Asiya bakori reading list
49 stories
YA JI TA MATA by miss_untichlobanty
miss_untichlobanty
  • WpView
    Reads 88,193
  • WpVote
    Votes 8,201
  • WpPart
    Parts 63
Wannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsira ba domin kuwa babu wacce take iya zaman sati biyu dashi tsanani kwana 10 sai su gudu. Toh fa an Sami matsala domin reshe ta juye da mujiya inda Allah ya hadosa da Wanda ta fisa jaraba toh yanzu kuma shi ke gudu. Wai ya za'a kwashe ne a lokacin da iyayen sa sukace bai isa ya saketa ba kamar yadda ya dafa kur'ani cewa bazai saketa ba? KU BIYONI CIKIN WANNAN LABARI NAWA DAN JIN YADDA ZA'A KAYA. SAURAN LABARAI NA: 1.KURUCIYAR MINAL 2. YARINYAR CE TAYI MIN FYADE AND NOW 3. YAJI TA MATA.
BAHAUSHIYA.....!? by Mai_Dambu
Mai_Dambu
  • WpView
    Reads 40,085
  • WpVote
    Votes 3,362
  • WpPart
    Parts 22
'YA CE kamar kowa wadda ta taso cikin ɗabi'a da al'ada irin ta BAHAUSHE! "Me ta ke so? Me nene burinta?" Babu wanda ya taɓa tambayarta. Kalma ɗaya ce ko yaushe take hawa kanta "KE BAHAUSHIYA CE! Ko me da ke gareki zai zama irin na Hausawa ne." Tabbas Bahaushiya itace macen da ke shimfiɗar da rayuwarta dan kula da mijinta da yaranta. Itace mace guda da ke killacewa ƙarƙashin igiyar riƙon Ɗa Namiji, da ke kiran shine mafi rinjaye akanta. Sanan Kalma guda da yake nanatawa, Rayuwar 'YA MACE kamar gilashin da ke riƙe a dungulumin hannu ne, ko wani lokaci zai iya faɗuwa dan ya tarwatse ne. Idan aka ci gaba da ganinsa to zai zama shuɗaɗɗen labarin rayuwarsa. Tabbas bayan karatun allo babu buƙatar biyantar da kururuwar zamani wajan tsoma hannayenta dumu-dumu dan janta da tafiya a ƙarƙashin hasken Nasaran da ke da jajayen kunnuwa.
DIYAR DR ABDALLAH  by Aynarh_dimples
Aynarh_dimples
  • WpView
    Reads 46,864
  • WpVote
    Votes 6,343
  • WpPart
    Parts 32
Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wannan yanayin ba. Yanayin da zai zama useless baida amfani. Sai yanzu ya lura da dalilin dayasa ya kasa barci. Ba komai bane illa wannan sabon shafin dake baƙunta sa. A hankali yake mamayansa, ya shammace shi cikin dare. Yanzu gashi yazo yayi kane kane yana kokarin gina muhalli cikin rayuwarsa. Tabbas zuciya batada ƙashi, kuma ba'a kwaɓanta. Amma idan tace zatayi mashi abinda yake tsammani bata kyauta mashi ba. Tayi mugun cutan sa. Ya kamata tayi tunani saboda abinda take so yafi karfin ta. Runtse ido yayi ransa yana mashi ɗaci. Shi dama dukansa akayi da itace zai fi jin daɗi akan raɗaɗin dayake ji cikin ransa. Akwai abubuwa da ke faruwa da bawa wanda baida ikon hanawa. Kamar yadda zuciyar sa take raya masa ga abinda takeso yanzu, idan kuma bata samu ba tabbas zatayi masa tijara. Toh tijara na yaushe kuma, fafur ta hanashi barci. Murmushi yayi na takaici, "akwai ƙura," yace a fili. Dimplicious Empire, ku biyoni sannu a hankali domin jin wannan labari. Love you Fisabillahi ❤️
RAYUWAR BADIYYA ✅  by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 276,583
  • WpVote
    Votes 21,590
  • WpPart
    Parts 61
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi. Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai. Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu. _______ Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?
UWA TA GARI (EDITING) by Ishamoha
Ishamoha
  • WpView
    Reads 46,413
  • WpVote
    Votes 4,179
  • WpPart
    Parts 57
Jawahir yarinya ce 'yar kimanin shekara sha takwas wacce take tsananin son mahaifinta kwatankwacin yanda take kin mahaifiyarta. Bata shakkar nuna soyayyarta ga mahaifinta a gaban kowa ciki kuwa harda mahaifiyarta dukda tanada masaniyar cewar mahaifanta sun dade da rabuwa. Zata zauna hannun matar uba wacce zata gana mata azaba irin na matan uba wanda imani ta musu karanci. Mahaifiyarta me sonta zata ceceta ba tareda tayi fushi akan halin da 'yarta ke nuna mata ba.
