UmmNafesa's Reading List
24 stories
MENENE ILLA TA? by zm-chubado
zm-chubado
  • WpView
    Reads 764
  • WpVote
    Votes 83
  • WpPart
    Parts 15
"Idan kina ganin hakan shine dai-dai a zuciyarki to kiyi hakan BINTOU. ni kuma nayi alƙawarin cewa bazan taɓa dakatar dake ba, sai dai kafin ki zartar da hukuncin da kike ƙokarin zartarwa ina so kiyi tunani Akan ƴaƴan dake tsakanina dake...." cewar EDRIS MUHAMMAD KANKIA, ya faɗi hakan yana kallon tsakiyar idanun Bintou a Sanyaye "bana buƙatar komai daga gareka shiyasa ma naƙe so ka sauwaƙe min wannan jarababben Auren naka. kai in banda ƙaddara mai zai sa in haɗa zuriya da kai? In dan ƴaƴan dake tsakankna da kai ne, yasa kake tunanin zan janye ƙudirina akan ka, to kaje na yafe duk wata alaƙa ta jini dake tsakanina da ƴaƴan ka har Abadah Edris....!." cewar FATIMAH HAMZA MAI-GORO, ta gaya masa haka cikin maɗaukakin ɓacin Rai kasa cewa komai yayi illa zuba mata rinannun idanunsa da yayi yana kallon Yanda take huci tamkar macijiya, cikin ƙoƙarin son ya shanye ɓacin Ransa Edris ya saki wani gajeran murmushi wanda ke baiyana ƙunar dake ransa,. batayi Aune ba ya juya ya bar mata gurin ba tareda ko waiwayenta ya ƙarayi ba, Don ya riga ya ƙudurtawa kansa cewar ba zai ƙara waiwayarta ba har Abada, kamar yanda take fatan Samu a tareda shi.........
TSAKANINMU by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 2,306
  • WpVote
    Votes 114
  • WpPart
    Parts 1
Su uku suka kulla yarjejeniyar, sirri ne da ya kamata ya tsaya a tsakanin su ukun kawai, ko da ta kama zaren ta ja shi, ta hange shi da tsayin da ta kasa ganin karshen shi, burinta ne mafarin, yarjejeniyar da sirrin duk a tsakiya suke, karshen kuma sai ta dauka cikar burinta ne, shi tayi hasashe, shi ta shiryawa zuciyarta karba, ko a mugun mafarki bata hango burinta zai ci karo da kaddarar da ta dauketa tayi sama da ita, ta girgiza kafin ta tikota da kasa ba, faduwar da tayita akan sirrin da take ta riritawa, data mike kuma sai ya koma sama kafin tayi wani yunkuri ya dawo ya binneta da ranta!
ALKALAMIN KADDARA.  by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 45,563
  • WpVote
    Votes 2,110
  • WpPart
    Parts 14
Karka nuna dan yatsa akan kalar rubutun da Alkalamin kaddara yaima waninka. Baya tsallake kowa, naka a rubuce yake tun kamun samuwarka. Karkace zakai dariya akan kalar shafin rubutun Alkalamin kaddarar wani, a duk minti daya na rayuwarka sabon shafi yake budewa, waya san ko cikin shafukanka akwai rubutun dayafi nashi muni. Karka saki jiki da yawa, komai zai iya canzawa. Zuwa yanzun kowa yasan ban yarda da Happily ever after ba, idan har shi kake buqata, ALKALAMIN KADDARA ba littafin ka bane ba. Yan gidan Tafeeda da Shettima zasu taba rayuwarku kaman yanda suka taba tawa. Bance akwai sauqi a cikin tasu tafiyar ba. Banda tabbas akan abubuwan da zakuci karo dashi in kuka biyoni a wannan tafiyar. Tabbaci daya nake dashi, ba zaku taba dana sani ba IN SHA ALLAH. #AnaTare #VOA #FWA #TeamAK
RAI DA KADDARA by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 77,718
  • WpVote
    Votes 7,816
  • WpPart
    Parts 59
Daada, Ku saka mata Munawwara, ku kira ta da Madina. Watakila albarkacin sunayen biyu rayuwar da bata da zabi a kanta ta zo mata da sauki ko yaya ne. Zan so kaina a karo na biyu, ku fada mata mahaifiyarta ta sota a watanni taran zamanta a cikinta, ko ba zata yarda ba Daada ki fada mata ta yafe mun, ki bata hakuri na yanda zata kare sauran kwanakin ta a duniya tana biyan zunuban mahaifanta. Kuma ku fada mata sunan baban ta Kabiru, yanayin haihuwar ta ba zai canza cewa ita din jinin shi bace ko da bata da gadon shi. Ke ma ki yafe mun, kiyi mun addu'a ko da rayuwa ba zata sake hada fuskokin mu ba. Yelwa.
