user75101877's Reading List
60 stories
AUREN FARI.... by meenaslimzy
AUREN FARI....
meenaslimzy
  • Reads 39,073
  • Votes 2,891
  • Parts 40
wayace miki ana bawa namiji dama?babu abinda yake canja namiji sai ikon allah idan kince zaki iya canja Abdallah to kin yaudari kanki mazaasu hali irin na Abdallah wadanda basu da lokacin matansu saina aikinsu daban suke basa taba canjawa don haka ki saki jikinki a matsayina na yar uwarki aminiyarki inada hanyar da zakibi kisamu farin ciki ba dole saida soyayyar abdallah ba domin idan kikace zaki koyi tarairayar miji tou kin sa kanki a hanyar wahala baa taba tarairayar miji...namiji baayi masa gwaninta.....SABON SALO MAI CIKE SA DARUSSA MAI DAUKE DA TSANTSAR CIN AMANA....MAI DAUKE DA SALO NA SOYAYYA
FATU A BIRNI (Complete) by suwaibamuhammad36
FATU A BIRNI (Complete)
suwaibamuhammad36
  • Reads 65,645
  • Votes 2,254
  • Parts 18
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa. Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa? Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan. Fatima- Budurwar Sultan.
DR SAMEER AMEER!!!!!(COMPLETED✅) by missxoxo00
DR SAMEER AMEER!!!!!(COMPLETED✅)
missxoxo00
  • Reads 12,575
  • Votes 483
  • Parts 9
Labarin sarqaqiyar rayuwa...💫💕Na NAFI ANKA DA MISS XOXO (2016)
Dr. Salman (ON HOLD) by Umm_meenarll
Dr. Salman (ON HOLD)
Umm_meenarll
  • Reads 26,471
  • Votes 1,537
  • Parts 20
Dr. Salman labari ne mai kunshe da yaudara, kiyayya, sonkai, tausayi dakuma sakaci da zafin kishi, labari ne irin Wanda baku ta ba jin irin sa ba, dan aka ku biyo ni da sanin ya zata Kaya cikin wannan kiyattacen littafi.
SHU'UMIN NAMIJI !!    (completed) by fatymasardauna
SHU'UMIN NAMIJI !! (completed)
fatymasardauna
  • Reads 407,573
  • Votes 24,858
  • Parts 75
Labarin Zaid da Zahrah...."Idan har yaudara zata zamemaka abun ado mai zaka amfana dashi acikin rayuwarka ? Miye ribar aikata zina da fasiƙanci ? Natsaneka Zaid ! Natsaneka !! Bana fatan Allah yasake haɗa fuskata da taka fuskar har gaban abada".....
RUWAIDA ✔️ by rahma_Inuwa
RUWAIDA ✔️
rahma_Inuwa
  • Reads 222,145
  • Votes 30,624
  • Parts 54
Poor Ruwaida Mahmoud had to get married to her friend's brother, Turaad, a rich sophisticated Doctor not knowing she had signed a contract to save her life! _______________________________ Her eyes tinged with tears the moment she raised her head to look at him. All the while he spent talking to her, she had her head down, staring endlessly at her hands. His words filled with a sincerity which he had shown broke her to pieces. The most she could do was smile at him. Even if she wanted to, her words wouldn't be able to make sense. She had so much to say, so much to let out, but then, her vocals refused to let her. He held both her hands and smiled back, his other hand on the small hospital bed she had laid. "You scared me Waida, I almost passed out seeing you being trolled back into the ICU you know," He said, and laughed, ducking his head low, as the way he had acted replayed in his memory. She also chortled silently, not minding the tears that refused to stop, moments like this, always left her emotional. "I did? But I'm fine now ain't I," she asked and he placed a hand on his forehead, his overdramatic wife mode had just been turned on. "Yes you're, but please don't ever do that again," he said with a stern face. "Promise me," With an absentminded look in her eyes, she nodded and gave a quick reply. "Yes Muhammad, I promise," Love_ Silentwriter ☕️
NIDA AMEENATU. {Completed} by Real_autarhajiya
NIDA AMEENATU. {Completed}
Real_autarhajiya
  • Reads 37,501
  • Votes 1,977
  • Parts 17
Its all about DESTINY.
MATAR HAIDAR by MSIndabawa
MATAR HAIDAR
MSIndabawa
  • Reads 41,020
  • Votes 1,885
  • Parts 91
*Assalamu alaikum warahmatullah!* The authur of Mijin Ummu nah, Wa nake so?, Ni da Yaa Fauwaz and Ni da Aminiyya ta (Samira da Ja'adah) bounces back with another heart touching love story named.... MATAR HAIDAR MATAR HAIDAR labari ne da ya kunshi rayuwar wasu masoya guda biyu wanda dukkan iyaye da yan uwa sun san wannan soyayyar, sai dai me? MARYAM ta yi rashin HAIDAR a daidai lokacin da zuciyarta ke tsananin kaunarshi, a daidai lokacin da tafi kaunar sa, a dai dai lokacin da take zaton ba abinda zai raba su, a lokacin da take tunanin burin ta ya gama cika a rayuwar ta gaba daya. Daga nan rayuwar ta ta fada kunci da tashin hankali, wanda ta dalili haka ta rasa maganar ta bama wannan ba wata daya da rashin HAIDAR aka gano MARYAM dauke da cikin a dalilin cikin mahaifin ta ya kore ta daga gida wanda barin ta gida ke da wuya ta manta wacece ita, ta manta kowa nata. #To wai wannan cikin wanene? #Me ya faru da HAIDAR (Mutuwa yayi ko kuwa)? #Me zai faru da rayuwar MARYAM?
KASHE FITILA by BatulMamman17
KASHE FITILA
BatulMamman17
  • Reads 243,257
  • Votes 18,194
  • Parts 53
Iyaye musamman mata sukan sadaukar da dukkan farincikinsu domin kyautata rayuwar 'ya'yansu. Haka ce ta faru ga Maamu har zuwa lokacin da Allah Ya azurta mata tilon danta Awaisu. A daidai lokacin da take tunanin kyautatawa wadanda suka wahalta musu a baya sai Gimbiya matar dan nata ta murda kambun da ko iyayenta basu santa dashi ba.... Ga uwa, ga da sannan ga suruka.
AL'ADUN WASU (Complete) by BatulMamman17
AL'ADUN WASU (Complete)
BatulMamman17
  • Reads 217,889
  • Votes 16,017
  • Parts 45
Bahaushen mutum yana da kyawawan dabi'u wadanda addinin Musulunci da al'adunmu su ka koyar damu. Sai dai zamani yazo da wani salo, mun wayi gari bamu da abin koyi da tinkaho sai AL'ADUN WASU. Shin hakan hanya ce mai bullewa???