ummyakdrs's Reading List
22 cerita
FATU A BIRNI (Complete) oleh suwaibamuhammad36
suwaibamuhammad36
  • WpView
    Membaca 75,562
  • WpVote
    Vote 2,363
  • WpPart
    Bab 18
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa. Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa? Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan. Fatima- Budurwar Sultan.
MARWAN COMPLETE oleh AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Membaca 21,734
  • WpVote
    Vote 2,356
  • WpPart
    Bab 35
Safwan yace, " dama inasan ganin Nazir akwai muhimmiyar maganar dana zo da ita nake san mu tattauna " yana gama faɗa mahaifiyar su Nazir ta rushe da kuka sannan tace, " Nazir baya magana hasalima baya cikin hayyacinsa baisan waye ma akansa, kallan yayan Nazir tayi ta ce, " kai je kaxo mai da Nazir " nan take ya tashi ya fice sai gashi da wheel chair da Nazir aciki sai kallan mutane yake yana zubda hawu hannuwansa da ƙafafu gaba ɗaya sun shanye, Safwan na ganinsa cikin tashin hankali yace, " Wannan ne Nazir ɗin mai ya sameshi? " wani sabon kukan mahaifiyar su Nazir ta ƙara sawa, cikin ƙarfin hali yayan Nazir ya fara magana, " aranar da mahaifinmu ya rasu Nazir yace mana zaije gidansu Maryam, to bayan y dawo muna zaune sai gani mukayi ya zabura yana ihu yana cewa bazai kuma ba, sai kuma muka ga yana ta surutai daga haka kawai sai gani mukayi ya yanke jiki ya faɗi, shikenan har yau ka ganshi ahaka kullin magani ake bashi amma ba sauƙi kullin ciwon gaba yake yi. " gaba ɗaya jikin Safwan ne yayi sanyi cikin sumutar baki Safwan yace, " tabbas Marwan ne " karaf yayan Nazir yace, " wai waye Marwan ɗin nan naji lokacin da yake ta sumbatu yana cewa Marwan kayi haƙuri, ko kuma abokin aikinsu ne dan wannan ciwon ba tantama sihiri ne. " Safwan gaba ɗaya tausayi da tsoron halin da Nazir ke ciki ya kama shi.
BAYA BA ZANI oleh fadeelalamido
fadeelalamido
  • WpView
    Membaca 24,957
  • WpVote
    Vote 1,016
  • WpPart
    Bab 17
Hausa novels
💪🏻💪🏻GAWURTACCEN SOJA 👨‍✈️👨‍✈️ (COLONEL UBAIDULLAH RETURN) oleh fateemah0
fateemah0
  • WpView
    Membaca 3,797
  • WpVote
    Vote 165
  • WpPart
    Bab 10
ZANEN KADDARARSA TA FARA NE TUN YANA YARO HAR IZUWA GIRMANSA, AN KASHE ƘANWARSA YA ƊAUKI FANSA!!! TA MUTU SABIDA MUYAGUN DA SUKA YI MATA FYAƊE!! YA HUKUNTASU A MATSAYINSA NA JARUMIN SOJA!! MAHAIFIN YARON DA YA HUKUNTA YA DAWO YA KASHE MASA MATARSA!!! WAI SHIN YA ZATA KAYA NE!!?? KARKU BARI A BAKU LABARI DAN YACE ƊAUKAR FANSA A JININSA YAKE BA A BAKINSA YAKE BA, ZA KU SAMU BOOK DIN GAWURTACCEN SOJA AKAN FARASHIN ƊARI UKU #300 VIP #500 SAI NA JIKU MASOYANA, DAN AKWAI CAKWAKIYA KARKU BARI A BAKU LABARI.
