neenatusman's Reading List
102 stories
NANA AMINATU 2022 by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 16,325
  • WpVote
    Votes 916
  • WpPart
    Parts 56
Maganganun ta tamkar saukar kibiya take jin su a zuciyarta duk idan ta tuna, suna sukan ta su hana ta sukuni, suna tarwatsa ta su saka ta taji ita ƙasƙantanciya ce wacce bata kai ɗin ba kamar yadda take cewa, tana ganin baƙin kanta a koda yaushe a wacce bata kai ba, ko kaɗan bata taɓa saurara mata ba, ya za'a yi ta dena kallon kanta ta daban a cikin mutane yayinda take tuna duk wata kalma ta ɓatanci da take bin ta dasu a kullum ranan duniya? tun sanda ta buɗe idanuwanta da wayon ta take jin waɗannan munanan kalaman da ke tarwatsa mata duk wani farin ciki da jin daɗin ta. Sai dai kuma a duk sanda take jiyo kalaman sa sai ta ji ƙwarin gwiwa har ta kalli kanta a wacce ta kai kuma ta isa, ashe akwai ranan da zata yi farin ciki haka? Akwai ranan da wani zai iya yabon ta har ya nuna mata tana da matsayi fiye da sauran Mata? She can't believe that... Shi ne Mutum na farko da yake faɗa mata kalaman da idan ta ji su take ganin ta kai Mace, ta kai Mace cikakkiya ba wacce ta rako Mata ba, a kullum ganin kanta take yi a bata kai matsayin ba, ita bata kai Macen da zata iya fitowa ayi gwagwarmaya da ita a matsayin ta na ɗiya Mace ba. Shin wane ne shi wannan ɗin? Tabbas Ƙaddara kowa da irin tasa, wasu tana zuwar musu da sauƙi wasu kuwa akasin hakan, ba wai don wani ya fi wani bane a wurin Allah hakan ke faruwa, a'a, sai dai don Allah na gwada ko wanne bawa ta hanyar ɗaura masa tashi ƙaddaran, walau me sauƙi ko akasin sa, ko wanne bawa da tashi ƙaddaran kuma kowa yana fatan ace ya tsallake ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa. Haka itama NAANA AMINATU tayi fafutuka a cikin rayuwar ta domin ta ga ta cinye nata ƙaddaran da ta kasance babba a gare ta. Na san Kuna so ku bibiyi labarin ta domin ku ji mene ne ya faru a rayuwar ta, to ku bi Ni sannu a hankali Zan warware muku komi a cikin sauƙi, ina fata labarin zai zame muku darasi a cikin rayuwa.
HAIRAN🔥💥♥️ by Shatuuu095
Shatuuu095
  • WpView
    Reads 7,009
  • WpVote
    Votes 160
  • WpPart
    Parts 23
Tunda Anty ta fara magana, Prof yake kallon ta, idan ka kalle shi ba zaka taba fahimtar a yanayin da yake ciki ba, ba zaka fahimci emotions din shi ba, Amma yadda yake kallon Anty, da yadda ya bata dukkan hankalin shi, Abu ne da zai tabbatar maka cewar maganar babba ce. Anty ta gama bayanin ta tsaf sannan tayi shiru tana jiran ganin hukuncin da Prof zai yanke. Cikin nutsuwa yace " A Ina ta samu?" Shi ne tambayar da yayi ma Anty, maimakon tayi masa bayani se cewa tayi " Ai na Gama nawa professor, abin da ya rage kaji ta bakin HAIRAN kawai!" "Me yasa Anty?" Cike da nutsuwa tace " Saboda zaka ga kamar kare ta nake, Amma idan tayi maka bayani Ina Jin zaka fi gamsuwa da kyau!" Daga haka Prof yayi shiru Yana son ya auna nauyin Abubuwan da Anty ta fada Masa, se kawai ya Mike yayi ma Anty sallama ya fita. Kunsan yadda tsumma yake idan aka tsoma shi cikin ruwa ko? To haka Prof yayi, gaba daya jikin shi ya saki, yayi shiru tamkar wani kurma, ya bude mota ya shiga ya kifa Kan shi akan steerer wheel, shi yasa take fada Masa lallai lallai se sun rabu kenan? To Ina ta samu shi ne tambayar da take zuwa Masa... *** Shigowa ta kenan daga lecture, na gaji, gajiya kuwa matuka saboda shirin exams da muke, har lokacin bana cikin dadin rai, Abu ya kusa wata daya Amma still nukurkusa ta yake Yi. Ina Zama Saman gado Ina kallon Nuriyya da ta dakko wani gari tana kokarin kwaba shi da ruwa nace " Me zakiyi?" Tace "Kunun aya Mana!" Se nace " Kunun Aya Kuma, gaskiya Kin iya bawa Kai wahalar, ana shirin exams din!" Tayi dariya tare da daga min wata transparent ziplock tace " Waye zai Baki wani wahala, wannan ai is outdated, halan Baki San Islah foods ba ko? To ita take siyarda wannan garin na kunun Aya, yours is just to make little effort se ki Sha!" Nayi murmushi Amma kafin nayi magana se Naga Kiran Anty na shigowa cikin waya ta, da sauri nayi excusing Kai na sannan na mike Dan fita
BILLIONAIRE'S second chance ✔ by HephziLolami
HephziLolami
  • WpView
    Reads 955,375
  • WpVote
    Votes 29,739
  • WpPart
    Parts 31
Billionaire's series~ 2 Monica Ambrosia left New York four years ago with a broken heart and a pregnancy test confirming the worst. Or maybe it was the best because she had the chance to get a new life, feel loved again and discover herself. But that dream is short lived when Sucre Ambrosia, the man that broke her heart years ago waltzes back into her life and acts like nothing happened, blaming her for leaving him without an explanation. Feelings are reignited and secrets are revealed. Only, Monica refuses to give him a second chance because, What if he breaks her heart again?
