hajjouba's Reading List
98 stories
WANI GARI by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 14,202
  • WpVote
    Votes 605
  • WpPart
    Parts 16
A wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yayi mata zane a garin da bata da kowa ciki kuwa har da masu jin yarenta! Garin da babu masu cin irin abincinta babu ma su kalar addininta balle kuma al'adar da ta ginu a kai! Ta fallasa wani sirri da aka dade da binnewa shekaru ashirin da bakwai a baya, ta yi nasarar sauya rayuwar Maleek. Hakika wani mafarkin baya nufin cikar burin mai shi, wani burin kuma yana tabbatuwa ne tun kamin zuwa mafarki. Ya Ameer zai ji idan ya farka daga dogon bachin da ya dauke shi mafarkin shekarun da babu wanzuwarsu a rayuwarsa ta baya da kuma wanda za ta zo a gaba? Mi ya haifar da gaba a tsakanin yan'uwa jini? Anya wuta da ruwa za su hadu? Find out in WANI GARI. Rikicin cikin gida. Labarin soyayyar da bata jin yare...
RUFAFFEN SIRRI by Sadnaf
Sadnaf
  • WpView
    Reads 4,569
  • WpVote
    Votes 335
  • WpPart
    Parts 10
labarin Sajeeda da ta ga jarrabawar rayuwa,ta wayi gari cikin tsananin ciwon da bata san ya akayi ta same shi ba,duk halin da take ciki makusancinta ya jefata a ciki
WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI) by MaryamahMrsAm
MaryamahMrsAm
  • WpView
    Reads 148,319
  • WpVote
    Votes 10,254
  • WpPart
    Parts 67
Labarin Soyayya, Sadaukarwa, Yaudara, Tuggu da Makirci.
A DALILIN KISHIYA  by sakee19
sakee19
  • WpView
    Reads 65,416
  • WpVote
    Votes 5,904
  • WpPart
    Parts 39
Rayuwa gaba daya ta canzawa Rabi a dalilin kishiya, duk wata dama da ta zata kauna ce ta sa ya hanata yanzu ya bawa amaryarsa wannan damar; harma ya na kafa mata hujja. Bata taba zaton zai yi mata haka ba ko mata nawa zai aura.
CIWON - SO by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 10,397
  • WpVote
    Votes 952
  • WpPart
    Parts 16
A masarautar ABIEY. Soyayyah ce kawai abun da ke iya sada rai da rayuwa. Sai dai a duniyar ZAHRA soyayyah wata hallinta ce da bata da mahadi da rayuwa, tun a wata kunyatacciyar rana da Iyalan ABIEY suka fitar da kansu daga duniyarta! DEEN ya zama wani bangare na rayuwar ABIEY da ZAHRA, ya sabunta wasu shafukan na rayuwarsa da ta su, ya kuma jefar da wasu. A yayinya da ra'ayoyin juna ya fara girmama, sai tafiyar ta sauya salo, dogon zaren ya tsinke. Tabbas rayuwa bata da sauki ga mutanen da soyayyah ta auresu. Sai dai shagaltuwa ya saka zuciyoyinsu yin wasi-wasi. CIWON - SO labari ne da aka gina akan wata irin soyayya mai ratsa jini da zuciya.
BAKAR WASIKA by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 25,434
  • WpVote
    Votes 1,095
  • WpPart
    Parts 11
BAƘAR WASIƘA... Mai farin rubutu Ban ce tafiyar mai sauki ba ce. Ban muku alkawarin zallar soyayya ba. Ban ce babu farincikin ba. Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki. Labarin Talba, Rafi'a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal da kuma Aminatu. Labarin BAKAR WASIKA, labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta... Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira! A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi. Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke? Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa? BAKAR WASIKA... JUANURY 2022
BONGEL(COMPLETED) by ZeeYabour
ZeeYabour
  • WpView
    Reads 120,930
  • WpVote
    Votes 7,970
  • WpPart
    Parts 81
BONGEL
ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅ by SaNaz_deeyah
SaNaz_deeyah
  • WpView
    Reads 26,714
  • WpVote
    Votes 2,349
  • WpPart
    Parts 49
"A ganinka wannan shine adalcin da zakayi min, matsayina na matarka amma idan zakayi kwanciyar aure dani sai dai kayi min fyaɗe, wannan wace irin azabtarwa ce, ni ba zan taɓa hanaka haƙƙin ka na aure ba, amma muguntar da kake min ta isa haka, likita ya tabbatar min da cewa gabana yana gab da ruɓewa. Zayyan ka tausaya min ka riƙa sassauta min, ina son in ɗanɗana daɗin soyayya kafin in mutu." Labarin Amatul-ahad wadda ta taso cikin maraicin uwa, kuma tayi auren jeka nayi ka, wanda ta gwammace gara zaman gidan ubanta akan gidan mijinta, labarine daya faru a gaske, labarine mai cike da ɗumbin darussa musamma ga wanda basu yawaita ambaton Allah a lamarunsu.
RAI DA KADDARA by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 78,098
  • WpVote
    Votes 7,816
  • WpPart
    Parts 59
Daada, Ku saka mata Munawwara, ku kira ta da Madina. Watakila albarkacin sunayen biyu rayuwar da bata da zabi a kanta ta zo mata da sauki ko yaya ne. Zan so kaina a karo na biyu, ku fada mata mahaifiyarta ta sota a watanni taran zamanta a cikinta, ko ba zata yarda ba Daada ki fada mata ta yafe mun, ki bata hakuri na yanda zata kare sauran kwanakin ta a duniya tana biyan zunuban mahaifanta. Kuma ku fada mata sunan baban ta Kabiru, yanayin haihuwar ta ba zai canza cewa ita din jinin shi bace ko da bata da gadon shi. Ke ma ki yafe mun, kiyi mun addu'a ko da rayuwa ba zata sake hada fuskokin mu ba. Yelwa.