Labarin wasu mata guda uku mabanbanta asali da kaddara ta hada su a yayin da suka dauki aniyar yiwa talauci gudun fanfalaki. Sai suka fada karuwanci..duniya ta zo musu a tafin hannu har suke zaton tafiyar ta kare. Ku biyo su tsakanin Niger da Nigeria mu ga yadda za ta kaya!
Mai tafiya..wani guzuri ka tanada??????
Rashi ba shi kaɗai yake samar da giɓi a rayuwa ba. Wani yana doron ƙasa amma dalilai kan sa wanzuwarsa ta kasa amfanar da makusantansa. Me zai faru da rayuwar ƴaƴan da su ka zaɓi zama da giɓi a gurbin da mai cike shi yake da rai da lafiya? RAYUWA DA GIƁI...