RUWAN ZUMA (completed) by suwaibamuhammad36
suwaibamuhammad36
  • WpView
    Reads 39,574
  • WpVote
    Votes 2,691
  • WpPart
    Parts 24
Shin wani irin kallo kake yiwa masoya biyu wad'anda akwai tazarar shekaru tsakaninsu, musamman ma in aka ce Macen ta fi Namijin yawan shekaru? Tayi wuff dashi, ko Tsoho yayi wuff da yarinya. To ga labarin wani matashin saurayi mai farin jinin 'yan mata amma shi hankalinsa kwata-kwata ba ya kansu dalilin tun asalin fari Aliyu Haydar yafi son auren mace wacce ta girmeshi da yawan shekaru. Ana haka ne kuma ya had'u da Laila Kashim wacce ta dace da duk tsari na matar aurensa. A yanzu kuma da mutanen duniya suke kyama game da kushe irin wannan tarayya shin Aliyu Haydar da Laila zasu cika burinsu ko dai zasu iya hak'uri da juna don gujewa zagin duniya a kan tarayyar da Allah ya halatta? Soyayya... RUWAN ZUMA
DA AURENA by HauwauSalisu
HauwauSalisu
  • WpView
    Reads 64,071
  • WpVote
    Votes 2,661
  • WpPart
    Parts 59
DA AURENAH labarin wata yarinyace da tasha gwagwarmayar rayuwa silan auren mugun miji da sa hannun babbar ƙawarta,wadda ƙarshe ta aure ma ta miji bayan sun gama lalata a gabanta cikin dakinta , ta wani gefen kuma tana tare da baƙin cikin mutuwar wanda ta tsara rayuwar aure dashi , karshe akai ma ta auren dole wanda ya jefata cikin gararin rayuwa .ta samu kanta da kaunar ɗan'uwan mijinta wanda shima ta kamashi da cin amanarta ,
LABARIN AURENA by DeejahtAhmad
DeejahtAhmad
  • WpView
    Reads 19,827
  • WpVote
    Votes 1,095
  • WpPart
    Parts 18
Labarin soyayya, sadaukarwa, cin amana... Najib da naila sun taso cikin jin dad'in rayuwa even thou mahaifan Naila r ol late, Najib ma mahaifinsa ya rasu, he's living with his mom. Sunyi aure bisa ga soyayyar da suke wa juna komai na morewar rayuwa se hamdallah se dai d'an adam tara yake baya ta'ba cika goma suna lackn abu guda d'aya rak! d'aya rak wanda rashinsa ya jefa su cikin 'kangin rayuwa.. d'aya rak yasa su afkowa kansu abinda ya ja su ga da na sani.. #Romance#love story#a little bit steamy#
YARDA DA KAI (Compltd✔) by Oum_Nass
Oum_Nass
  • WpView
    Reads 82,092
  • WpVote
    Votes 2,365
  • WpPart
    Parts 13
ldan YARDAR KA tayi yawa akan mutane, to kamar ka basu lasisin kwaye maka baya ne. Awanan duniyar tamu da son kai yayi yawa, cin amana ta zama ruwan dare, ka yarda da mutum yaci amanar ka, ɗan uwa ya tsani ɗan uwan sa saboda wata ɗaukaka ta duniya. Wanan shi ne ga janyo ƙin yarda da kowa arayuwar AHMAD NASIR, zuciyar sa ta bushe da ƙiyayyar mutane, ayayin da gefe guda yake tsoron mu'amala ta haɗasu da ko wani mutum ciki kuwa harda ƴan uwan sa. LABARIN YADDA DA KAI yana magana akan yanda zamani yayi hautsinewar mugunyar ɓarna, sakaci da al'amura suka ƙarama mai rauni raunika acikin zuciya.
SHU'UMAR IZZAH  by BilkisuAhmad2
BilkisuAhmad2
  • WpView
    Reads 3,747
  • WpVote
    Votes 164
  • WpPart
    Parts 22
Duniya cike take da abubuwan al ajabi,tabbas akwai rud'ani daban tsoro,azamanin dayakasance ita kad'ai ke mulki adaular ta wacce ta had'a da aljanu da manyan bokaye tazuba izzah uwa bazata mutuba,duk da shekaru dubu biyu dasuka shud'e amma ya akai takeso ta cika qudirinta bayan tashud'e adoron qasa,ya iyayen jawahir zasi saboda shu'umar izzah datasawa kanta afamilynsu ,bayan kowannensu yakasance d'an boko ga kud'i wannan se alittafin shu'umar izzah karki sake abaku labari!!!!!!!!
MATAR K'ABILA (Completed) by suwaibamuhammad36
suwaibamuhammad36
  • WpView
    Reads 436,164
  • WpVote
    Votes 30,487
  • WpPart
    Parts 58
Anwar Bankudi, the Handsome Young Millionaire ke zagaye da matan Aure uku, kowacce da salon halinta da matakin matsayinta a zuciyarsa. Shin wacece Tauraruwarsa? Rayuwar gidan Bahaushe mai cike da sark'akiya had'e da zallan zaman aurenmu a yau.
DOCTOR EESHA👩‍⚕️ by JafarHajara5
JafarHajara5
  • WpView
    Reads 46,889
  • WpVote
    Votes 991
  • WpPart
    Parts 56
labari ne data kafu aka kadara🙇🙇 Kubiyoni ku ji yanda LabariDr. Essha Ahmad zata Kaya da Young Tycoon Namji Mai ji dankashi Aliyu Umar Tycooon 💃💃💃💃💃 Ko ya ya zai kasance 🤔🤔🤔 Sai mu Haduuu