UmmiLukman's Reading List
95 stories
MATAN?? KO MAZAN??? by MSHAKURworld
MSHAKURworld
  • WpView
    Reads 86,762
  • WpVote
    Votes 2,533
  • WpPart
    Parts 45
Labarine kan matsalolin da ake samu agidajen aure daga bangaren Matan dakuma Mazan. Series ne dazan dinga kawo muku duk ranan ASABAR DA LAHADI
BAKAR TA'ADA  by SurayyaDee91
SurayyaDee91
  • WpView
    Reads 3,272
  • WpVote
    Votes 393
  • WpPart
    Parts 11
Murya Babu amo ta ce "Ai kuwa zan yi dukkan iyawata na kubutar da ke, ba zai yiwu ki zabe ni, ki mutunta ni, ki taho wajena sannan na kasa yi miki adalci ba, sai idan abin ne yafi k'arfin azancina". Tana rufe baki sai ganin Bulkachuwa na yi, ya fito daga cikin kicin dinta da yake falon. Take na tuna dangantakarsa da Baba ta Bulkachuwa. Wani irin tashin hankali ya sake ziyarta ta. Kunya da ki'dima suka rifar mini, na rasa yadda inda zan tsoma raina. Na kalle shi, na ga alamun damuwa a tare da shi, haka da na kalli Babar sai na ga ita ma tana cikin zullumi. Kunyar yadda na zo gabanta ina fa'din bana son dan cikinta ta nemi zautar da ni, domin bansan ya aka yi ba na zabura na tsallake kwanukan abinci da na ruwa na yi waje a guje. Ina jinta ta biyo ni tana fa'din Yabi! Yabi!".
RAYUWA DA GIƁI by BatulMamman17
BatulMamman17
  • WpView
    Reads 110,722
  • WpVote
    Votes 8,385
  • WpPart
    Parts 41
Rashi ba shi kaɗai yake samar da giɓi a rayuwa ba. Wani yana doron ƙasa amma dalilai kan sa wanzuwarsa ta kasa amfanar da makusantansa. Me zai faru da rayuwar ƴaƴan da su ka zaɓi zama da giɓi a gurbin da mai cike shi yake da rai da lafiya? RAYUWA DA GIƁI...
TSANINMU by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 3,654
  • WpVote
    Votes 318
  • WpPart
    Parts 3
Duk abin da mutum zai zama a duniya sai ya bi ta wasu matakala wanda ke manne a jikin tsani, tsanin kan iya zama na katako wanda ruwa da rana ke saurin lalatasu wani tsanin kuma na karfe ne da sai dai yayi Tsa-tsa. Ana samun tsani na azurfa ko lu'ulu'u ko ma zinari wanda hakan bai isa a ki kiran sa da tsani ba, hakan bai ki a bar shi yashe cikin ruwa da rana ba, hakan bai isa a daraja sama fiye da shi ba duk da kuwa in babu shi ba za a isa ga saman ba. Maluma su ne TSANINMU. Duk abin da gobe zai haifar mana dole sai ta sanadinsu. Ku biyo ni mu shiga rayuwar TSANI malam Muhyideen Jibril.
