Fancy
16 stories
MATAR MIJINA...Completed by Kamala_Minna
Kamala_Minna
  • WpView
    Reads 37,541
  • WpVote
    Votes 2,661
  • WpPart
    Parts 92
...Zuciyarta sosai take mikata wani mataki na firgici, ba ta shirya ansar wannan lamarin ba, lamarin da take hango cikin sa ba komai ba illa tashin alkiyamar duniyarta.Tana tsoron sake afkawa tashin hankalin rayuwa sosai take jin zuciyarta bata yi amanna da bukatar Jaamal Bukar Kutigi ba, in tayi duba da halaccin da Sumayya Attahiru Kangiwa tayin mata, a filin duniyar rayuwarta.Butulci take kallon lamarin, butulci mafi girma wanda in har mutanan duniya suka ji,ta sani za suyi mata tofin Allah tsine...
KOWANNE BAKIN WUTA by fadeelalamido
fadeelalamido
  • WpView
    Reads 62,458
  • WpVote
    Votes 3,372
  • WpPart
    Parts 46
labrin yana dauke wa wani muhimmin darasi
AMINAN JUNA!.  by Zarah_bb
Zarah_bb
  • WpView
    Reads 3,590
  • WpVote
    Votes 343
  • WpPart
    Parts 23
Sun kasance AMINAN JUNA tun suna yara amma sai da ya bi duk wata hanya dun ganin ya raba su.
NA YI DA NA SANI!.  by Zarah_bb
Zarah_bb
  • WpView
    Reads 11,395
  • WpVote
    Votes 953
  • WpPart
    Parts 19
"Adda ki ji tsoron Allah, kada ki bari son zuciya ya kai ki da yin da na sani."
ZANYI BIYAYYA by asmasanee
asmasanee
  • WpView
    Reads 43,039
  • WpVote
    Votes 2,832
  • WpPart
    Parts 29
It All About love nd destiny of life
GADAR ZARE by HauwaAUsmanjiddarh
HauwaAUsmanjiddarh
  • WpView
    Reads 402,112
  • WpVote
    Votes 19,018
  • WpPart
    Parts 85
A firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu yana yarfa hannunsa, zumbur ya mik'e ya nufi fridge ya d'auko robar ruwa ya bulbulawa kansa "Akan ido na suka k'one gidan mu, mahaifiya ta, mahaifi na, k'anne na duk suka mutu akan kunne na ina jiyo ihun su *************** "Cikin waye wannan a jikin ki? uban waye yayi miki ciki? bazaki fad'a ba saina kashe ki, wayyo na shiga uku duk irin tarbiyyar dana baki abinda zaki saka man dashi kenan, cikin kuka tace " wallahi Aunty ban sani ba, idan za'a kashe ni ban san wanda yayi min cikin nan ba, nima ganin shi kawai nayi ajiki na, tafiya tayi ta bud'e durowa ta d'auko Qur'an ta d'ora akan ta tace " na rantse da wanda raina ke hannunsa bansan wanda yayi min ciki nan ba. Kanta tayo gadan-gadan tana nizaki rainawa hankali, ta shak'e ta idonta suka kakkafe ************** A cikin gidan yarin yake ihu yana kuka yace " sunci Amana ta, sunyi min butulci, na yarda dasu amma sun ci min amana sun had'a min GADAR ZARE Amintattu nane suka yi silar zuwa na gidan yarin, sun raba ni da kowa nawa sun raba ni farin cikina,cikin matsanancin kuka yace " wallahi koda zan rasa komai na rayuwata bazan kyale su ba. Sun mun sharri, sun had'a man makirci da GADAR ZARE ************* "Koken a cikin kayana kuma, kafin ya k'ara sa maganar dubbun police sun kewaye shi da bindugogi, Ana cikin haka wayarsa ta fara ringing, dakyar ya samu ikon d'agawa, ji yayi muryarsa ta tintsere da dariya yace " nine, d'an uwanka, kaga yadda nayi wasa da hankalinka ko, na nuna maka halin 'yan Adam Cikin rawar murya yace " mai yasa kaci amanata? " saboda ina santa, ita rayuwa tace kuma mallakina , Wani irin mahaucin ihu ya saki tare da buga wayar da k'asa .
