Mariyamalamie's Reading List
187 stories
JUMANATU by rashmarrka
rashmarrka
  • WpView
    Reads 3,190
  • WpVote
    Votes 129
  • WpPart
    Parts 13
love an romantic story
🎀BAFFAH'AM🎀  by Aishadaleel2
Aishadaleel2
  • WpView
    Reads 105,003
  • WpVote
    Votes 9,702
  • WpPart
    Parts 52
Labarine daya k'unsa abubuwan rayuwa yanayin yadda Abeedah ta sha gwawarmayar rayuwa.Ta sha alwashin cewa muddin tana raye k'annenta baza su ta6a shan wahalan data sha lokacinda take yariny'a.Ta fara soyayyah da lecturer d'in makarantar su wanda har yakaisu ga son yin aure,in da bata san cewa Sir Salman mazinaci bane.Yana fasa auren ta ya aura K'awarta Suhailat wacce tajima da fad'awa soyayyah da malamin nasu SIR SALMAN. Ba suda Asali wannan shine musabbabin wanzuwar Zafin rai da Abeedah take da shi.Taci burin dawoda martabar iyayanta dan mutanen duniya su daina zargin cewa iyayenta zaman dadiro suke yi. Ta 6idda kamanninta ta dawo tamkar iny'amura inda ta koma garin adamawa wajen kakanta mahaifin uwar ta dan dawoda Asalinsu.Taje gidan a sigar y'ar aiki,in da take kula da duk wani motsin en gidan.nan tagane cewa kowa ha'intar kakanta yake cikiko harda matar kakanta.wacce har qungiya take dashi wanda akeyi duk mako dan kawai a cuta kakanta.Hajia nenne tayi ma Abeedah tayin shiga wannan k'ungiyar intaki kuma zatasa a kasheta. Mutum d'ayane tak ta gaza ganewa shin yana ha'intar kakan nata ko akasin haka?.Waye shi wanan mutumin da take gani jefi jefi a gidan wanda ta lura kowani mahaluki a cikin gidan na tsoronsa?............. Ku biyoni sannu a hankali zan warware maku zare da abawa.Shin Abeedah zata amsa tayin kungiyar da Hajia Nenne ta mata?shin waye wannan mutumin da batasan ko ha'intar kakanta yake ko a kasin hakan?shin zata iya dawo da mahaifiyarta cikin ahalinta?any'a zata iya cika wannan burin data d'aukar ma mahaifiyarta kuwa? Kubini a sannu zaku sha labr
KALLABI..! A tsakanin Rawuna... by Mai_Dambu
Mai_Dambu
  • WpView
    Reads 47,343
  • WpVote
    Votes 9,909
  • WpPart
    Parts 78
The gap between Love and Hate is not the same as the gap between Death and Life ... But to be killed or to win is one thing ... you are nothing .. in terms of Drawing Fate .. To die or not to live must be shared on two things ... Love and Destiny ... do not blame the pen of destiny Karka kalubanci zanen ƙaddara!!!
HISNUL MUSLIM  by Oumzaynab
Oumzaynab
  • WpView
    Reads 16,804
  • WpVote
    Votes 426
  • WpPart
    Parts 85
Littafin Hisnul Muslim, Addi'o'i da suka dace da Sunnar Annabi. FALALAR ZIKIRI Allah Madaukakin Sarki ya ce: Fazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni. Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152]. Ya'ayyuhallazina Amanuzkurullaha Zikran Kathiran. Ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa". (Ahzab aya ta 41). Wazzakirinallaha Kathiyran Wazzakirati A'addanlahu Lahum magfiratan Wa'ajran Aziyman. Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma". [Ahzab, aya ta 35] Wazkurrabbaka Fiy Nafsika Tadarru'an Wakhiyfatan waduwanaljahri Minal kawli Bil'guduwi Wal'asali Walatakun Minalgafiliyna. Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kankan da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (saka-tsaki) tsakanin asirtawa, da bayyanawa, da safe da marece, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu". [A'araf, aya ta 205]. Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne". (Duba Sahihul Bukhari tare da Sharhinsa Fat'hul Bari (11/208). Muslim ya rawaito shi da lafazin; 'Misalin gida da ake ambaton Allah a cikinsa, da wanda ba a ambaton Allah a cikinsa kamar misalin rayayye ne da matacce". (1/539).) Kuma ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Srkin da yake mallakar ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku daga ciyar da zinariya da azurfa kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Madaukaki". (Tirmizi (5/459), da Ibn Majah (2/1245). Duba Sahih Ibn Majah (2/316). Da Sahihul Tirmizi (3/139).)
