ummuhmanha83's Reading List
136 stories
Ba Ni Da Laifi by Shatuuu095
Shatuuu095
  • WpView
    Reads 2,755
  • WpVote
    Votes 324
  • WpPart
    Parts 16
Ba Ni Da Laifi! Kaddara tana zuwa maka a yadda baka tunani, Kuma a matsayin mutum na musulmi Dole ne ya karba wannan kaddarar. Ko kunsan meye tawa kaddarar? Hannuna na rawa na karba takaddun da Dadaa yake Miko min, Ina karba cikin sauri na bude envelope din, a take naga takaddu da yawa, sunan Zayyad Abdulhamid ne a jiki, a take gabana ya fadi, nayi saurin scanning cikin paper da idanuna da suka firfito kamar zasu fado kasa, takardar farko wadda ta kasance ta asibitin koyarwa da ke garin Lagos, ta can kasa result din genotype dinshi ne "AS" na dago hannuna na rawa nace " Dadaa Amma ba Zayyad di na ba ko? Bashi bane AS ko? Dadaa..." Tuni idanuna Suka fara zubar da hawayen, na tuna farkon haduwar mu, na fada Masa Ina da sickle cell disease, se yace min Yana da tabbacin jinin shi AA ne, Amma Kuma ya nake ganin akasin Haka. " A'isha ki saurare ni!" Nayi saurin katse shi Nima Ina fadin " Dadaa Ina son shi, Dadaa ku Kara dubawa ba lallai wannan result din gaske bane" To Amma me? Takaddun hannuna sun nuna result da yawa har da na AKTH, Shika, national hospital! Result din Ina nake nema Kuma? Bayan wannan hudun dukka asubutoci ne da ake ji dasu a kasar nan Baki daya. Hawaye ya cigaba da sauka min, Ina jin kamar zuciyata ana babbaka ta ne, Ina jin kamar blow din yayi min yawa! Ba Ni Da Laifi kasancewa ta me sickler, kasancewar genotype dina SS ne! Amma bansan me yasa mutane ke gudu na ba, bansan me yasa kowa baya Sona ba, shi ma Zayyad Dana kwallafa Rai na Akan shi se jinin shi ya kasance irin Wanda bazan iya Zama dashi ba! Labarin sabo ne! Salon ma Kuma sabo ne! Tafiyar ma Kuma sabo ce! Labarin na A'isha ne, ko Kun taba Jin labarin sadaukar wa? Ko Kun taba ganin labarin kauna da soyayya? Ni din nan ce shatuuu, ni din na rubuta Unaisa, Kuma na rubuta Mace a yau, na rubuta Afiyya da Fara Yar shehu!
CIWON - SO by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 10,471
  • WpVote
    Votes 952
  • WpPart
    Parts 16
A masarautar ABIEY. Soyayyah ce kawai abun da ke iya sada rai da rayuwa. Sai dai a duniyar ZAHRA soyayyah wata hallinta ce da bata da mahadi da rayuwa, tun a wata kunyatacciyar rana da Iyalan ABIEY suka fitar da kansu daga duniyarta! DEEN ya zama wani bangare na rayuwar ABIEY da ZAHRA, ya sabunta wasu shafukan na rayuwarsa da ta su, ya kuma jefar da wasu. A yayinya da ra'ayoyin juna ya fara girmama, sai tafiyar ta sauya salo, dogon zaren ya tsinke. Tabbas rayuwa bata da sauki ga mutanen da soyayyah ta auresu. Sai dai shagaltuwa ya saka zuciyoyinsu yin wasi-wasi. CIWON - SO labari ne da aka gina akan wata irin soyayya mai ratsa jini da zuciya.
KUNDIN HASKE💡 by Pherty-xarah
Pherty-xarah
  • WpView
    Reads 302,903
  • WpVote
    Votes 23,824
  • WpPart
    Parts 160
Hannu da yawa...... 🤝🏻🤝🏻🤝🏻
Anyi Walk'iya....... by meenaslimzy
meenaslimzy
  • WpView
    Reads 90,523
  • WpVote
    Votes 6,026
  • WpPart
    Parts 50
Banida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamnati Sena baiwa k'adangarun gwamnati damar dazasu lalata rayuwata? idan naje lahira Sena cewa Allah sabida Ina gidan marayu nake Zina? ki gane Mana maryama nifa wlhy Koda zasu kasheni bazan tab'a aikata abinda kuke aikatawa ba sedai ko su kasheni, Kuma dasuke cewa watak'il ta hanyar Zina aka haifeni ba wannan Kuma ba zunu Bina bane ba, dadai into zinar gwanda suci gaba da hanani abincin har yunwar ta kasheni!!!!!.
