Ummuazamm's Reading List
4 stories
AKIDA LINZAMI  by Ummuazamm
Ummuazamm
  • WpView
    Reads 3,105
  • WpVote
    Votes 310
  • WpPart
    Parts 3
Aƙida kan iya zama linzami akan tafarki na Rayuwar Ɗan Adam Aƙida kan iya zama linzami da zai ja kansa da kansa ?? ( yayi jagora a fagen tafiyar rayuwar Ɗan Adam ) . Ba koyaushe Ɗan Adam yake da zaɓi ba akan aƙidar sa . A hankali aƙida take sanɗar Ɗan Adam har ta shiga ta saje da halayyarsa da kafin ya farga tayi masa rumfar da ba shi da zaɓi wajen irin yanayin da zata iya zo masa da shi . Amma me zai faru a lokacin da aƙidar ta zurfafa har ta kai mai ita ga makancewa daga ganin zuzzurfan ramin da ya mamaye kan tafarkin aƙidar sa ?? Ya kuma gaza wajen riƙo linzamin akiɗarsa maimakon haka sai ya sakar mata linzami har ta kai maƙuryar ƙurewar da ta birkice ta jirkita ta rikiɗe ta koma mummunar akiɗar da ta zama guba sannan kuma annoba acikin al'umma sannan ta jefa mai ita a hallaka mafi munin ji da gani . Anya Salman bai yi fargar daji ba ? Lokacin da ya farga ya fara yunƙurin riƙo linzamin aƙiɗarsa ya dawo da ita bisa kyakkyawan tafarkin da ainahi ya gina akiɗar zuciyar sa a kai , a kuma dai-dai lokacin ne zuciyarsa tayi masa tirjiya ta jaa ta toge sakamakon aƙidarsa da tayi arangama da wata aƙidar da take mabambanciya da ta shi . So kuma yayi tasiri irin nasa ta hanyar sarƙe tsakanin aƙidun biyu da suke kishiyoyin juna ba tare da ya lura da tazarar da ke tsakanin su ba . Sannan a ƙarshe zuciyoyin su suka zaɓi da suyi watsi da tasirin aƙidunsu su rungumi junan su a tsakiyar bigiren da ko cikin shuɗaɗɗun mafarkai irin na baccin tsakiyar hunturu , ɗayan su bai taɓa tsintar kansa a ciki ba sai ga rayuwa ta juya musu aƙida kuma ta musu jagora . Shin wai gaske ne aƙiɗar ka linzamin ka ??? Sahihiyar amsar tana ga Salman tare da Madinah .
MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA) by Ummuazamm
Ummuazamm
  • WpView
    Reads 523,171
  • WpVote
    Votes 42,153
  • WpPart
    Parts 59
MAFARI...komai yana da farko, komai yana da tushe, komai yana da asali, HARGITSIN RAYUWA kan faru cikin ƙanƙanin lokaci. Duniyar daka saba da ita zata iya birkicewa zuwa baƙuwa a gareka cikin ƙanƙanin lokaci. Tafiya mabanbanciya da sauri a cikin kaddara da dai-daito
Mai Tafiya by donutfairy
donutfairy
  • WpView
    Reads 199,130
  • WpVote
    Votes 20,120
  • WpPart
    Parts 29
Labarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeria mu ga yadda za ta kaya! Mai tafiya..wani guzuri ka tanada??????
ABINDA AKE GUDU (Completed) by BatulMamman17
BatulMamman17
  • WpView
    Reads 327,417
  • WpVote
    Votes 20,935
  • WpPart
    Parts 61
Labarin Asmau....labarin ABINDA AKE GUDU.