CUTARWA! by Ayshercool7724
Ayshercool7724
  • WpView
    Reads 57,479
  • WpVote
    Votes 2,437
  • WpPart
    Parts 50
Kowane ɗan Adam, ɗauke yake da littafi, mai tarun shafukan ƙaddara, idan ka karanta fejin yau, sai ka buɗe na gobe zaka san me yake ɗauke da shi. Sai dai ummi na iya cewa, tun da ta buɗi ido, ba ta taɓa cin karo da shafin da buɗe shi yayi mata daɗi ba, sarƙar ƙaddara ke ta janta daga wannan tarago zuwa wancan ko menene dalili?...
H U R I Y Y A by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 18,643
  • WpVote
    Votes 657
  • WpPart
    Parts 16
Wata rayuwa ce zan taɓa ta Hausawa, wani ɓangare na ƙabulan da yara suke fuskanta a gidan iyayensu, tun farko tashi har girma, wani abu ne da nake ta hangowa kuma na daɗe da ƙishin son rubutawa. ••• ••• H U R I Y Y A -Labari ne mai ban tausayi da taɓa zuciya. Story of the Year 2023... Be kind to every human being, because you don't know the whole story and matter what you are facing never give up. You don't know what the future holds...
KWARYA TA BI KWARYA  by Sadnaf
Sadnaf
  • WpView
    Reads 2,861
  • WpVote
    Votes 156
  • WpPart
    Parts 11
A heart touching story of love sacrifice
JANNAH by Humaira3461
Humaira3461
  • WpView
    Reads 6,077
  • WpVote
    Votes 509
  • WpPart
    Parts 25
Kaddara abuce mai nauyi, kuma mai zafin gaske,ayayin da ta kasance mai kyau alokacin take da dad'i a yayinda tazo akan akasin hakan lokacin kakejin duk duniya babu wanda ya kaika fuskantar kalubale, Ku shigo cikin labarin anan ne zakuji LABARIN KADDARARTA.
MIJIN KANWATA(K'ADDARATA) by JamilaUmar315
JamilaUmar315
  • WpView
    Reads 33,992
  • WpVote
    Votes 2,974
  • WpPart
    Parts 30
_*Wata irin KADDARA CE wannan..?Kaddaran data Ratso MIJIN KANWATA cikin Rayuwata..?wanda yake matukar girmamani kamar yadda Kanwata SUNAIRA take girmamani?Meyasa kaddara ta zamo tayi min haka..?meyasa sai ni..?Taya zan iya zama da wanda muke jin nauyin juna muke gogayar shekarun juna..?Tabbas MIJIN KANWATA ne KADDARATA...*_
BAKAR WASIKA by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 25,152
  • WpVote
    Votes 1,093
  • WpPart
    Parts 11
BAƘAR WASIƘA... Mai farin rubutu Ban ce tafiyar mai sauki ba ce. Ban muku alkawarin zallar soyayya ba. Ban ce babu farincikin ba. Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki. Labarin Talba, Rafi'a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal da kuma Aminatu. Labarin BAKAR WASIKA, labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta... Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira! A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi. Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke? Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa? BAKAR WASIKA... JUANURY 2022