Ajrab29's Reading List
188 stories
ASEELA COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 22,456
  • WpVote
    Votes 1,704
  • WpPart
    Parts 52
Ƙwarangwal ɗin suna tafe wani irin ruwa mai yauƙi na fita daga gaɓɓan jikinsu tamkar waɗanda aka kunna fanfo ajikinsu, daga kowanne ɓangaren hallita akwai shugabansu wanda shi ne yake kan gaba su kuma suna biye dashi abaya, hannu kowanne shugaba ɗauke yake da wani farin ƙyale da jikinsa yake da ɗishi-dishin jini, ahankali ta fara ɗaga ƙafarta tana ƙoƙarin ja da baya da niyyar guduwa sai dai nauyin jikinta shi ya hana ta gudu har suka ƙaraso inda take, mararta ce ta ɗan karta mata bayanta ya riƙe sannu ahankali ta tsugunna ta duƙa agurin wani irin azababben ciwo na cinta, jeruwa suka yi sahu-sahu sannan suka fara zagaye ta suna faɗin wasu kalmomi da sam bata fahimtar mai suke faɗa, " YAMDUMISA! YAMDUMISA!! YAMDUMISA BISRATIK KUZAR!!!, KIMBASA MIN! KIMBASA MIN!! KIMBASA MIN MAR FAZKINBAT!!! " ( BARKA! BARKA!! BARKA DAI SHUGABA!!!, DAWOWARKU NASARA CE! DAWOWARKU NASARA CE!! DAWOWARKU NASARA CE TARE DA FANSA!!! ) haka suka dinga zagayeta suna maimaita kalmomin bakinsu shugaban ɓangarori biyun masu ɗauke da farin ƙyallen nan suna zazzaga mata wannan kyalen akanta, ciwon da take ji ƙara tsananta yake banda ihu ba abinda takeyi sai kiran sunan KABEER take tana maimaitawa, idan abun ya kuma tsananta ta kuma kiran Kabeer ko Habeebee amma ko gezau basu fasa wannan surutan nasu ba kuma basu fasa zagayeta ba suna yarfa mata wannan farin ƙyallen ba, wani lokacin ma wannan ruwan mai yauƙi na ɗiga ajikinta, ita bata ma san suna yi ba saboda azabar ciwo fatanta kabeer ya kawo mata ɗauki. Ta ɗan ɗauki lokaci ahaka kamar minti talatin ahaka sai ji sukayi kukan jariri alokacin ta galabaita sosai amma ahaka take yunƙurin ɗaukar abinda ta haifa dan neman tsira daga garesu, sai dai kafin tayi wani yunƙuri tuni shugaban ƙwarangwal ɗin nan ya kai hannu yayin da shima shugaban mai mummunar hallitar shima ya kai hannunsa, atare suka suka ɗago jaririyar kowanne ya riƙe hannunta ɗaya yana faɗin, " KAGARSIN BIDA, KAGARSIN BIDA LANBISMA GIRUS " ( KA
MADUBIN SIHIRI by MSKutama87
MSKutama87
  • WpView
    Reads 4,014
  • WpVote
    Votes 127
  • WpPart
    Parts 2
labari ne akan wani madubin sihiri Wanda wannan madubi mallakar Sarkin Bakaken aljanu ne na farko lokacin da aka sana'anta madubin amma sai aka samu wani hatsabibin boka Wanda ya kware a harkar tsafi da tsatsuba ya tura aljanunsa suka kwato daga hannun sarkin bakaken aljanun sannan ya soma mulkar gabadaya halittun duniya har sarkin bakaken aljanun sai da yayi masa mubaya'a sanoda babu yanda ya iya dashi madubin nan yayi yawo a hannun masarautu daban daban daga karshe aka samu wani shugaban sarakunan musulmai ya raba shi izuwa gida bakwai sannan yasa kowane a cikin akwatin bakin karfe yasa aka kulle da makullin muftahul zarmal Wanda wannan makulli kafin kasame shi sai aka keta dajika guda goma sha biyu mafiya hadari a duniya suka kai akwatu ta farko izuwa Bahur akhlas teku mafi girma a duniya suka kulle inda sarkin aljanun ruwa ke gadinta akwatu ta biyu suka kaita izuwa bangon duniya na gabas akwatu ta uku suka kaita izuwa bangon duniya na yamma ta hudu suka kaita izuwa bangon duniya na kudu ta biyar ka kaita izuwa bangon duniya na arewa ta shida suka rufeta adaji na sha daya India kubar take ta bakwai suka rufeta a daji na sha biyu
