KhadeejaCandy
- Reads 5,476
- Votes 209
- Parts 28
Love doesn't need words to be real. Idan kalmomi suka kasa, zuciya ce ke magana. idan murya ta yi rauni, kallo daya kan iya fassara duk wani abu da rai ke ji.
He fell in love with her silence.
She fell in love with the way he saw her heart, not her voice.
Ba kowace soyayya ke bukatar baki ba. Wasu zukata na tarayya da juna ne ta hanyar sadarwa, wasu kuma hawaye ne ke zama harshensu.
BATULA... Ta taso da ƙalubalen da ya sa mutane da dama suka raina ƙarfin da ke tattare da ita. Kasancewarta kurma, kuma huntuwa.
JAWAD... Ƙwararren mai nazartar harshe kuma gwanin zane a fannin Automotive Design. Mutum ne mai basira, amma zuciyarsa na ɗauke da sirrin da ba kowa ya san da shi ba.
TURAKI... Masanin tattalin arziki mai hikima.
Da akwai wani boyayyen JARUMIN da ba baƙo ba ne a gare ku, sai dai tabbas rawarsa za ta ba ku da mamaki.
Shin ƙaddara za ta haɗa waɗanda zuciya ta zaɓa? Ko kuwa rayuwa za ta tabbatar da cewa ba kowace soyayya ce ake kaiwa ƙarshenta ba?
GUMBAR DUTSE labari ne mai cike da tausayi, sirrika, ƙalubale, darussa, da tsantsar soyayya mai jiƙa rai ta bar zuciya da tunanin ko wane shafi.
Hausawa suka ce: "MAZA GUMBAR DUTSE ." Amma wa yake cancantar wannan suna? Amsar tana cikin wannan tafiya....