🍒🌺NATSANE SHI🌺🍒 by asmasanee
asmasanee
  • WpView
    Reads 579,534
  • WpVote
    Votes 39,697
  • WpPart
    Parts 93
Dan iska ne Tantiri ne ,mawaki ne da yayi fice afadin duniya,yana karatu a abroad,dan iska ne na karshe amma yasan da wa yake iskancin nasa,baya son hayani miskiline na karshe,wannan halin koh nace rayuwar tasa yasa yan mata masu takama da mulki saurata ,dukiya soke mugun fadawa kan tarkon sa,koh diyar wace ke koh me kike takama dashi yana iya wulakan ta ki,bakomi yake takama dashi ba sai kyau ,kuddi,ilimi da haiba,ya fito daga daya daga cikin masu kuddi Maiduguri wato MAITAMA FAMILY Zan iya yi yafada mata yana kashe mata ijiya daya dasauri ta saka tafin hannu ta da yaji xane lalle ja da baki ta rufe fuskar ta hade da gyada masa alamar yayi😝....komi nene wannan xaiyi oho😂fans..mu hade ciki don jin ya xata kaya. ROMANTIC ND HATRED LOVE😍😍
UKU BALA'I (Completed) by Kamala_Minna
Kamala_Minna
  • WpView
    Reads 67,165
  • WpVote
    Votes 3,742
  • WpPart
    Parts 77
"kin gama aikin ki don haka ga tukuicin ki". Ya fadi yana sanya hannu cikin aljihunsa yana zaro bandir din yan dubu dubu guda biyu ansa tayi tana mai kau da fuska kamar bata so ba. "Sannan kuma wannan lamarin ya kasance tsakanina da ke in har naji labari mai kama da shigen wannan lamarin kin san Allah sai kin bar filin duniyar nan". Ya karashe fuskarsa a daure kamar bakin hadarin dake kokarin zubda ruwa. Ko a jikin ta bata nuna damuwa da maganganunsa ba illa tsaki da tayi can kasar makoshi ta na balle murfin motar ta fice Khairiyya dake takure bayan mota ta duba da wani irin yanayi na tausayawa tana faman gyaɗa kai kafun ta dubi Alhaji Mati. "batar da sunanka sananne ka aro na banza ka sakawa kan ka akan wani KUDIRI naka na daban...Uhmm ba na ganin wanda ya isa rikakken mutum mara tsoro zai fito da wannan salon na boye sunan sa domin duk wanda yake so ya fado DUNIYAR SHAHARA a wani fanni da sunan sa ya kamata a san shi ko an rufe babin sa ba za taba mantawa dashi ba da abin da ya aikata". Tana gama fadin haka ta buga murfin motar da karfi yan yatsunta biyu ta dagawa Khairiyya wacce a wannan lokacin ta dago da kanta tana dubansu su duka biyun cikin yanayin na rashin inda suka dosa a tsakanin su. "Hajiya Layla" Ya fadi da murmushin mugunta a laɓɓansa kafun ya dora. "...abu daya zai sa na kyale ki a filin duniyar nan shi ne wannan yarinyar da kika bada takomashin taimako har na same ta saboda ita ce hanyar samun arzikina da nake burin cimma wa wannan dalilin zai hanani yi miki komai amma duk da haka ki tsumaye ni ina nan tafe". yatsine fuska tayi kafun ta juya ta fara takawa kan kafafuwanta. Dariya yake yi sosai da sosai har yana buga sitiyarin motar kafun ya tsagaita kamar daukewar ruwan sama fuskar nan tashi ya haɗe ta waje daya kafun yayi wa motar ki ya fizge ta kamar mai kokarin tashi sama.