YUMINALIYU's Reading List
59 stories
*ƘARFE A WUTA* by Ayshercool7724
Ayshercool7724
  • WpView
    Reads 15,311
  • WpVote
    Votes 282
  • WpPart
    Parts 12
*A lokacin da doka, ke ƙoƙarin yaƙi da ta'addanci, ko ta halin ƙaƙa, an samu naƙasu a sanadiyyar bara gurbi, da masu yi wa dokar bi ta da ƙulli. Nasara na daf da samuwa, soyayya ta yi kutse, wurin gwamutsa ƙaddarori biyu wuri guda. Ga soyayya da ta'addanci ga kuma doka, ko wane ɓangare ne mai gaskiya? Waye zai yadda ya bi wani *ƘARFE A WUTA ka fi ƙarfin ɗauka da hannu....ƘARFE A WUTA sai dai kallo. Ƴar kasada ce, kuma mai kishin ƙasa a zatonta komai zai zo da sauƙi, kamar yadda take hangensa, sai dai ƙaddara ta shammace ta, abun harinta ya zama abun bawa kariyarta*
NAUSHIN WUTA by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 1,479
  • WpVote
    Votes 53
  • WpPart
    Parts 12
'Yar uwata idan kin san ke uwa ce, ko mai burin kasancewa uwa wannan littafin naki ne. Ki dakata ki karanta domin ƙunshe yake da sadaukarwar da babu wata hallita da za ta iya gudanarwa sai uwa. NAUSHIN WUTA masu iya magana suka ce, ƙarfe da danga ba sa iya kare shi. Shin kowacce uwa ce take fuskantar takaici da ƙuncin rayuwa? Shin kowacce uwa ce ke haƙurƙurtar da zuciyarta domin farincikin 'ya'yanta? Shin akwai uwar da za ta iya rayuwar ƙunci domin samun nagartar rayuwar 'ya'yanta? Tabbas akwai sadaukarwar da mahaifi ba zai iya wa 'ya'yansa ba, amma tabbas uwa tana iya ba da rai da zuciyarta domin farincikin 'ya'yanta.
ABBAN SOJOJI by BossBature88
BossBature88
  • WpView
    Reads 49,970
  • WpVote
    Votes 972
  • WpPart
    Parts 19
💋Romantic Love story💋 Labarin matashiyar yarinya wadda ƙaddara ke kaita aikatau gidan sojoji tayi shigar maza Amatsayin ɗan aiki, gidan Abban sojoji wanda yakasance chief of Army staffs, ƴa'ƴansa goma shatakwas duk maza masu riƙe da manyan muƙamai na sojoji 💋💘💞
TAFIYAR ƘADDARA  by NASRULLAH133
NASRULLAH133
  • WpView
    Reads 1,019
  • WpVote
    Votes 54
  • WpPart
    Parts 23
"Kai bil-adama! Kai bil-adama! Kai bil-adama! Wanne tsautsasayin ne ya jefo ka cikin wannan ƙasurgumin jejin namu, Jejin Balkaltum Jejin halaka? Ya kai bil'adama kai sani cewa wannan Jejin Balkaltum birnin mune fadar muce bugu da ƙari masarautar muce, wannan ce nahiyar mu duk wani bil'adama da ya yi ƙokarin shigar mana masarautarmu za muga bayanshi" ko da mai magana yazo nan a zancen shi shiru yayi.
ANYA BAIWA CE? by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 12,999
  • WpVote
    Votes 215
  • WpPart
    Parts 11
Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za'ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? " Boka ya ce, " Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan " ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa. Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, " Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba " Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, " Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani. Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al'amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba."
SOFIA ✔ by DielaIbrahim
DielaIbrahim
  • WpView
    Reads 545
  • WpVote
    Votes 43
  • WpPart
    Parts 24
Nakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sila ne ta dalilin Depression a turance kenan, to amma likitoci sun faɗa cewa da ace mahaifiyar bata da ciki da ita zata samu rauni (na rashin ji, ko kuma rashin gani, ko ciwon hauka) sai akayi rashin sa'a uwar na ɗauke da juna biyu sai abin ya sauka akan abin da ke cikin ta,Maimakon yayi ma uwar illah sai yayi ma SOFIA illah aka haife ta nakasasshiya kuma likitoci sun tabbatar ba lallai ta iya tafiya ba saboda jijiyoyin da zasu taimake ta wajan tafiya sun mutu basu da karfin da zasu iya zama lafiyayyun jijiyoyi. Shin da gaske ita ɗin MABARACIYA ce?, Yaya zata kalli AL'UMMA ko yaya AL'UMMA zasu kalle ta?, SADAUKARWA mai cike da rugujewar Mafarkai da Burika, SARƘAƘIYA, KADDARA, RAYUWA mai cike da ZAGON ƘASA.
