oumsamhat's Reading List
2 stories
YARDA DA KAI (Compltd✔) by Oum_Nass
Oum_Nass
  • WpView
    Reads 81,856
  • WpVote
    Votes 2,359
  • WpPart
    Parts 13
ldan YARDAR KA tayi yawa akan mutane, to kamar ka basu lasisin kwaye maka baya ne. Awanan duniyar tamu da son kai yayi yawa, cin amana ta zama ruwan dare, ka yarda da mutum yaci amanar ka, ɗan uwa ya tsani ɗan uwan sa saboda wata ɗaukaka ta duniya. Wanan shi ne ga janyo ƙin yarda da kowa arayuwar AHMAD NASIR, zuciyar sa ta bushe da ƙiyayyar mutane, ayayin da gefe guda yake tsoron mu'amala ta haɗasu da ko wani mutum ciki kuwa harda ƴan uwan sa. LABARIN YADDA DA KAI yana magana akan yanda zamani yayi hautsinewar mugunyar ɓarna, sakaci da al'amura suka ƙarama mai rauni raunika acikin zuciya.
RASHIN UBA by oumsamhat
oumsamhat
  • WpView
    Reads 63,065
  • WpVote
    Votes 4,285
  • WpPart
    Parts 33
"RASHIN UBA! Itace kalmar da ke cinye zuciya da kuma daƙusar da karsashin ko wani yaro! Fatan ko wani UBA shine kafa ma yaransa kyawawan tarihi da bar musu gobe mai kyau. Sai dai mu kam namu UBAN kallon matacce muke masa, da babu amfanin wanzuwarsa a tare da mu. Shin dama maraici ba sai an mutu ake yinsa ba? Na yi fatan ace mutuwa ce ta shuɗe labarin mahaifinmu, ba mu ne labarin ya duƙun-ƙune ya cutar damu akan sakacin Uba ba. Da mamaki ace yara na fatan mutuwar UBAN SU! Amma idan zamani yayi rakiya babu abin da ba zai iya sauyawa ba. Ciki kuwa harda RASHIN UBAN da bai zama gawa ba. Sunana MAIRO kuma wannan shine labari nah!"