Badeeyehbeauty's Reading List
6 stories
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE) by Mai_Dambu
Mai_Dambu
  • WpView
    Reads 303,037
  • WpVote
    Votes 50,735
  • WpPart
    Parts 113
A zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun haɗakar soyayyan Abu daya! Domin farin cikin mutum daya domin samun farin cikin mutum daya! Dole sai an sadaukar da farin cikin mutum daya
UKU BALA'I (Completed) by Kamala_Minna
Kamala_Minna
  • WpView
    Reads 67,165
  • WpVote
    Votes 3,742
  • WpPart
    Parts 77
"kin gama aikin ki don haka ga tukuicin ki". Ya fadi yana sanya hannu cikin aljihunsa yana zaro bandir din yan dubu dubu guda biyu ansa tayi tana mai kau da fuska kamar bata so ba. "Sannan kuma wannan lamarin ya kasance tsakanina da ke in har naji labari mai kama da shigen wannan lamarin kin san Allah sai kin bar filin duniyar nan". Ya karashe fuskarsa a daure kamar bakin hadarin dake kokarin zubda ruwa. Ko a jikin ta bata nuna damuwa da maganganunsa ba illa tsaki da tayi can kasar makoshi ta na balle murfin motar ta fice Khairiyya dake takure bayan mota ta duba da wani irin yanayi na tausayawa tana faman gyaɗa kai kafun ta dubi Alhaji Mati. "batar da sunanka sananne ka aro na banza ka sakawa kan ka akan wani KUDIRI naka na daban...Uhmm ba na ganin wanda ya isa rikakken mutum mara tsoro zai fito da wannan salon na boye sunan sa domin duk wanda yake so ya fado DUNIYAR SHAHARA a wani fanni da sunan sa ya kamata a san shi ko an rufe babin sa ba za taba mantawa dashi ba da abin da ya aikata". Tana gama fadin haka ta buga murfin motar da karfi yan yatsunta biyu ta dagawa Khairiyya wacce a wannan lokacin ta dago da kanta tana dubansu su duka biyun cikin yanayin na rashin inda suka dosa a tsakanin su. "Hajiya Layla" Ya fadi da murmushin mugunta a laɓɓansa kafun ya dora. "...abu daya zai sa na kyale ki a filin duniyar nan shi ne wannan yarinyar da kika bada takomashin taimako har na same ta saboda ita ce hanyar samun arzikina da nake burin cimma wa wannan dalilin zai hanani yi miki komai amma duk da haka ki tsumaye ni ina nan tafe". yatsine fuska tayi kafun ta juya ta fara takawa kan kafafuwanta. Dariya yake yi sosai da sosai har yana buga sitiyarin motar kafun ya tsagaita kamar daukewar ruwan sama fuskar nan tashi ya haɗe ta waje daya kafun yayi wa motar ki ya fizge ta kamar mai kokarin tashi sama.
RAYUWAR BADIYYA ✅  by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 278,568
  • WpVote
    Votes 21,592
  • WpPart
    Parts 61
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi. Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai. Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu. _______ Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?
BAN AIKATA BA by Basira_Nadabo
Basira_Nadabo
  • WpView
    Reads 14,239
  • WpVote
    Votes 711
  • WpPart
    Parts 9
Labari ne akan abinda majority ďinmu muke aikata wa wanda kuma wallahi muna kai kanmu ga halaka ne ku kasance tare dani don jin wani irin abu ne wanna. Karku manta vote da comment yana karawa labari armashi Vote Vote Vote And Vote Karku manta da comment dearest friends 13/09/2017
DOGARO DA KAI  by ayeesh_chuchu
ayeesh_chuchu
  • WpView
    Reads 39,663
  • WpVote
    Votes 2,626
  • WpPart
    Parts 24
It's a Hausa story, based on self confidence, love, business, Hausa culture and lot more. Zainab yarinya ce da ta Dogara da kan ta, ta dalilin sana'ar da take takama da ita. Hakan yasa 'yan uwanta matasa su ke koyi da ita wajen ganin sun dogara da kansu. Katsam! Kaddara ta haɗa ta Samir Alkali da Hafeez Sulaiman. Matasa ne da su ka dogara da kan su, su ka kawo rud'ani a rayuwar Zainab. Shin waye gwarzon?? Ku tsunduma tsundum acikin wannan gajeren labarin.
choose | luke hemmings by abstractstyles
abstractstyles
  • WpView
    Reads 35,351,813
  • WpVote
    Votes 1,124,190
  • WpPart
    Parts 90
It's you, May. You're what I want forever. [COMPLETE] achievements: #1 in fanfiction