MAHAUKACIN KISHI oleh zaynerbmuhammadkabir
zaynerbmuhammadkabir
  • WpView
    Membaca 22
  • WpVote
    Vote 0
  • WpPart
    Bab 1
yana magana akan MAHAUKACIN kishin dawasu matan sukeyi
UQUBAR UWAR MIJINA oleh YoungNovelist4
YoungNovelist4
  • WpView
    Membaca 11,264
  • WpVote
    Vote 530
  • WpPart
    Bab 19
Based on true life story labarine akan wata baiwar Allah wanda uwar miji tajefata cikin matsanancin baƙin ciki ɗa gararin rayuwa,sanadin hakan ta..just read and find out
A DALILIN ZOBE 2019 oleh Ummeetah270
Ummeetah270
  • WpView
    Membaca 667
  • WpVote
    Vote 14
  • WpPart
    Bab 1
Wannan labarin daya faru shekara dari biyar da hamsun da suka shude. Anyi wani azzalumin sarki mai suna sarki Barbus wanda ya mulki duniya ta dalilin zoben sihiri. Sai dai kash! Sarki Barbus bai da magaji shinko ko waye zai gaji sarautar say bayan mutuwar sa? Duk ku biyoni cikin littatina na A DALILIN ZOBE. Ngd
Nisa Aljana oleh InayahDjauhariPutri
InayahDjauhariPutri
  • WpView
    Membaca 268
  • WpVote
    Vote 14
  • WpPart
    Bab 11
Cerita singkat seorang gadis berhijab yang sangat lincah bernama Nisa Aljana, dengan segala polah tingkahnya yang tomboy
WATA UNGUWA oleh Ruky_i_lawal
Ruky_i_lawal
  • WpView
    Membaca 1,242
  • WpVote
    Vote 29
  • WpPart
    Bab 16
labarin kwamacalar dake afkuwa a wata hargitsattsiyar unguwa, akwai al'ajabi a labarin.
SANADIN RAGON LAYYA CMPLT oleh AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Membaca 3,361
  • WpVote
    Vote 248
  • WpPart
    Bab 10
Bil hakki mlm kabiru ya dage yake ta karantowa hajara ayatulkursiyyu, ya karanta yafi a irga idan ya karanto wannan aya yana kaiwa karshe zai karanto wata, duk atunaninsa aljanune suka make hajara, mamaki ne ya kara cika shi ganin takalmin hajara wari daya akafarta wari daya kuma igiyar ta tsinke, buta a tuntsire ruwan cikinta ya tsiyaye tas, surutai hajara ta cigaba dayi bakai ba fasali, hakan ne yasa mlm kabiru ya kara daga murya cikin azama yana karanto mata ayoyin kur'ani yana tofa mata. Hajara cikin fusata tace, " mlm wai sai tofeni kake yi ni kabarni inji da abinda yake damuna " Dan dakatawa yayi da karatun yana karewa hajara kallo, tsab muryarta take da alama ba wasu jinnu da suke damunta, zaninta ya janyo ya rufe mata cinyoyinta dasu, yunkurawa hajara tayi ta tashi zaune tana zubda kwallah. Cikin tashin hankali Mlm kabiru yace, " hajara lafiyarki me ya sameki cikin dare kike wannan ihun, nasha gaya miki idan zaki kwanta ki dinga tofe jikinki da addu'a, kuma idan mummunan mafarki kikayi basai ki karanta addu'a ki koma bacci ba, idan baccin ya gagareki sai ki yo alwala ki gabatar da sallah ki fawwalawa Allah lamuranki, to hajara kodai gamo kikayi dan naga buta kusa dake " mlm kabiru ya karasa magana yana kallan hajara da fuska ta hade hawaye da majina. Hajara girgiza kai tayi sannan tace, " babu ko daya malam " Mlm kabiru kuluwa ya farayi cikin fada yace, " amma ba abinda yake damunki kikaxo tsakar gida cikin dare kina wannan haukan salan mak'ota suce wani abun akai miki ko azaci aljanu kika hau, cire makota ma yanxu da yaran nan sun farka suka fito suka ganki da dan kanfai me zaki ce musu, sai ki tashi ki kamwashe tsummokaranki kiyi gaba, ina cikin baccin na me dadi kin tashe ni " Hajara bakin ciki ne ya cikata, zafi biyu ga na rashin rago ga sababin da mlm kabiru yake mata, rushewa tayi da kuka cikin kuka tace, " mlm rago ne, wallahi ragon nan ne " sai kuka yaci karfinta ta kasa karasa maganar. Guntun tsaki yaja sannan yace, " yanxu hajara