wani numfashi da bata san lokacin data rike shi ba, ta jefa mishi harara cikin wasa. Duk da cewa manyan fararen idanunta babu abinda suke fitarwa sai tsananin kauna mai tsafta. Ya kasheta da murmushin nan nashi da har kullum yake kashe mata jiki, ya kanne mata idanu, "Hello, love!". * Wai bahaushe yace 'hali zanen dutse!', 'mai hali baya canza halinsa!'. Bahijjatu tayi tunanin wadannan duk fada ce kawai, sai da ta kwashe watanni shida bata cikin gidansu ta koma, ta ga babu abinda ya canza zani daga tsarin rayuwar gidan. Wata irin rayuwa ce ake yi a cikin gidansu mai matukar daure kai. Rayuwar da babu girmama na gaba, babu bautar Allah, babu kuma tsoron Allah a cikinta. Bata san cewa rayuwarta na shirin yin juyi wanda bata taba zata ko tsammani a wannan dawowar ba. Ku biyo matashiya Bahijjatu domin jin ta yadda zata karbi wannan canji da yazo mata babu zato balle tsammani, ba kuma tare da ta shirya ba. Wannan littafi kyauta ne, wanda zai dinga zo muku a duk lokacin da damar yin typing ta samu... :)
RAI DA KADDARA by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 77,718
  • WpVote
    Votes 7,816
  • WpPart
    Parts 59
Daada, Ku saka mata Munawwara, ku kira ta da Madina. Watakila albarkacin sunayen biyu rayuwar da bata da zabi a kanta ta zo mata da sauki ko yaya ne. Zan so kaina a karo na biyu, ku fada mata mahaifiyarta ta sota a watanni taran zamanta a cikinta, ko ba zata yarda ba Daada ki fada mata ta yafe mun, ki bata hakuri na yanda zata kare sauran kwanakin ta a duniya tana biyan zunuban mahaifanta. Kuma ku fada mata sunan baban ta Kabiru, yanayin haihuwar ta ba zai canza cewa ita din jinin shi bace ko da bata da gadon shi. Ke ma ki yafe mun, kiyi mun addu'a ko da rayuwa ba zata sake hada fuskokin mu ba. Yelwa.
KALMA DAYA TAK by AyusherMuhd
AyusherMuhd
  • WpView
    Reads 152,311
  • WpVote
    Votes 24,196
  • WpPart
    Parts 67
A rayuwata ban taba neman abu nawa na karan kaina ba, duk abinda aka tsaramin shi nake bi, ko inaso ko banaso abinda suka shimfidamin shi nake bi. Haduwata dake yasa zuciyata ta fara canzawa inaji kamar samunki shine cikar buri na rayuwata..... Sai dai me? Kalma guda daya tak daya kamata ta fito daga bakina ta wargaza miki rayuwa, na jefaki cikin kuncin rayuwar da nake ciki........
WAIWAYE... 1 by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 7,853
  • WpVote
    Votes 534
  • WpPart
    Parts 6
***Labarin WAIWAYE... #Dandano *** Na baku labarai kala-kala, a cikin su na baku labarin soyayyar data qullu a WATA BAKWAI, na zo muku da labarin tashin hankalin daya faru AKAN SO, kafin muyi tafiya a cikin RAYUWAR MU in da mukaga labarin Labeeb, ban gajiya ba wajen warware muku ababen da ALKALAMIN KADDARA ya kunsa da addu'a kawai take da tasirin sauya shi, ABDULKADIR ya zo da soyayyar da take ginuwa a bisa kyautatawa, kafin burin Hindu ya kaita hango MIJIN NOVEL, hankula kan tashi, zukata sukan girgiza lokacin da MARTABAR MU ta samu tangarda. * Tafiya ce ta ahali uku, tafiya ce da WAIWAYE...*ya hada kaddarorin su waje daya. Zan baku labarin iyaye uku mabanbanta da junan su, zan baku labarin uwar da ta mayar da yaranta jari, zan baku labarin uwar da ta amsa sunan domin kudi kawai, zan baku labarin uwar da ta so *WAIWAYE...* domin musayar zabin daya canza rayuwar nata 'ya'yan. Zan baku labarin SO, zan baku labarin KAUNA, zan baku labarin kaddarar da bata zuwa da zabi.