ABBAN SOJOJI by BossBature88
BossBature88
  • WpView
    Reads 52,328
  • WpVote
    Votes 981
  • WpPart
    Parts 19
💋Romantic Love story💋 Labarin matashiyar yarinya wadda ƙaddara ke kaita aikatau gidan sojoji tayi shigar maza Amatsayin ɗan aiki, gidan Abban sojoji wanda yakasance chief of Army staffs, ƴa'ƴansa goma shatakwas duk maza masu riƙe da manyan muƙamai na sojoji 💋💘💞
KAUTHAR!!  by jeeedorhh
jeeedorhh
  • WpView
    Reads 8,995
  • WpVote
    Votes 271
  • WpPart
    Parts 6
Yadda ya daga kai yana kallonta ne yasa ta shiga taitayinta babu shiri. Ya fara dumfararta gadan-gadan, kamar wanda yake shirin cinyeta danyarta. Duk dauriyarta kasawa tayi, ta fara ja da baya a rikice, idanunta sun fito waje kuru-kuru, dankwalin dake hannunta ta sanya tana kare fuskarta kamar shi zai kwaceta daga hannunshi. Sai daya danganata da bango, ta jita ta lafe a jiki kamar zata shige ciki., Ya duka yana kallon tsakiyar idanunta da wani irin murmushi na gefen baki kwance akan fuskarshi, taji wasu abubuwa masu kama da jan wutar lantarki na yawo a sassan jikinta.... Murmushi ya sake saki, "kina ta babatu da daga murya akan Anty Ummynki Kauthar, sai dai, me yasa dana kalleki nake ji a jikina kamar ba ita kike tayawa kishi ba? Me yasa nake ji kamar.... kishina ne yake cinki? Me yasa nake hango tsabar kishina kwance a cikin idanunki, iye Kauthar? Me yasa??!!!". Ganin yadda take faman zare idanu kamar kazar da aka lakume za a yanka, yasa ya ja da baya, wannan murmushi nashi dake matukar bata mata rai yana kara fadada akan fuskarshi, sai ya juya ya fita daga dakin. Ta sani, kamar yadda ya sani, bashi da sauran ta cewa, don kuwa ya riga ya gama daureta kam da jijiyoyin jikinta! Ta silale a jikin bangon, zuciya na bugu kamar zata fasa kirjinta, ta samu kanta da maimaita tambayarshi a gareta, 'Me yasa? Kuma me yake nufi?!'. ***************** ***Zaku iya samun cikakken labarin a HIKAYA BAKANDAMIYA yanzu***
BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach}  by SiyamaIbrahim
SiyamaIbrahim
  • WpView
    Reads 12,662
  • WpVote
    Votes 1,390
  • WpPart
    Parts 46
"Make sure you take good care of your sister duk runtsi da tsanani kar ki bari ki karaya ko ki sami rauni dangane da abin da kika saka a gaban ki,ki sani,horon da kika samu sama da shekaru ashirin da uku tun kina jaririyar ki,farat ɗaya ba'a isa a ƙwace maki shi ba sai in ke kika bada damar yin hakan dan haka nake ƙara jadadda maki kamar yadda kika yaƙi sojoji ɗari biyu da talatin da bakwai da aka sako su daga masarautar OTTOMAN haka zaki jajirce ki cigaba da yaƙar duk wasu maƙiyan ki da zasu biyo ki,make sure you find your sister and take her far away from Ottoman promise me"!!haka jikin ta na ɓari gaban ta na faɗi zuciyar ta na daɗa bushewa sakamakon ƙudiri mai nauyin gasken da ta alkawarta ma kan ta.. Wuf ta miƙe ta tashi tsaye ran ta na tafasa zuciyar ta na rura mata wani irin hucin ɓacin rai.. Kamar ƙiftawa da bisimillah ta zari doguwar takobin da ke gefen ta lulluɓe cikin marufin fatar sa da ke sagale a jikin rigar ta ta soƙe shi da shi ta daɗa tursasa takabin ciki ta juya shi ta yadda zai illata kayan cikin sa,ta cire takobin ta kuma yunƙurawa da iya ƙarfin ta ta kuma caka mai a daidai inda ta cire na farkon..ƙasa yayi yana nishi daga bisani numfashin sa ya ɗauke ɗif.. Kallon matar tayi idanun ta a ƙuntace ta mata kallon ƙarshen sannan ta juya ta yanki daji tayi wucewar ta.....!!! DON'T MISS OUT THE THRILL..... Don't forget to click on the button "Vote&Comment" in order to continue enjoying the atmosphere......
