nurasgaro's Reading List
2 stories
TAURARONA LITTAFI NA DAYA by nurasgaro
nurasgaro
  • WpView
    Reads 37
  • WpVote
    Votes 1
  • WpPart
    Parts 1
Ameera ta yi ajiyar zuciya gabanta yana dukan uku-uku domin zuciyarta ta fara raya mata abun da Ameer ya zo yi wajenta shi ya sa yake yi mata irin wannan kallon na bankwana wato Abubakar ya saye soyayyarsa kenan. "Allah ya sanya alkairi" Ta ce mishi cikin nuna ƙarfin hali domin kar ya gane halin ruɗu da damuwar da ta shiga. Ameer ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, "abu na biyu Ameera na zo ne muyi bankwana da juna domin bazan iya haɗa neman aure da Abubakar ba kasancewar ya fini komai kamar yadda ya lissafa" Ameera ta girgiza kai cikin nuna takaicin abun da Ameer yake cewa sannan ta ce, "bai fika komai ba Ameer, ko da ya fika to be kai ka a cikin zuciyata ba domin ni kai na ke so kuma iyayena sun bani damar na kawo musu wanda nake so kuma kai zan ce musu" "bani ki ke so ba Ameera" Ameer ya ce mata ta juya da sauri ta kalleshi ya gyaɗa mata kai sannan ya ci gaba da cewa, "da ace ni ki ke so da ba wanda zai iya rabani da ke sai Allah. Na fahimci bani Ameer ɗin ki ke nema ba akasi aka samu wani ya baki lambata amman maganar gaskiya ni ba Marubuci ba ne ni ɗan kasuwa ne shagona yana kasuwar kwari shadda da atamfofin mata nake sayarwa. sunana na gaskiya Usman ana kirana da suna Ameer ne saboda sunan kakana aka samun dan haka Ameer wakilin sunana ne idan kuma kina sona a haka to zan aureki Ameera domin bana zaton yanzu a duniya akwai wanda zai ganki ya ce baya sonki sai dai kuma idan ya san baze samu ba musamman idan ya ji cewa matashin sojannan ne abokin takararshi to dole ya ja da baya..."
WACECE KHADIJAH LITTAFI NA BIYU by nurasgaro
nurasgaro
  • WpView
    Reads 131
  • WpVote
    Votes 7
  • WpPart
    Parts 1
Wacece Khadijah Littafine na soyayya da aka ginashi akan fahimtar juna da yarda a tsakanin ma'aurata, ba kaɗai so Ma'aurata ke buƙata domin samun zaman lafiya mai ɗorewaba, yarda da kawar da zargi yafi so muhimmanci... Naku a ko da yaushe Nura Isa S Garo