Ralyyaaa's Reading List
118 stories
AMAREN BANA by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 143,680
  • WpVote
    Votes 9,321
  • WpPart
    Parts 17
#9 in romance on 05/09/2016 "Wai ina son ki fada min, me yake damun ki ne, da za ki haddasa irin wannan fitina, sannan ki zauna lafiya, kamar ba abinda ya faru?" Dubansa ta yi a sanyaye, sannan ta-ce. "Ina da dalilina." "Wane irin dalili ne, zai sa ki na ji, ki na gani auren iyayenki ya mutu? Idan banda irin gurguwar tunani irin naki? Ashe ki na da halin yin gyara a wannan al'amari, ba za ki yi ba?" Mikewa ya yi daga kan kujerar zai tafi, da sauri ta kamo bakin rigarsa, ya tsaya, ganin zai saurareta, ya sa ta sakar masa riga. "An fada maka ni ma ina jin dadin ganinsu da na ke yi a haka ne? Sam, ba son raina bane, amma na daure na kauda kaina, saboda mu kawar da gagarumar matsalar da ta fi wannan. Na san halin Momi, tana da fada, tana da rashin son gaskiya, amma kuma haka tana da saurin nadama, na san za ta nemi afuwa, kuma Abba zai saurareta. Sai dai wannan tafiyar, dole ka taimaka ka ba ni goyon baya, don mu shawo kan al'amarin nan tare." Kallonta ya yi, ita ma duk ta jikkata, ta jejjeme ta zama wata iri, tabbas yadda take ji haka yake ji, koma fiye, don bayan baya sonta, ya tsani uwarta, sannan yana mutuwar son Meena. "Ki yi hakuri, amma ba zan iya aurenki ba." Ranta ya baci kwarai, har ya juya zai fita ta-ce. "Saboda me ya sa ba za ka iya aure na ba? Saboda me ya sa ban kai matsayin na zamo matarka ba?" "Ki fada min, ta yaya zan iya zama dake, alhali ki na matsayin 'yar matar da na tashi da tsanarta a zuciyata?" "Wane irin dalili zai sa maka tsanar mahaifiyata, har da zai sa ni ba za ka iya aurena ba?" Shiru ta yi don ta ji dalilin wannan tsanar.
DAUƊAR GORA...!! by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 9,110
  • WpVote
    Votes 339
  • WpPart
    Parts 6
Labari mai cike da bahaguwar cakwakiya, ɗimuwa, ruɗani tare da bam mamaki. tsantsar mulki da ƙarfin ikon masu mulki. tsaftatacciyar soyayya mai cike da nagarta da dattako.
GARIN DAƊI.....!  by ummishatu
ummishatu
  • WpView
    Reads 15,861
  • WpVote
    Votes 1,924
  • WpPart
    Parts 38
Tabbas lamarin so yana da rikitarwa domin yakan jefa zuciya so da kaunar wanda bai dace ba, a wani sa'ilin so na mayar da mai yinsa kamar wani zautacce Hakan shine ya faru da widat....!
MIJINA NE! ✅  by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 106,073
  • WpVote
    Votes 6,614
  • WpPart
    Parts 27
Ashe dama ana mutuwa a dawo? Ashe dama in mutum ya mutu, aka binne shi a kasa zaka iya ganinshi a rayuwarka? Kodai idonta ke mata gizo? Ko kuwa ta haukace ne? Aa, kila kuma kuncin da rayuwarta take ciki shine take ganin mutanen daya kamata ace tana tare dasu? Amma tabbas mijinta ne, shine. Ta tabbata shi din ne. Ga murmushin shi nan, dariyar shi, yanayin yadda yake tafiya. Wallahi shine! Shin mijin nata ne ko kuwa? Da gaske shi din take gani ko kuwa? Amma ba'a mutuwa a dawo. Saidai a yanayin yanda rayuwarta take juyata, takan iya cewa ita a nata fannin rayuwar, kila mutum yakan mutu sai ya dawo. Mijinta ne, kome zasuce bazata taba yarda dasu ba. Aisha Malumfashi.
MASARAUTAR JORDAN!!! by Mai_Dambu
Mai_Dambu
  • WpView
    Reads 235,556
  • WpVote
    Votes 19,800
  • WpPart
    Parts 61
Baiwa ce......A cikin masarautar Jordan....... Kuma a haka suke kallonta a matsayin baiwar Amma tun daga ranar da yaganta ya Fahimci ba Baiwa ce....... Akwai wani ɓoyayyen alamari da tare da ita..Shin me yasa tayi yunkurin kashe shi? Dukda ba farar fata bace daga wani yanki na duniya take? Shi da kanshi yasanya Hannu akan kundin tsarin Masarautar kuma babu wanda yayi yunkurin dakatar da shi, sai dai Kashi........Qaddara tariga Fata..........
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE) by Mai_Dambu
Mai_Dambu
  • WpView
    Reads 302,845
  • WpVote
    Votes 50,735
  • WpPart
    Parts 113
A zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun haɗakar soyayyan Abu daya! Domin farin cikin mutum daya domin samun farin cikin mutum daya! Dole sai an sadaukar da farin cikin mutum daya
BOROROJI....The Journey of Destiny!!! by Mai_Dambu
Mai_Dambu
  • WpView
    Reads 91,502
  • WpVote
    Votes 16,558
  • WpPart
    Parts 73
love and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....
BAƘO........  by ummishatu
ummishatu
  • WpView
    Reads 974
  • WpVote
    Votes 66
  • WpPart
    Parts 2
Matashi ne mai ji da kansa wanda baya taɓa ɗaukar reni sai dai yana da wata ɗaɓi'a guda ɗaya...... Baƙo ba asan halinka ba!!!
KALMA DAYA TAK by AyusherMuhd
AyusherMuhd
  • WpView
    Reads 152,238
  • WpVote
    Votes 24,196
  • WpPart
    Parts 67
A rayuwata ban taba neman abu nawa na karan kaina ba, duk abinda aka tsaramin shi nake bi, ko inaso ko banaso abinda suka shimfidamin shi nake bi. Haduwata dake yasa zuciyata ta fara canzawa inaji kamar samunki shine cikar buri na rayuwata..... Sai dai me? Kalma guda daya tak daya kamata ta fito daga bakina ta wargaza miki rayuwa, na jefaki cikin kuncin rayuwar da nake ciki........
ZABI NA | ✔ by fadeelarh1
fadeelarh1
  • WpView
    Reads 78,336
  • WpVote
    Votes 10,378
  • WpPart
    Parts 46
KWADAYI mabudin wahala, QARYA fure take bata 'ya'ya, DA-NA-SANI qeya ce sannan DAN HAKKIN da ka raina shi yake tsone maka ido!!