IYA RUWA FIDDA KAI(THE LOVE SAGA) COMPLETED by SiyamaIbrahim
SiyamaIbrahim
  • WpView
    Reads 93,191
  • WpVote
    Votes 6,040
  • WpPart
    Parts 55
Ta kasance kyakyawar yarinya mai ilimi da kwazo wanda ilimin ta zai kasance mata abin alfahari a gare ta bata da isashiyar lokacin kan ta kuma bata da lokacin sauraron maza komai ilimin namiji da arziƙin shi bai kai mata matsayin wanda zata saurara ba Ya kasance kyakyawan namiji mai ji da kai da izza haɗe da ƙarfin zuciya bai da lokacin ko wace mace a rayuwar shi illah yarinya ɗaya da ya kasance yana burin mallaka a rayuwar sa amma ita kuma yarinyar bata san yana yi ba. Ya tsani halin ta na izza da jijin kai haka ita ma ta tsane shi shi da halin shi dan ba su da kyakyawar fahimta tsakanin su The two will keep on clashing on each other countlessly Don't miss out the exciting,explosive,romantic,hot love story, tragic,pains,cheat,wild thoughts,brainstorming and lot more Keep up with siyama ibraheem on this amazing love epics of IYA RUWA FIDDA KAI(the love saga) make sure you don't miss any part of the book Is yet to come your way very soon!!!! Vote and drop ur comments
AL-HUSSAIN Complete by Halimahz
Halimahz
  • WpView
    Reads 4,151
  • WpVote
    Votes 395
  • WpPart
    Parts 30
*_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da siffofi guda biyu, ko ta siffantu da alkhairi ko kuma ta siffantu da jarabawa kala daban-daban....ka zalika acikin kowanne duniya kuma kowacce rayuwa, ƙaddara na tafiya ne dai-dai da rayuwa, kuma ta rayu damu cikin farinciki ko akasin hakan, sannan babu wani bawa da yake iya gujewa ƙaddararsa, cikin kowacce rana da kowanne lokaci ƙaddararmu na gudana ne ajikinmu tamkar jini, kuma kamar yanda rayuwarmu ta ke mabanbanciya haka ita kanta ƙaddarar ta ke...yanda kundin ƙaddararsu ya buɗe yasha banban dana saura, kuma tabbas da ace suna da iko, da sun ɗau wannan kundin ƙaddarar sun shafe komai dake cikinsa, tukunna su ƙara tsara shi zuwa wata sabuwar rayuwar da ba zata haɗa hanya da waccen ba...WAYE NI? wannan tambayar me kalmomi biyu da harufa shida ke yawo kullum a cikin kan AL-HUSSAIN, da su yake kwana yake tashi, kuma acikin tsumayin jiran lokacin da ganyensa zai bushe ya faɗo zuwa ƙasa, daga nan shikenan sai ya zama tarihi...sai dai abinda AL-HUSSAIN bai sa ni ba shine; zaren wata ƙaddarar na sauyawa ne a sa'ilin da adu'a kaɗai ke iya sauyata...to amma a ɓangaren SABINA da ta san WACECE ITA fa?, idan har ƙaddara na ɗaure a wuyan kowanne bawa to abun tambayar shine mecece tata ƙaddarar? ya ya ta ke? da yaushe zata fuskanceta? ta wanne irin yanayi zata zo ma ta? mai kyau ce ko kuma mara kyau? zata iya karɓanta ko ba zata iya ba?...wata ƙaddarar kamar zanen dutse ta ke da babu abunda ke iya sauyata!..._*
UNAISA by Shatuuu095
Shatuuu095
  • WpView
    Reads 3,724
  • WpVote
    Votes 446
  • WpPart
    Parts 11
A yanzun maza da yawa suna shunning daga responsibilities dinsu, kamar yadda mahaifina ya auri mahaifiyata ya barta take daukar dawainiyar mu. Idan ya dawo ta samu ciki se ya tafi yayi shekara biyar Bai dawo ba, mu din mun tashi a hannun mahaifiyar mu, ita din ce komai namu, cinmu, shanmu da Kuma suturar mu. Sunana Unaisa wadda akeyiwa take da gayun duniya, ni din Yar gayu ce Kuma kyakyawa me ilimi.....