Autan-Eloquence
Tarin Ƴan Jaridu ne ke gewaye da Ƴan Sandan da suke a tsaitsaye a bakin katafaren gate na Luxury Hotel ɗin da ke birnin Maiduguri, gaba ɗaya Ƴan Jaridun sun gama hargitsa ilahirin wajen da hayaniyar su ta watsa labaran ji-da-gani kai-tsaye a ƙafafan yaɗa labarai. Daga cikin harabar Hotel ɗin kuwa, Sufeta Hassan ne da Sajen Gambo tare da wasu ma'aikatan Asibiti ke tsaye a jikin motar ɗaukan marasa lafiya ta General Hospital Maiduguri. A gaban su kuma gawarwaki ne guda Uku jere a ƙasa lulluɓe da fararen ƙyallaye, wanda tuni jinin da ke ɓul-ɓula daga jikin gawarwakin ya gama sauya musu launi daga asalin kalar su ta farare.