AHUMAGGAH by SURAYYAHMS
SURAYYAHMS
  • WpView
    Reads 671,658
  • WpVote
    Votes 52,611
  • WpPart
    Parts 49
"Never let your best friend become your enemy"...that was my abbus last words before he left the world.Am a perfect girl,with a perfect heart i secrifice alot witout expecting returns.In this world they are two main life directors,the push or pull factors,surely one is good one is bad, both are necessity.BUT my necessity was meeting him,who is he?the royal prince of persia.a bonified brigadier general of USMC. As a wife, sister, or maid that only my destiny will tell.... #Bahiyya Ahmed #khaldun sa'ood #junnut
Inteeesar by Khaleesat_Haiydar
Khaleesat_Haiydar
  • WpView
    Reads 30,067
  • WpVote
    Votes 913
  • WpPart
    Parts 4
#pride #Obsession #Ego #Step mothers #Funny granny #Khaleesat Haiydar #Love #Foolishness #Romance
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* by sameehasusman
sameehasusman
  • WpView
    Reads 81,122
  • WpVote
    Votes 1,018
  • WpPart
    Parts 200
*AMSOSHIN TAMBAYOYINKU* *NA KASA YIN AZUMI SABODA QARAMIN CIKI, GA SHAYARWA, YA ZAN YI?* TAMBAYA:
WATA FUSKA by 68Billygaladanchi
68Billygaladanchi
  • WpView
    Reads 206,213
  • WpVote
    Votes 17,321
  • WpPart
    Parts 50
Sosai take a tsorace, ganin komai take tamkar a mafarki ji takeyi tamkar ma ace bata rayuwa a doron qasar, se zare ido takeyi tana kallon qungurmin dajin datake ciki, gata a d'aure ba hanyar guduwa, tayi iya kacin qoqarin taga ta qwace kanta amma sam abun ya faskara ya kuma tunzura, tunaninta d'aya yanzu idan wani naman daji yazo ya cinyeta ya zatayi kokuma wani mugun aljani gashi ko dankwali babu a kanta, babban tashin hankalinta shine sallar dabatayi ba, tun shekaranjiya da aka gudo da ita rabon datae sallah!!!! zata iya d'aukar kowane hukunci amma banda na hanata sallah!!! yaya zatayi da tulin sallolin dake kanta? batada halin yin koda taimamane sabida a d'aure tamau take to meye mafita?!!!!!!!
UKU BALA'I (Completed) by Kamala_Minna
Kamala_Minna
  • WpView
    Reads 66,951
  • WpVote
    Votes 3,738
  • WpPart
    Parts 77
"kin gama aikin ki don haka ga tukuicin ki". Ya fadi yana sanya hannu cikin aljihunsa yana zaro bandir din yan dubu dubu guda biyu ansa tayi tana mai kau da fuska kamar bata so ba. "Sannan kuma wannan lamarin ya kasance tsakanina da ke in har naji labari mai kama da shigen wannan lamarin kin san Allah sai kin bar filin duniyar nan". Ya karashe fuskarsa a daure kamar bakin hadarin dake kokarin zubda ruwa. Ko a jikin ta bata nuna damuwa da maganganunsa ba illa tsaki da tayi can kasar makoshi ta na balle murfin motar ta fice Khairiyya dake takure bayan mota ta duba da wani irin yanayi na tausayawa tana faman gyaɗa kai kafun ta dubi Alhaji Mati. "batar da sunanka sananne ka aro na banza ka sakawa kan ka akan wani KUDIRI naka na daban...Uhmm ba na ganin wanda ya isa rikakken mutum mara tsoro zai fito da wannan salon na boye sunan sa domin duk wanda yake so ya fado DUNIYAR SHAHARA a wani fanni da sunan sa ya kamata a san shi ko an rufe babin sa ba za taba mantawa dashi ba da abin da ya aikata". Tana gama fadin haka ta buga murfin motar da karfi yan yatsunta biyu ta dagawa Khairiyya wacce a wannan lokacin ta dago da kanta tana dubansu su duka biyun cikin yanayin na rashin inda suka dosa a tsakanin su. "Hajiya Layla" Ya fadi da murmushin mugunta a laɓɓansa kafun ya dora. "...abu daya zai sa na kyale ki a filin duniyar nan shi ne wannan yarinyar da kika bada takomashin taimako har na same ta saboda ita ce hanyar samun arzikina da nake burin cimma wa wannan dalilin zai hanani yi miki komai amma duk da haka ki tsumaye ni ina nan tafe". yatsine fuska tayi kafun ta juya ta fara takawa kan kafafuwanta. Dariya yake yi sosai da sosai har yana buga sitiyarin motar kafun ya tsagaita kamar daukewar ruwan sama fuskar nan tashi ya haɗe ta waje daya kafun yayi wa motar ki ya fizge ta kamar mai kokarin tashi sama.
Zabina Part 2 Complete HausaNovel  by Autan_Mumcy
Autan_Mumcy
  • WpView
    Reads 3,934
  • WpVote
    Votes 61
  • WpPart
    Parts 1
Zabina Part 2 Complete HausaNovel By www.hausanovel.com.ng