DUBU JIKAR MAI CARBI by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 9,107
  • WpVote
    Votes 276
  • WpPart
    Parts 14
Da sauri Yaya babba ta matsa baya tana zaro ido ta ce, "Dubu me nake gani kamar aski akanki." Dubu ta rushe da kuka ta ce, "Inno wallahi aski ya mini kuma wallahi ɗan iska ne." Cak Yaya Babba ta tana ƙarewa Dubu kallo sannan ta ce, "Dubu je ki can mu gani." Dubu ta tashi tana ƙobare ƙafafuwa saboda irin gwale-gwalen da ta sha. Ba su yi aune ba sai ga ni suka yi Yaya babba ta faɗa ɗaki ta rushe da kuka. Da sauri suka bi bayanta saboda kusan kowa bai ji daɗin abin da Aseem ya yi ba musamman Mahaifinsa, faɗa yake yi masa sosai sannan suka shiga ɗakin. Yaya babba kallonsu ta yi fuska a murtuke ta ce, "Garba ka tara mini ƴan uwanka saboda wannan ba maganar tsaye ba ce. Kuma idan har Aseem ya farke mini Dubu na rantse da Allah ba ita kaɗai ya yi wa illa ba, ya fi kowa shiga uku domin babu makarin maganin ƴan shafi mu lerar da za a bashi. Kai ni wallahi ban lamince ba ke Nafisa ke ce uwarsa wuce ki je ji bincike shi tas, don wallahi Idi ɗan wanzan ya mutu babu wani magani da zai karya laƙanin aikin, saboda aikin har da haɗin ƴan shafi mu lera." Tana gama maganar ta fisgo Dubu tana shafa mata suɗaɗɗen kanta ta ci gaba da cewa, "Ka ga yanda Kan Dubu ya sulle kamar bayan sulba. To kwarankatsa dubu idan har ka farketa kaima haka wurin zai shafe kamar bayan silba." Kallon-kallon aka fara yi da juna, jikin Hajiya Nafisa ya yi sanyi dukda ta san a tarbiyyar da suka bawa Aseem ba zai taɓa yi wa Dubu fyaɗe ba. Amma shaidar ɗan yau bata da tabbas, domin ɗa ne ka haifshe baka haifi halinsa ba. Babban abin da ya fi ɗaga hankalinta da ta ji an ce Aseem ɗin ta ya koma kamar bayan silba. Ita da take yi masa tanadin Yusra ƴar aminiyarta ya aura.
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 2,221
  • WpVote
    Votes 63
  • WpPart
    Parts 10
Kuka haɗe da dariya ne suke ta shi a cikin dajin, zuwa can ta hango inuwar wata hallita na tunkaro ta, matsananciyar guguwa ce ke tashi bishiyoyi na kaɗawa da ƙarfa yanda kasan za su jijjigo daga jikin jijiyoyinsu. Cikin wani irin gwamamman yare ta riski muryar inuwar tana cewa, "Sai kin halaka ke da abin da yake cikinki, kin zama halakakkiya keda tsiron da ke cikinki." Ba ta yi aune ba ta fara jin abu na bin ƙafarta zuu! A daidai lokacin da ta ji wani irin nishi ya taso mata. Durƙushewa ta yi a wurin tana murƙususu, nan take wani irin kukan Jarirai mai haɗe da kukan Jaki ya fara karaɗe lungu da saƙon da ke cikin dajin tamkar zai tsage gida biyu. Sannu a hankali Jarirai suka fara rarrafowa suna zageta kamar ana zagaye wainar gero. Duk da halin da take ciki bai hanata yunƙurin tashi domin tseratar da rayuwarta ba, amma ina! Haihuwa ta tunkarota gadan-gadan nan take jaririn ya faɗo. Sannu a hankali ya rinƙa bin duk wurin da jini ya zuba yana lasa shi da sauran 'yan uwansa Jarirai, tamkar waɗanɗa suke da'irar ƙungiyar asiri. Raihan da ke durƙushe da sauri ta zabura kamar wacce aka ɗanawa ruwan dalma, tana yunƙurin tashi nan take mabiyiya ta faɗo. Kamar yanda Kura take ƙishirwar nama haka suka afkawa Mabiyyar kafin wani lokaci tuni suka gama da ita.