💖💖💖💖💖💖  *AUREN JARI* 💖💖💖💖💖💖   by fareedathusainmsheli
fareedathusainmsheli
  • WpView
    Reads 2,143
  • WpVote
    Votes 58
  • WpPart
    Parts 10
Labarine wanda yake fadakar da iyaye akan illan auren jari duba ga yanda yarinyar cikin labarin ta kasance kamilalliya wacce ta samu tarbiyya daga iyaye na kwarai amma daga qarshe bayan sun aurar da ita ga wanda bataso duk rayuwarta ya canza ta yanda shaidan ya ribaci rayuwarta. Haka zalika shima ya kasance a bangaren masoyin nata wacce aka aura mishi wacce bayaso qarshe yashiga mummunan yanayi wanda har takai ya xamto abin kwatance acikin sa'annin shi,ga gorin da kowa yakeyi mishi akan zuciyar shi ta mutu ne shiyasanya ya auri wacce zata ja ragamar rayywar shi.
CAPTAIN SADIQ  by SalmaMasudNadabo
SalmaMasudNadabo
  • WpView
    Reads 179,136
  • WpVote
    Votes 7,810
  • WpPart
    Parts 54
d'an tsokacin labarin CAPTAIN SADIQ ya kunshi rayuwar soja ne mai zafin zuciya, d'aurewa rashin fara'a tun bayan lokacin da Allah yayiwa matarsa rasuwa, bayan ta haifa masa baby girl wadda taci suna mahaifiyarsa wacce Allah ya d'aura masa son ta, Hakan yasa duk mai aikin da aka kawo domin kula da yar tasa sukan gudu ko ya koresu, saboda rashin gamsuwa da aikin nasu, ko saboda cin kashin da suke fuskanta a wajan sa, hakan duk yanada nasaba ne da tun bayan rasuwar matarsa KAUSAR ya rasa walwala, har mahaifiyar sa ta fara gajiya da irin halin nasa, kwatsam sai ga Allah yasa mahaifiyar sa ta samo mai aiki FATUHA wadda ta adabi mutanan kauyan su da rashin jinta, haka yasa k'anwar mahaifita tahowa da ita birni aikatau gidan su CAPTAIN, ko mutanan kauyan sun huta da halin ta, ya kuke tunanni masu karatu? shin FATUHA zata d'au wulak'ancin CAPTAIN SADIQ koka zata rama tunda dama bata ji ko a kauyan su RANO mu kaftan💃
'YAR HUTU (LABARIN KAUSAR DA BINTA) Editing by Ishamoha
Ishamoha
  • WpView
    Reads 296,649
  • WpVote
    Votes 23,595
  • WpPart
    Parts 74
Ta taso a gidan hutu, gidan da ko tsinsiya bata dauka tsabar hutu, soyayya takeyi mai tsafta da masoyin ta kuma sanyin idaniyarta wanda da za'a bude kirjin ta se anyi mamakin irin son da take mishi amma sedai kash HUTU ya sangartar da ita ya kuma hanata kula da sanyin idaniyarta yanda ya kamata, shin wannan soyayya zata dore? Bakar wahalan da takesha ba karami bane a hannun matar uba, tsabar tsana da rashin son ganin er baiwar Allahn da ko shekara sha hudu bata karasa ba zata turata birni kuruwanci bayan tanada masaniyar cewar mafiyarta ta tsine mata duk ranar da ta bawa wanda ba maharraminta ba jikinta, shin tazayi abinda aka tura yi kokuwa ?
farouk Ko haidar  by 13deeja
13deeja
  • WpView
    Reads 22,937
  • WpVote
    Votes 1,429
  • WpPart
    Parts 48
a heart touch story dat iz talking about identical twins
Journey of Prophet Muhammad by Jaseema_yasmin
Jaseema_yasmin
  • WpView
    Reads 20
  • WpVote
    Votes 3
  • WpPart
    Parts 4
This is an in debt view of the life of our Prophet Muhammad [PBUH]. this book will be free of all wrong information with only authentic incidents. Hope you will find it useful !!!!
