Maman-xahra
5 stories
Morhan by BintouAbdool
BintouAbdool
  • WpView
    Reads 206
  • WpVote
    Votes 3
  • WpPart
    Parts 15
*MORHAN* _Bismillahir rahamanir Raheem, Da sunan Allah mai rahama mai jin 'kai_ *_SADAUKARWA_* _Gabadaya littafin nan sadaukarwa ne ga aminina Sani M Naseer Allah ya biya maka bukatunka na alheri_ *SHIMFI'DA da GABATARWA* Tabbas a cikin rayuwar kowannenmu akwai duhuwa wanda idanuwa baya iya ganinta. Kullum nitsawa cikin duhuwar muke a yayinda haske ke bayyana a gare mu bayan mun nitsa cikinta. Kaman yadda 'kaddara yake ba mu sanin ta sai min nitsa a cikinta sannan haskenta zai bayyana a gare mu. Hmmm... Masu yawan bibiyan al'kalamina zasu yi tambaya a nan, me yasa Bintou take yawan jefo 'kaddara a cikin rubutunta?. Amsar ita ce 'kaddara ita ce zaren da ke bibiye da rayuwar kowannen mu. Ban ce tafiya ce mai sau'ki ba, labari ne da ta 'kunci tsantsar soyayya da sadaukarwa, amma ban muku alkawarin zallar soyayyar ba. Kunci, da kaddara su suka na'kasa farincikin MUHAMMAD NASEER (Morhaan). (Labarin Zakiyyah, Muhammad Sani, da Ahmad). MORHAN Labari ne da ya ta'bo wani 'bangare na rayuwar Morhan, ya rayuwa zata kasance idan mutum ya rasa soyayyar mahaifiya?, me zai sa uwa ta guji abin da ta haifa a cikinta sannan ta 'ki bashi kariya. Saniyar da ba ta da jela, Allah ke kore mata ƙuda.
ASABE REZA by lamtana
lamtana
  • WpView
    Reads 73,618
  • WpVote
    Votes 2,369
  • WpPart
    Parts 5
'Kwallina!' Zuciyarta ta buga da wannan kalmar, jan jikinta ta fara yi tana son isa inda ta jefar da kwallin, ji take shi kaɗai ne Zai iya taimakonta, shi kaɗai ne zai iya hana HAMOUD aikata duk wani abu da yake hari. Dafe kwalbar kwallin ta yi tana ƙoƙarin ɗauka. Da shi da gabjejen takalmin ƙafarsa ya ɗora a hannun nata, ya murje, ya muttsike, ya ƙara murjewa har sai da sautin rugurgujewar kwalbar da yatsunta ya fita, ta kwalla gigitacciyar ƙara jin kwalaben sun lume a tafin hannunta, a haka ta ji sautinsa yana faɗa mata abin da ya dakatar da fitar numfashinta. "Idan akwai halittar da ba zan taɓa yafewa a duka duniyata ta ba, to ke ce Fakriyya. Ki yi zina da mahaifina, ki keta alfarmar mahaifiyata, ki zo kuma ki aure Ni? Wane irin kwamcala ce wannan? Ki faɗa mini me na miki a rayuwa da za ki min wannan hukuncin? Ta ya ya ma na aure ki, me ya sa na so ki? Me zan miki?... Lura: (Akwai tarin sarƙaƙiya a labarin, ku taho a sannu, kuna kiyaye duk wani motsi na jaruman)
WATA ƘADDARA  by shamsiyaManga
shamsiyaManga
  • WpView
    Reads 329
  • WpVote
    Votes 7
  • WpPart
    Parts 10
A lokuta da dama ƙaddara tana zuwar mana ba tare da mun shirya mata ba,na kasance ni mutum ne a rayuwata mai taka tsantsan sannan ni mutum ne da babu abun da na tsana a rayuwata kamar rashin tarbiyya. Tun da nafara girma nasan menene fari da baƙi,nasan ciwon kaina naji a rayuwata bazan taɓa iya auren macen da bata da tarbiyya ba,daga cikin abun da na tsana a rayuwata akwai SATA,na tsani SATA na tsani mai aikatata,Saidai kuma kash! duk yadda nakai ga tsanartata hakan bai hanani cin karo da WATA ƘADDARA ba wadda ta sanya na auri ƴar gidan SATA ma'ana ita yarinyace da ta ginu akan SATA domin kuwa babu wanda bai san mahaifinta ba indai shahara ne a fannin SATA sannan itama yarinyar ta gado halin SATAR.
ALBI (My heart) ❤️ by hajjac
hajjac
  • WpView
    Reads 875
  • WpVote
    Votes 5
  • WpPart
    Parts 11
"Ina ruwanki da Rayuwata ? Ko mutuwa kika ga zanyi ina ruwanki? Humaidah kin takurawa rayuwata, nace miki bana san alaƙarmu dole ne? Ko ce miki akai idan na rasa matar aure zan iya auranki ne? Leave my life Humaidah, ki barni kije kiyi rayuwarki idan ba haka ba.." Ya faɗa yana sake matse mata wuya ta fara kakarin mutuwa ya sake ta. "Get out of my room kafin na kasheki a gurin nan." Da gudu ta fice tana wani buga kafafuwa. Shi kuwa juyawa yai cikin fushi ya dinga cilli da pillows ɗin kan gadonshi. Wai me yasa ake masa kallan bad man ne? Me yasa kowace shaiɗaniya tazo da shaiɗancinta sai ta tunkaro shi? Wajan mirror ya nufa yana kallan kansa, gani yai be yi kala da wanda za'a cewa mutumin banza ba, banda wanda yasan yana shan giya, duk inda zai fita ya shiga ba za'a kirashi da mai shanta ba, amma ya rasa me yasa mata suke yi masa haka. Juyawa yai tare da fadawa kan gadonsa, Rahama ce ta faɗo masa a rai, yai saurin tashi tare da, zuge glass window yana hango gidan su Rahama, ko a wane hali take ciki oho. Koma menene shi ya janyo mata, da beje club ba da wannan abun ba zai faru ba bare har ta baro school taje inda yake. Rintsa ido ya yi yana cizon lips. Zaku iya samun damar ci gaba da karanta labarin a can manhajar AREEWABOOK ta hanyar shiga wannan blue link ɗin. Ko kuyi searching hajjace22522 Karku manta da following namu, mungode. https://arewa-one.vercel.app/chapter?id=6352fd3b892e81ead74c443d
Zuri,a Daya by OumRamadan1
OumRamadan1
  • WpView
    Reads 32,909
  • WpVote
    Votes 3,043
  • WpPart
    Parts 48
Ko wacce tana takama da asalinta da yarenta, zazzafan kishi tsakanin wasu kishiyoyi na kabilar kanuri da kuma buzuwa da mijinsu bafulatani