MASARAUTAR MAYURNO by AuntiMamee
AuntiMamee
  • WpView
    Reads 28
  • WpVote
    Votes 0
  • WpPart
    Parts 3
Masarautar Mayurno nayi shine Dan dalilai biyu. Na farko nishadi na biyu kuma domin masu karatu susan wani dadaddan masarautar misulunci mai tsohon tarihi dake yankin Sudan.
WATA MASARAUTA by hauwahhh_
hauwahhh_
  • WpView
    Reads 5,458
  • WpVote
    Votes 258
  • WpPart
    Parts 7
Mulki da Sarautar Bizar Wa'innan abubuwa guda biyun sune duniyarshi, zai iya rasa komai da kowa ta dalilinsu, ciki kuwa Harda tilon d'ansa. Musamman ma a Irin wannan lokacin da babban asirin sa ke gab da tonuwa. Asirin da ya shafe shekaru Yana Dakon su, asirin da yasa shi kashe mahaifiyar shi, k'anin shi shi da kuma matar mahaifin shi,asirin da zata iya tarwatsa shi a cikin sakanni, asirin da koh Matan shi bata san da zaman shi ba, asirin da yake ganin ya rufe ruf kenan Har abada. Sai Gashi K'aramin alhaki Kaman Ateed Zarrah Yana qoqarin tonowa. A irin wannan lokacin bashi da wani zab'i illa yayi kare jini biri jini da d'an qanin nasa kuma Sarkin na Bizar wato Ateed Zarrah. Lokaci yayi da zaibi su Naqeeba da Sameed.
SIRRIN MU by nimcyluv
nimcyluv
  • WpView
    Reads 11,987
  • WpVote
    Votes 286
  • WpPart
    Parts 12
_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin littafi ce,baka sanin abinda yake bangwan baya dole saika buɗe shafin gaba,muna zuwa Duniya ne ba tare da sanin abinda ke cikinta ba,wasu na zuwa a makance, wasu a kurmance,wasu kuma babu ido,kunan jin magana,uwa uba wasu basa zuwa da ƙafar takawa_ _Nakasa bata taɓa zama kasawa,haka kuma ƙaddarar data mai dashi nakashasshen zata iya sauya, kullum cikin zullumi yake, shin tayaya ne rayuwa zata kasance masa? tayaya yana nakashasshen zai iya mulkan dubban jama'a? Cikin ana tsangwamarsa bare ace ya zama shugaba,yaya jama'ar gari zasu ɗauke sa?tayaya zai gabatar da mulkin bayan Allah ya taushe ta hanyarsa rasa wani ɓangare na jikinsa?_ _Zuciya nada abubuwan ban mamaki,abinda kake so ita bashi take so ba,kullum yana ganin abin kamar mafarki amma yadda abin ke zamar masa a gaske shike masa mamaki,me zaiyi wanda zai samu farin ciki?me zaifi wanda zuciyarsa zata daina kewa ta daina ƙunci,duhun dake cikinta haske ya mamaye shi, FARAUTA shine abinda zuciyarsa ta yanke masa,abin mamaki shine tayaya nakashasshe zai iya zama mafarauci? Tayaya farauta zata masa maganin damuwarsa?.._ '''SHIN ZAI IYA KO A'A? YANA CIN RIBA A FARAUTAR KO A'A? KUNA TUNANIN WATA RANA NAKASAR SA ZATA IYA ZAMA RIBA GARESA?
KWANTAN ƁAUNA by Nana_haleema
Nana_haleema
  • WpView
    Reads 12,578
  • WpVote
    Votes 372
  • WpPart
    Parts 27
Izza, mulki, ƙasaita sun tattara a gare ta ita kaɗai. ƴar sarki ce, jikar sarki ce, matar sarki ce. Bata ƙaunar talaka, bata son haɗa hanya da talauci. Burinta ɗaya tak ya rage a duniya; shi ne ɗanta ya zama sarki, ita kuma ta zama babar sarki kuma kakar sarki na gobe. Sai dai kash! ƴaƴan nata maza har guda uku, masu matuƙar kama da juna, sun kasance babu wanda yake da qualities ɗin riƙe ragamar al'umma. A Lokacin da burinta ke gab da cika kwatsam aka ti mata dirar mikiya, ƴar talakawa, baƙa, gurguwa, mai tallan abinci ta shigo rayuwar samarin ƴaƴan nata guda uku, gurgurwar da ta zama silar girgizar duniyarta da burinta, gurgurwar da ta haddasa mata raunin da bata da shi, gurguwar da ta zamar mata inuwar dodo, gurguwar da ta zama mata ƙadangaren bakin tulu. Shin me zai faru? Ta wacce hanya gurguwa zata kutso cikin rayuwar waɗannan jinin sarautar...? Waye zai zama sarki cikinsu ukun duk da kasnacewar su masu kama ɗaya? ina alwashin da ta ɗauka na ganin cewar sai taga bayan duk wanda ya nemi ya ruguza lissafinta?, ina alwashinta na cewar sai ta kassara rayuwar wanda ya kawo kutsen hana ɗanta zama sarkin gari....?