AL'AMARIN SUHAILA  by cynosure3
cynosure3
  • WpView
    Reads 5,939
  • WpVote
    Votes 515
  • WpPart
    Parts 53
Heart touching story
KUSKURE DAYA by Atize21
Atize21
  • WpView
    Reads 127
  • WpVote
    Votes 8
  • WpPart
    Parts 1
Arziqi da yaya sune silar farin ciki a gurin dan adam, a duk inda mutum ya samu daya zai ta qoqari wajen ganin ya samu dayan, in kuwa ya rasa za ka same shi cikin yanayi na rashin walwala sai dai masu tawakkali su kan mi qa ma Allah lamarin su har su kai ga samu abun da suke muradi. A wannan ahalin ba haka bane, haqiqa Allah ya azurta ta su da duk wannan abubuwan har ma da qarin ilmi, wanda shine gishirin zaman rayuwar. amma KUSKURE DAYA ya hana musu samun farin cikin da suke gani gashi daf da su amma ya gagare su samu. **** 'sai yaushe rayuwar mu zata daidaita ne mu ma mu samu daidaito? 'yaushe zamu gane wannan rayuwar mai yanayika mabanbanta inda ta dosa, 'ko yaushe zamu samu farin ciki ---- ko me ta tuna kuma ta gaza qarasa kalmar ta, sai kuma murmushi da ya zo mata a ba zata, tayi shi ba tare da tasan ma murmushin ya subuce mata ba. dan a halin da ta ke ciki wannan murmushin ba gayyatar sa tayi ba,fuskar ta ta dago mai dauke da idanuwanta dara dara masu haske da qyalli gwanin kyau, masu yalwar gashi da kuma cikar gira da ta qara qayata mata su, don in har da ido ake gane kyau to tabbas ita din tana cikin kyawawa, qyallin idanuwan na hango kawae ban samu damar qare mata kallo ba sbd duhun gurin da take zaune, hasken farin wata ne ma ya qara taimaka min gurin gano idanuwan sbd qyallin da sake. 'zaune take ita kadai take ma kanta tambayoyin da bata san amsar su ba, Korda ace wani ta tambaya daga cikin waanda zata iya tambaya amsar dai daya ce, duk a xuci take wannan mahawarar, sai dai tana sane da alqawarin Allah na cewa duk tsanani yana tare da sauqi. inaga wannan dalilin ne ma yasa ta murmusa. **** ku biyoni don jin lbrn wannan ahalin, ahalin malam taju da irin tasu qaddarar a rayuwa, mai dadi da akasin hakan tunda ita rayuwar haka ta gada.
🔥Huda🔥💄 by Aysha_sona
Aysha_sona
  • WpView
    Reads 30,388
  • WpVote
    Votes 2,342
  • WpPart
    Parts 95
Huda kyakyawar yarinya ce son kowa kin wanda ya rasa. Amma iyayen ta sun kasance talakawa gaba da baya. Ta taso cikin wuya da kuncin rayuwa. Rasuwar mahaifinta yasa ta kuduri niyar samun kudi ko ta halin yaya ne. Bata abota da kowa sai masu shi. Ta dauki sona abun duniya ta daura wa kanta. Amma son mutum daya data kamu dashi zai iya barinta ta cimma burinta? Wanan labarin yana dauke ta tarin soyayya, cin amana, yaudara da kuma irin halin da yan mata masu son abun duniya suke jefa kansu ciki.💔
MUTUM DA DUNIYARSA...... by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 129,512
  • WpVote
    Votes 9,449
  • WpPart
    Parts 41
Wannan labari labarine da ya taɓo rayuwar da mafi yawan mata ke fuskanta a wannan rayuwar, tare da rayuwar kishi na gidajen aurenmu, da nuna jarumtar mazan ƙwarai da ke aiki da hankali da ilimi wajen tafiyar da ragamar rayuwar aurensu. Magidanta da yawa basa son a haifa musu ƴaƴa mata, abin kuma zai baka mamaki idan zaka tarasu wajen buƙatar jin dalilinsu, musani UBANGIJI ya fimu sanin mu su wanene? miyasa yayimu jinsi-jinsi, yare daban-daban, zuri'a daban-daban. kai dai ka roƙi ALLAH ya baka mai albarka kawai shine magana.
Nafi karfin aurenshi (girman kansa yayi yawa) by sharhabilasuleiman
sharhabilasuleiman
  • WpView
    Reads 8,725
  • WpVote
    Votes 584
  • WpPart
    Parts 15
haduwace ta bazata inda yayi mata rashin mutumci batare da yasan ko ita waceceba. itama takasance bata barin kota kwana inda ta nuna masa ruwa ba sa'an kwando bane.... Yaci Alwashin Aurenta tare da daukar fansar CI mishi fuska da tayi a bainan nassi kubiyoni domin jin yanda zata kasance tsakanin zahra da Abdurrahim.