WANDA BAI JI BARI BA.... by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 3,976
  • WpVote
    Votes 275
  • WpPart
    Parts 22
Iska ce ta fara kaɗawa ahankali ta fara hango waɗansu irin manyan ƙwari masu kama a fasalin maguna sai dai kowanne su maƙale yake da fukafuki a gadon bayansa, sautin tafiyar Dokin ce ta ƙara kusantota hakan ne yasa ta maida kallonta ga inda tafi jin sautin na matsowa. Kamar yanda ya bayyanar mata a karan farko wannan karan ma wata zabgegiyar Abaya ta hango baƙa, tsawon abayar ya kece tsawon bishiyoyin dake cikin dokar Dajin sai da ta ɗaga kanta sama sosai sannan ta hango dai-dai kansa sai dai kansa ne amma babu alamar fuska ajikinsa. Ƙarasowa yayi gabanta ya tsugunna cikin murya mara daɗin sauraro ya fara magana, " Bingirsima baguar kinbasu wakisfatminar, kisasu biragu kilbasu tattarakimbas wajihagar, farafafus bintigad gurmanas YUSRA? harbaskila mindadu bar washbasbismas shizas kima bu warsa? " ( A karo na biyu ina ƙara miki barka da zuwa cikin daularmu nida ahalina, da sannu zan gabatar da ke ga sauran iyalaina domin kusan juna keda su ina fatan kina jina YUSRA? Ga ƴaƴana nan sun fara zuwa gaisheki ina fatan zaki basu kulawa ? ) Wannan zabgegen Aljanin ya ƙarasa maganar yana nuna mata waɗannan hallittun masu fasalin Maguna da fukafukai. Yusra da tuni hawaye yake wankewa fuska ta ƙara durƙushewa ƙasa cikin sigar magiya tana faɗin, " Ka dubi girman Allah da Annabi ba dan ni ba, ba dan halina ba kayi haƙuri ka maidani cikin mutane dan Allah, wallahi bazan iya rayuwa cikinku ba na tuba dan Allah kamun rai " Miƙewa tsaye yayi sannan yayi taku biyu zuwa uku sannan ya waigo ya ce mata, " Hargigas markusa bayas tinga " ( Tashi tsaye kije jikin waccen bishiyar kukar ) Yusra har tuntuɓe take da sauri ta miƙe tsaye saura kaɗan Abayar jikinta ta kayar da ita, jikin bishiyar taje ta tsaya tana sauraron abinda zai sake faɗa, batayi aune ba ta tsinkayi muryarsa yana faɗin. " YUSRA Lilbas faragaras binsafa walgibas zalzulfat kinari " ( YUSRA kalli Abayar jikinki da kyau, idan har kin iya cireta daga jikinki
AZIMA DA AZIZA (🐍MACIZAI NE🐍) by fateemah0
fateemah0
  • WpView
    Reads 28,103
  • WpVote
    Votes 398
  • WpPart
    Parts 12
the story of two snakes sister's, don't miss this story, just cost #100naira only now b4 i ending the story, if i done u would cost #300naira b4 u get the full of the story contact me (09131778646 M AHLAN). vote comments and follow me.tnk u dear fans muhhhh
AMRIYA (Hatsabibiyar Aljana) by Al_Ashtar
Al_Ashtar
  • WpView
    Reads 32,889
  • WpVote
    Votes 1,362
  • WpPart
    Parts 51
Labarin wata hatsabibiya kuma fitinanniyar aljana da ta yi bayyanar bazata ga wata budurwa Zahara cikin wani irin salo na almara. Zahara tayi arba da Amriya cikin suffan mutane, har ta kwatanta mata gidansu, kuma zahara ta tafi gidan inda ta iske labarin da ta kira da zanen ƙaddara. Mahaifiyar Amriya ce ke sanar da ita, ita fa ƴarta yau shekarunta huɗu da rasuwa bisa haɗari, Zahara ta tsinci kanta cikin wani irin yanayi na ban mamaki. Ita data haɗu da yarinya a yau sukayi hira, harma ta manta da gyalenta, yanzu gashi ta zo gidansu ana shaida mata ta yi shekaru huɗu da rasuwa. Ku biyo mu domin jin yaya zata ƙarƙare cikin wannan ƙayataccen labari.
MIN QALB by Mamuhgee
Mamuhgee
  • WpView
    Reads 20,430
  • WpVote
    Votes 680
  • WpPart
    Parts 7
Labarin daya qunshi juyin rayuwa tareda soyayya me sanyi.