TajawwalAlRuwh
- Reads 3,233
- Votes 702
- Parts 17
Ina hanya?
Ina mafita?
Ina zata bi ta ga haske a rayuwar ta?
Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma abunda ta dade tana so da muradi a rayuwar ta.
Ya zama dole tayi zabi tsakanin rayuwar ta da kuma farin cikin wanda ta fi so fiye da kowa da kuma komi a kaf fadin duniya.
Koh a mafarki, Hadiza bata taba tunani irin wannan rana zai zo ba a rayuwar ta; bata taba tunanin zata sama kan ta a cikin rudun da take ciki ba sai dai kuma ta san cewar duk abunda ke faruwa a cikin rayuwar ta rubataccen lamari ne, wanda Allah ya riga ya rubuta faruwar shi tun kan ta zo duniya.
Tana da tabbacin cewar da za a buda takardan Lawh-Al-Mahfouz, toh tabbas za a sama abunda ke faruwa da ita ta a cikin shafin da aka ware musamman dan rayuwar ta.
Lawh-Al-Mahfouz is a story of pain
Of sacrifice
Of strife
Of longing
A story of undying love.