SOORAJ !!! (completed) by fatymasardauna
fatymasardauna
  • WpView
    Reads 906,261
  • WpVote
    Votes 71,683
  • WpPart
    Parts 59
Zanen ƙaddaransa yana cikin zuciyarta, kamar yanda zanen nata ƙaddan ke cikin tasa zuciyar. Idan zuciyoyi suka haɗe waje guda akan samu wata irin zazzafan ƙauna. Ako da yaushe jinsa yake kamar wani baƙon halitta, RAUNI DAMUWA sune abun da sukayi tasiri wajen cika rayuwarsa, yasani kowani bawa da irin tasa ƙaddaran Amma shitasa Ƙaddaran takasance me girma ne agareshi.... *** hearttouching and destiny!!!
DUNIYA MAKARANTA by sadiyah2
sadiyah2
  • WpView
    Reads 11,596
  • WpVote
    Votes 589
  • WpPart
    Parts 7
labarin rayuwa da abubuwan data kunsa na farin ciki,bakin ciki,samu,rashi,cin amana, da rikon amana
TARKON AURE,,,!!! by jiddanberry
jiddanberry
  • WpView
    Reads 3,667
  • WpVote
    Votes 129
  • WpPart
    Parts 1
TARKON AURE...-1 Cikin sanda Jamila ta ke tafiya a soron gidan, rike da takalminta. Sannu a hankali kuma tana wuwwurga idanunta a zagayen gurin. Za ta shige kenan cikin gidan ba zato ba tsammani ta ji an riko mayafinta. Gabanta ya yi wani irin yankewa ya fadi. Ta kasa juyowa bare ta yi wani kwakkwaran motsi illa sauke numfashi da ta ke yi a jigace. Birkito da ita ya yi suka fuskanci juna sosai. "A tunaninki za ki iya yaudara ta Jamila? A tunaninki zan sha wahalar kaunarki a banza?" Ya girgiza kai, "Ba zan iya ba! Ba zan iya wasa da wannan damar ba, domin ni ma Dan Adam ne da yake da jini tare da tsoka. Ban da haka tanadin da muka jima muna yi wa yaranmu ba zai tashi a wofi ba!" Jamila ta kasa rike kukan da ya taho mata, duk da ba ta ba shi damar fitar da sauti sosai ba, amma tuni hawaye ya wanke kundukukin fuskarta. "Ka yafe min Jamilu, ka yafe min... Ka yi hakuri mu karbi wannan nannauyar kaddarar. Jamilu ya dinga irgiza kai har ta rufe baki, sannan ya ce, "Na ji... Na ji... Yanzu ya ki ke so a yi?" Ta yi shiru tana sunkuyar da kanta kasa. "Kina nufin na rabu da ke, na daina sonki? Na cire ki a matsayin da na ba ki na zamowa uwar 'ya'yana? Uhum Jamila kenan, kin san Allah daya kenan ko? To wallahi ba zan iya hakura da ke ba, don haka ya kamata ki sani idan ma kin manta ni Jamilu SadeeQ M ba irin wadannan ragwayen mazan nan ba ne da ake kwace soyayya a hannunsu ta ruwan sanyi ba". Ya juya ya koma cikin dakinsa, ya barta tana share hawaye. Ta jima a gurin, yana daga dakin yana jin sautin shesshekar kukanta, wani irin tausayinta yake ji har zuciyarsa, amma ba shi da yadda zai yi, dole ya zage damtse don mallakar makullin farin cikin rayuwarsa. Motsin da ta jiyo daga cikin gidan ya sa ta saurin shanye sautin kukan nata sannan ta fara kokarin saisaita nutsuwarta. "Ah Jamila? Ai gidanku zan je". Amina kanwar Jamilun ta fada bayan ta shigo soron ta ga Jamilar.